• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, May 14, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Yadda na soma zama darakta – mawaƙiyar Kannywood Farida Ajebo

by DAGA ABBA MUHAMMAD
August 22, 2021
in Mawaƙa
0
Farida Usman

Farida Usman

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FARIDA Usman, wadda aka fi sani da Farida Ajebo, ba sabuwar fuska ba ce a Kannywood, domin kuwa ta daɗe ta na bada gudunmawa a masana’antar a fannoni da dama. Ban da waƙa, Farida jaruma ce, mai shiryawa ce, kuma darakta ce. Ana iya cewa ta biyo sahun tsohuwar jaruma Muhibbat Abdulsalam kenan.

Farida dai santaleliyar yarinya ce mai ladabi da biyayya ga kowa a industiri, har ma da wajen ta, domin duk inda za ka ji an ambaci sunan ta sai ka ji an yabi kyawawan halayen ta.

Mujallar Fim ta tattauna da ita game da rayuwar ta, yadda aka yi ta fara waƙa, nasarori da ƙalubalen da ta fuskanta a masana’antar ta fimafinan Hausa, yadda ta zama jaruma, mai shiryawa, sannan kuma ta fara rikiɗa zuwa mai bada umarni, waye ubangidan ta da dai sauran su. 

Ajebo ba ta yi ƙasa a gwiwa ba wurin amsa dukkan tambayoyin da wakilin mu ya yi mata, kamar haka:

FIM: Ki faɗa wa masu karatu tarihin ki a taƙaice.

FARIDA AJEBO: Assalamu alaikum. Ni dai suna na Farida Usman, amma an fi sani na da Farida Ajeboter, saboda inkiyar ta fi ƙarfi. An haife ni a Jihar Sokoto, amma aiki ne ya kai baban mu can. Daga nan kuma mu ka dawo garin Abuja. A can mu ka girma. Bayan rasuwar kakan mu ne mu ka dawo Kaduna, har na zama cikakkiyar ‘yar Kaduna ta dindindin.

Na yi karatun firamare na a ‘Jibril Memorial’, na kuma yi sakandire na a ‘Karu Secondry School’, sannan na je ‘School of Health’, Maƙarfi, inda na yi ND na da HND a can.

FIM: A ina sunan Ajeboter ya samo asali?

FARIDA AJEBO: Wannan sunan na Ajeboter ya samo asali ne daga wurin mahaifi na. Dalili kuwa, lokacin ƙanwa ta ta na ‘Police Secondary School’ ana kiran ta da Skelegaga, sai ake tambayar ta menene Skelegaga. Sai ta ke cewa ita dai sunan da ta ke so kenan. Sai aka ce mata, “Wato ma Skeleton kenan, kin yarda?” Sai ta ce e, ta yarda. Sai baban mu ya ce, “Ai ‘ya ta ce Ajebo!” To tun daga lokacin ya kasance ana kira na da sunan, har ya bi gari, kowa Ajebo; wasu ma ba su san sunan Faridan ba, sai Ajeboter. Ka ji yadda aka yi na samu sunan kenan.

FIM: Ke wace ƙabila ce?

FARIDA AJEBO: Ni Bafulatana ce daga Jihar Adamawa.

FIM: Ya aka yi ki ka fara waƙa?

FARIDA AJEBO: Wow! Ina son waƙa. Gaskiya ina son waƙa, saboda tun ina sakandire ina ‘Hausa Club’, a lokacin mu ne mu ke rera waƙa. In za a yi taro, za mu haɗu a ce a yi wannan waƙar ko kuma a yi waƙa kaza ko waƙa kaza. A haka dai mu ka fara waƙa, har ya kasance mun gama makaranta. Na zo na haɗu da wasu, su ka ce min ai su su na da situdiyon waƙa. Sai na ce, “Situdiyo fa! Ai ni ma ina so in yi waƙa; mu je!”

Mu ka je. Aka ce min, “Za ki iya kuwa?” Na ce, “Zan iya mana.” Ana  buɗe min sai na rera waƙar nan. Sai na ce, “Ashe zan iya waƙa!” Daga nan ga shi har abin ya girma.

