TSOHUWAR jarumar Kannywood, Hajiya Halisa Muhammad, ta ce tana neman addu’a daga jama’a.
A wani saƙo da ta saki a soshiyal midiya a yau game da halin da take ciki na rashin lafiya, Halisa ta nemi dukkan al’umma, ‘yan’uwa da masoya, da su taya ta da addu’ar samun nasara a bisa aikin da za a yi mata dangane da ciwon dajin mama da take fama da shi.
A saƙon, Halisa ta ce: “Assalamu Alaikum ‘Yan’uwana Musulmi da al’ummar gari masu albarka. Ina roƙon ku da ku taya ni da addu’a yayin da zan fara shan “radiotherapy” don ciwon cancer da nake fama da shi.
“Rayuwa tana hannun Allah, kuma addu’ar ku tana da tasiri matuƙa.
“Ina buƙatar ku ƙarfafa mani zuciya da taimakon Ubangiji a wannan mataki na jinya. Ku ce ‘Ameen’ tare da ni, ku ɗaga hannuwan ku ku roƙi Allah Ya ba ni lafiya cikakkiya, Ya sauƙaƙa mini hanya, Ya sa maganin ya yi tasiri, kuma ya maida ni cikin ƙoshin lafiya da natsuwa. Allahumma Ameen.
“Allah Ya saka muku da alheri. Ina godiya ƙwarai da kulawa da goyon baya.”
Halisa Muhammad dai ta daɗe tana fama da wannan cutar wanda a shekarar da ta gabata an yi mata aiki aka ɗora ta a kan shan magani. Daga baya sai ciwon ya ƙara dawowa.
Ko a wancan lokacin ta sha wahala tare da kashe miliyoyin kuɗi tare da tallafin ƙungiyoyi da kuma gwamnatin Jihar Kano.
Haka ma a wannan lokacin gwamnatin Jihar Kano ce ta ɗauki nauyin kashi mafi yawa na kuɗin da za a kashe a kan rashin lafiyar.