GWAMNAN Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya naɗa fitacciyar marubuciya Fauziyya D. Sulaiman muƙamin babbar mai taimaka masa kan harkokin jinƙai da agaji ga mabuƙata.
Fauziyya ita ce shugabar wata gidauniya mai zaman kan ta a Kano mai suna ‘Creative Helping Needy Foundation‘ kuma ta yi fice wajen nema wa mabuƙata, musamman marasa lafiya, taimako a wajen jama’ar Annabi.
Marubuciyar littattafai ce wadda kuma ke rubuta labarin fim (screenplay). Haka kuma ma’aikaciya ce a gidan talbijin na Arewa 24 da ke Kano.
An yi sabon naɗin ne a yau, kamar yadda marubuciyar da kan ta ta sanar a wani saƙo da ta wallafa a soshiyal midiya.
A rubutun da ta yi kan yadda ta samu labarin naɗin nata, Fauziyya ta labarta wa duniya cewa: “Ɗazu wani ya kira ni ya gaya mun suna meeting da mai girma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi ta ambaton irin aikin da nake yi saboda yana bibiyar shafi na, ya ce, ‘Tabbas kina abu mai kyau, ki ci gaba.’ Na yi godiya.

“Da la’asar kuma sai abokin aiki na, Nasir Nid, ya shigo ofis yana dariya, ya ce, “Uwar marayu, mai girma Gwamna ya ba ki muƙami a kan aikin ki na jinƙai.’ Na ce, ‘Tsokana ta kake.’
Ya yi ta rantsuwa, muna dariya.
“Zuwa can sai ga kiran Sunusi Oscar, ya ce mini, ‘Hajiya Fauziyya, mai girma Gwamna ya ba ki muƙamin SSA.’ Na ce, ‘Ni kuma?’ Ya ce, ‘E, yanzu haka muna meeting da shi, zan kira ki idan mun kammala.’
“Zuwa can ya kira ya ce mu haɗu. Bayan mun haɗu ya ba ni takardar nan, ya ce, ‘Mai girma Gwamna ne ya ce a ba ki.’
“Na riƙe baki da mamaki, na ce, ‘Ni da ba ‘yar siyasa ba yaya za a ba ni muƙami?’
“Sai ya ce, ‘E, ai da man ba a kan siyasa aka zaɓe ki ba. Mai girma Gwamna ya ba ki muƙami a kan aikin da kike yi na tallafi da jinƙai domin yana ganin aikin ki yana bin fejin ki hankalin sa yana tashi a kan duk abin da kike sakawa. Ga takardar ki. Amsa.’
“Na amshi takardar na kalla, na ce, ‘Yanzu wannan daga hannun gwamna take?’
“Ya ce, ‘Ƙwarai kuwa. Duk Kano wa ya isa ya yi rubutu da jan biro idan ba gwamna ba?’

“Kamar dai yadda kuke ganin wannan takarda, mai girma Gwamnan Kano ya ba ni muƙamin SENIOR SPECIAL ASSISTANT, NEEDY AND VULNERABLE. Ina godiya ƙwarai da gaske ga mai girma Gwamna.
“Ina neman addu’ar ku bisa wannan nauyi da mai girma Gwamna ya ɗora mini, ‘yan’uwa.
“Allah ya sa ya zama alkairi ga al’ummar Jihar Kano. Allah ya ba ni ikon cinye jarrabawar da ke tattare da wannan nauyin, amin ya Allah.”

Labarin wannan naɗi ya yi wa masoyan Fauziyya daɗi, musamman ma marubuta. Tuni dai ‘yan’uwa da abokan arziki suka shiga aikawa da saƙon taya ta murna tare da yi matan fatan Allah ya taya ta jagoranci.