FIM: Da wace waƙa ki ka fara?

FARIDA AJEBO: Gaskiya ni ba zan iya tuna sunan waƙar da na fara yi ba. Amma waƙar dai ta siyasa ce.

FIM: Daga lokacin da ki ka fara waƙa zuwa yanzu, aƙalla kin yi waƙoƙi sun kai nawa?

FARIDA AJEBO: Cab! Gaskiya ban sani ba. Amma a ƙiyasi zan iya cewa za su kai hamsin ko ɗari. Nawa na kai na kuma za su kai ashirin ko fiye da haka ma.

FIM: Ki faɗa mana wasu daga cikin waƙoƙin ki.

FARIDA AJEBO: Akwai waƙar ‘Kafin Aure’,  ‘Matan Gida’,  ‘In Dai Da Tunani’, ‘Mai Kunya’, ‘Da So Mu Ka Saba’, ‘Ki So Ni’, duk waƙoƙi na ne; akwai bidiyon su, da sauran waƙoƙi na. 

FIM: Wanene ubangidan ki?

FARIDA AJEBO: Ina da ubangida, gaskiya. Kuma ba wani ba ne illa Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa).

FIM: Bayan shi babu wani?

FARIDA AJEBO: Akwai abokan sana’ar waƙa, amma wasu sun fi so a kira su da ubangida, kamar El-Mu’az Birniwa, don shi ma zan iya kiran shi da ubangida, domin na kan samu abubuwan alheri da sauran su. 

FIM: Ke ki ke rubuta waƙa da kan ki ko rubuta maki ake yi? Domin yawancin matan da ke waƙa rubuta masu ake yi. Ya ki ke naki tsarin?

FARIDA AJEBO: Gaskiya ni na ke rubuta waƙoƙi na, amma yawancin lokuta idan na rubuta ya rage kamar baiti ɗaya kuma ya gagare ni, na kan je na samu Jibril Jalatu in ce masa ina rubuta waƙa amma na kakare, ya za a yi? Sai ya ce min, “Ki bari mu haɗu” ko kuma, “Zo ki same ni a situdiyo.” Daga nan kawai sai ka ga abu ya cika cif-cif.

FIM: A wane situdiyo ki ka fi jin daɗin yin aiki?

FARIDA AJEBO: A Hannun Dama, situdiyon Ala, wurin Auwal, saboda shi ne zai gyara min waƙa ta ka ji ta ta fita fes.

Farida Usman (Ajeboter): “Ina da ubangida … Alan Waƙa”

FIM: Da wane mawaƙi ki ka fi jin daɗin yin waƙa?

FARIDA AJEBO: Na fi jin daɗin yin waƙa da Jibril Jalatu sosai gaskiya, saboda waƙa ta da shi ta fi tafiya.

FIM: Waɗanne irin nasarori ki ka samu a harkar waƙa?

FARIDA AJEBO: Alhamdu lillahi! Na samu nasarori da dama, saboda  wasu lokutan za ka samu kyautar kuɗaɗe, ko a ce maka an biya maka abu kaza, in za ka je ne ka je, in kuma kuɗin ka za ka karɓa ka karɓi kuɗin ka. Amma dai kyautar kuɗi, ka na zaune wanda ma ba ka taɓa tsammani ba sai ya kira ka ya yi maka kyauta. 

FIM: A wace irin waƙa ki ka fi ƙwarewa? Wasu sun fi ƙwarewa a waƙar siyasa, wasu ta soyayya, wasu ta faɗakarwa, wasu ta jinjina.

FARIDA AJEBO: Gaskiya na fi ƙwarewa a waƙar faɗakarwa sosai fiye da ta soyayya, duk da dai ina yin ta soyayyar ita ma sosai.

FIM: Wace waƙar ki ce ta yi fice?

FARIDA AJEBO: Waƙar ‘Matan Gida’ da ‘Kafin Aure’ su ne su ka yi fice sosai a waƙoƙi na na faɗakarwa.

FIM: Waɗanne irin saƙonni ki ka aika a cikin waƙoƙin?

