• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, July 1, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Yadda Lawan Ahmad ya mari jaruma Hannatu Usman a lokeshin

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
May 10, 2021
in Labarai
2
Yadda Lawan Ahmad ya mari jaruma Hannatu Usman a lokeshin
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ANA zargin ɓacin rai ne ya sanya Lawan Ahmad ya ɗaga hannu ya kwashe jaruma Hannatu Usman da mari a lokeshin ɗin ɗaukar diramar nan mai dogon zango ta ‘Bugun Zuciyar Masoya’.

Wannan abu ya faru ne a Kano a lokacin da ake shirye-shiryen ɗaukar kashi na 37 na shirin, inda jarumar ke fitowa da sunan Nafisa. 

Wata ƙwaƙƙwarar majiya ta faɗa wa mujallar Fim cewa ran Hannatu ya ɓaci ne bayan an faɗa mata cewa labarin ba ya buƙatar ta a wannan lokaci kuma za a canza ta da wata sakamakon haɗari da ta yi a fim ɗin.

Majiyar, wadda ta buƙaci mu sakaya sunan ta, ta ba mu tabbacin cewa an samu matsalar, kuma ta ƙara da cewa, ”Kowane fim ana yin sa ne don riba kuma da man shirin fim mai dogon zango ya gaji haka, a cire ka lokacin da aka ga dama ko kuma ana ganin labarin ba ya yi da kai, sai a cire ka a sa wanda aka ga ya dace.” 

A yayin da majiyar ke bayyana yadda marin ya auku, ta ce, “Kowa ya san Lawan Ahmad ya na da zafi kuma ita jarumar gani ta ke kamar ba za a iya yin fim ɗin ba in ba ta. To bayan an bijiro mata da wannan batun, nan fa ta fara maganganu marasa daɗi wanda har ya kai ga samun matsala da darakta Nura Mustapha Waye inda kuma Lawan Ahmad ya tsoma baki tare da zagin jarumar har ta kai ga ya mare ta.”

Hannatu Usman da darakta Nura Mustapha Waye su na duba labarin ‘Bugun Zuciyar Masoya’ kafin ta fice daga shutin ɗin

Cikin fushi, Hannatu Usman ta yi wani gajeren bidiyo a Instagram inda ta bayyana cewa, ”Ni ba cire ni aka yi a cikin ‘Bugun Zuciyar Masoya’ ba, ni ce nan na cire kai na sakamakon wani abu da ya faru mara daɗi. Duk wani ɗan’adam ba zai jure wulaƙanci ba duk da ana jurewa a yi haƙuri domin gaba in ka na nema a yi maka, amma duk mutumin da zai yi maka abu kan ya maka sai ya wulaƙanta ka ko cin mutunci, haƙura da abin shi ne mafi alkairi.”

Mujallar Fim ta so jin ta bakin jarumar kan wannan batu amma abin ya ci tura saboda ba mu same ta a waya ba.

Sai dai mun samu wanda ake zargi da marin jarumar, wato Lawan Ahmad, don jin haƙiƙanin abin da faru tsakanin su.

Nan take Lawan ya musanta labarin, ya ce shi bai ma san da zancen ba.

Loading

Tags: Bugun Zuciyar MasoyaHannatu UsmanLawan AhmadNura Mustapha Waye
Previous Post

‘Ishara’

Next Post

Kalu ya yi tir da harin da aka kai wa ofishin INEC a Abiya

Related Posts

Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta
Labarai

Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta

June 23, 2025
Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama’a, inji Yerima Shettima
Labarai

Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama’a, inji Yerima Shettima

June 22, 2025
Yadda mahaifin mu ya rasu kwana ɗaya bayan ya dawo daga Makkah – Abba, yayan Rahama Sadau
Labarai

Yadda mahaifin mu ya rasu kwana ɗaya bayan ya dawo daga Makkah – Abba, yayan Rahama Sadau

June 22, 2025
Mahaifin Rahama Sadau ya rasu kwana 1 bayan ya dawo daga aikin Hajji
Labarai

Mahaifin Rahama Sadau ya rasu kwana 1 bayan ya dawo daga aikin Hajji

June 22, 2025
Masanin harshe, Korao Hamadou ya gabatar da haruffan rubutun Hausa na asali a taro a Kano
Labarai

Masanin harshe, Korao Hamadou ya gabatar da haruffan rubutun Hausa na asali a taro a Kano

June 20, 2025
Kotu a Kano ta tsare Tsulange, matashin da ke tare titi yana wanka da yin shigar banza
Labarai

Kotu a Kano ta tsare Tsulange, matashin da ke tare titi yana wanka da yin shigar banza

June 20, 2025
Next Post
Kalu ya yi tir da harin da aka kai wa ofishin INEC a Abiya

Kalu ya yi tir da harin da aka kai wa ofishin INEC a Abiya

Comments 2

  1. Habibu says:
    4 years ago

    Komai naduniya mai kariwane tayi hakuri takoma ai ita hannatu, itace jarumar data fi kayatar wa a shirin.

  2. Yunus saad says:
    3 years ago

    Comment: muna fatan allah yashiga lamarin amma dan allah ki dawo kicigaba da shirin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!