FARIDA AJEBO: Kamar waƙar ‘Matan Gida’, za ka ga a kan zaman cikin gida ne, gidan haya hakan nan. Za ka ga wata ta raina mijin ta, ta raina uwar mijin ta, ta raina mahaifin sa, kowa nashi abin rainawa ne, sai shi ɗin kawai da ta ke gani, kuma shi ɗin ma bai sha ba a wurin ta. Amma wata a cikin gidan ko kuɗin cefane ba a ba ta, amma ta na haƙuri da duk irin musguna mata da za a yi; dangin miji su zo su yi mata cin mutunci da sauran su, amma ba ta ɗaukar waɗannan abubuwan, za ta yi haƙuri saboda mijin ta da ta ke so. Saboda irin waɗannan abubuwan na yi waƙar ‘Matan Gida’.

Ita kuma waƙar ‘Kafin Aure’, a kan ma’aurata ne. Za ka ga wasu kafin su yi aure za ka ga ana soyayya sosai a waje kamar ba za a rabu ba, babu wulaƙanci. Amma daga an yi auren nan mace ta samu ciki, wasu da ma burin su kenan su ga matar su ta samu ciki, ta na samun cikin nan ta zama abar wulaƙantawa a wurin su. Ko me za ta yi ba za ta burge su ba, sun gwammace su je wurin wata ko su ɗauko wata su kawo ta gidan don su wulaƙanta matar su a idon duniya. To, saboda irin wannan abin ne na yi waƙar ‘Kafin Aure’.

FIM: Saƙonnin da ki aika sun isa wurin?

FARIDA AJEBO: Gaskiya saƙonni sun isa yadda ya kamata, domin daga irin kiran da ake yi min a waya na gane saƙonni na sun isa yadda ya kamata.

FIM: Ina da ina harkar waƙa ta kai ki?

FIM: Gaskiya na je jihohi da yawa, irin su Adamawa, Kamaru, Nijar da sauran su duk na je ta dalilin waƙa.

FIM: Menene alaƙar Ajebo da fitaccen mawaƙin nan Ahmad Shanawa?

FARIDA AJEBO (dariya): Lallai kam! Ahmad Shanawa aboki na ne, kuma ɗan’uwa na ne na sosai, kuma abokin sana’a ta ne. Saboda kaf industiri an san Ajebo da Shanawa; da an ga Ajebo sai ka ji an ce ai ga Shanawa nan, nan kuma ba a san ba tare da Shanawan na ke ba. Don haka Shanawa ɗan’uwa na ne ta ɓangaren Jos, saboda iyaye na sun yi zaman Jos, kuma ni ma na yi zaman Jos. Dalilin haka ne mu ka shaƙu da shi, ga shi kuma mu na da dangantaka. Amma ba wata alaƙa ba ce tsakani na da shi. 

Farida Ajebo

FIM: Amma wasu na cewa soyayya ce tsakanin ku, domin an ga ya na yawan aiki tare da ke.

FARIDA AJEBO: Ƙwarai da gaske, ba wai waƙoƙi ba ma kawai, har fim mai dogon zango mun yi tare, ‘Ƙauran Mata’. Wannan fim ɗi na ne, ni na shirya. Kuma ko waƙoƙin ma duk waƙoƙi na ne. Ina amfani da shi ne kamar yadda na ke amfani da sauran mawaƙan a waƙoƙi na.

FIM: Wato kenan ba a iya waƙa ki ka tsaya ba; ke jaruma ce kuma mai shiryawa?

FARIDA AJEBO: Wannan haka ya ke.


FIM: Da ma can tun da ki ka shigo masana’antar da wannan tunanin ki ka shigo na zama jaruma kuma mai shiryawa?

FARIDA AJEBO: Gaskiya daga baya ne tunanin zama jaruma ya shiga jiki na, domin kowa sai a rinƙa ce min gaskiya ya kamata in yi fim, “kin ga surar ki kuwa irin ta jarumai?” Tun dai ina tunanin kada waɗannan su yaudare ni, na zo na fara gwadawa, na ce abin fa ya yi kyau, na ce shi kenan bari na ci gaba. Cikin ikon Allah, ana zaune sai ka ji an ce a kira Ajebo ta yi aiki. Ka ga alhamdu lillahi.

FIM: Kin taɓa aure?

FARIDA AJEBO: Ban taɓa aure ba.

FIM: In na fahimce ki, kenan a kasuwa ki ke?

FARIDA AJEBO (dariya): A’a, ni ba a kasuwa na ke ba!

FIM: Ina aka tsaya da maganar aure yanzu?

FARIDA AJEBO: In Allah ya kawo miji nagari, sai a yi auren ai.

FIM: Wane irin ƙalubale ki ka taɓa fuskanta a masana’antar?

FARIDA AJEBO: Ka san mutane, ba ka raba su da ka-ce-na-ce a gari, waɗanda ba ka haɗa komai da su ba, babu ruwan ka da su, su ne su ka fi sa maka ido. Sai ka zo wuri ka wuce, sai ka ji ana cewa ai wane kaza ne, ɗan iska ne, ko a ce wani abu kaza. 

Amma ɓangaren gida ban samu ƙalubale da iyaye na ba. Mahaifi na bai hana ni ba, mahaifiya ta tun ba ta so har ta zo ta gane babu aibu, tunda ba wani abu mu ke yi ba, ta amince ta sa min albarka. Amma in dai mutanen gari ne, sai dai ka kalle su ka ƙyale.

Farida Ajebo: Ba soyayya mu ke da Ahmad Shanawa ba

FIM: Ina maganar kan-ta-waye? Ko Ajebo ta taɓa faɗawa hannun ‘yan kan-ta-waye?

FARIDA AJEBO: Kan-ta-waye? Gaskiya ban taɓa shiga ba.

FIM: Mecece shawarar ki ga masu irin wannan hali na kan-ta-waye?

FARIDA AJEBO: Ka san yawancin masu wannan halin ba laifin su ba ne, laifin waɗanda ke kawo kan su wurin su ne su ce lallai ala dole sai sun samu abin da su ke so a lokacin da su ke so su ke yi wa haka. Kuma ai masu kan-ta-wayen a ƙarshe ba su samun abin da su ke so. Kuma idan ka duba, yawancin ‘yan kan-ta-waye ɗin nan su fa ba kowa ba ne a masana’antar, su dai kawai inda su ka tsaya kenan. Amma gaskiya da so samu ne, su bar mutane su wataya; in ka san ba ka da hanyar yi wa mutum abu ka ba shi haƙuri ka ce ya je ya nemi waɗanda su ke yin abin bilhaƙƙi da gaskiya, ba sai ka ɓata masa lokaci ko cin zarafin sa ba.

FIM: Fim nawa ki ka shirya da kuma waɗanda ki ka fito a ciki?

FARIDA AJEBO: Gaskiya ban yi finafinai da yawa ba yanzu, don ba za su wuce biyar ko shida ba. Akwai ‘Ƙauran Mata’, wanda mu ka yi a Jos, wanda ake nuna shi a YouTube channel na Ahmad Shanawa; sai ‘Sanin Masoyi’, fim ɗin Kaduna ne. Amma sauran finafinan gaskiya ban ma riƙe sunan su ba. Sai kuma wanda za a yi a nan gaba, ‘Alwashi’.

Farida Ajebo ta ce ta fi jin daɗin yin waƙa da Jibril Jalatu

FIM: Ganin cewa ke mawaƙiya ce, jaruma kuma mai shiryawa, ko ki na da sha’awar zama mai bada umarni a nan gaba?

FARIDA AJEBO: Ƙwarai kuwa. Saboda kwanaki da na ce ina so in zama darakta, ana daraktin wata waƙa ce ta El-Mu’az, ‘Amatullah’, Hassan Giggs ke aikin bada umarni, sai na ce, “Ya za a yi a ce ga abin da waƙa ke cewa, ku kuma ga abin da ku ka zo ku na ɗauka?” Sai aka ce min, “Haka ne?” Sai na ce, “E.” Sai Rabi’u Gumel ya ce, “In dai haka ne, ku gwada yarinyar nan.” 

Ina gida, sai aka kira ni: “Ajeboter ki na ina?” Na ce ina gida. Sai su ka ce, “Ki zo ki same mu a Mogadishu.” Ina zuwa, sai aka ce min, “Ga waƙar nan, ai ke za ki bada umarni.” Na ce, “Wacce?!” Sai aka ce min, “Waƙar nan da ki ka ce an yi daraktin ba ta yi ba.” Na ce, “Sake ta za a yi?” Su ka ce, “Sake ta za a yi da Asabe Madaki.” 

Na bada umarnin waƙar, kuma waƙa ta bada abin da ake so. Ka na ganin nan gaba in-sha Allahu zan zama babbar darakta.

“Ni ma ina son ku kamar yadda ku ke so na,” inji Farida Ajeboter ga masoyan ta

FIM: Mecece shawarar ki ga abokan sana’ar ki?

FARIDA AJEBO: Shawara ta ga abokan sana’a ta mu ƙara haƙuri, saboda komai sai a hankali ake samun shi. Su kuma manyan mu haƙuri za su yi, duk wanda ya cancanci a ba shi aiki a daure a ba shi ya yi, kada a ce wannan ai bai da kaza da kaza. Turawa babu ruwan su da wannan; in dai za ka iya abu, an gwada ka, za su ba ka ka yi. Amma a nan kuwa ka na da basirar yin abu sai a ce, “Mu ba wannan mu ke so ba.” Don haka haƙuri za su yi su daure su ba kowa damar sa ya gwada, saboda a samu cigaba a nan gaba.

FIM: Ya alaƙar ki ta ke da sauran mawaƙa mata ‘yan’uwan ki, irin su Fati Khalil, Zubaida Mu’azu, Khairat Abdullahi, har ma da irin su Fati Nijar, Maryam A. Baba, Murja Baba da sauran su?

FARIDA AJEBO: Gaskiya akwai alaƙa mai ƙarfi tsakani na da su Fati Khalil, Zubaida, Khairat da sauran su. Ƙawaye na ne sosai, kuma mu na mu’amala mai kyau. Ban taɓa samun saɓani tsakani na da su ba. Alhamdu lillahi, ka ga ana tare kenan.

FIM: A ƙarshe, me za ki ce wa masoyan ki?

FARIDA AJEBO: Masoya na ina ƙara godiya da kallon waƙoƙi na da ku ke yi, kira na a waya  da ku ke yi. Allah ya bar zumunci, Allah ya bar ƙauna. Ni ma ina son ku kamar yadda ku ke so na. 

Farida Usman ta ce mahaifin ta ne ya sanya mata laƙabin ‘Ajeboter’

FIM: Farida, mun gode.

FARIDA AJEBO: Ni ma na gode, Abba.

Loading

Tags: Ahmad ShanawaAlan WakaAminu Ladan Abubakar AlaEl-Mu'az BirniwaFarida AjeboFarida AjeboterFarida UsmanHausa musicJibril JalatuKannywoodmawakan hausaMawakiya
Previous Post

A manyan ‘yan Hisbah akwai manema mata, inji jarumar Kannywood Ummah Shehu

Next Post

Illa ga ‘Farin Wata’, ɓarayin intanet sun ƙara sace wa Adam Zango shafin Instagram

Related Posts

Za a yi bikin naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa a Daura ranar Asabar
Mawaƙa

Za a yi bikin naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa a Daura ranar Asabar

December 11, 2025
Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi
Mawaƙa

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi

April 19, 2025
Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala

October 28, 2024
Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala

July 16, 2024
Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara
Mawaƙa

Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara

May 13, 2024
Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 
Mawaƙa

Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 

December 7, 2023
Next Post
Illa ga ‘Farin Wata’, ɓarayin intanet sun ƙara sace wa Adam Zango shafin Instagram

Illa ga 'Farin Wata', ɓarayin intanet sun ƙara sace wa Adam Zango shafin Instagram

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!