• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

A manyan ‘yan Hisbah akwai manema mata, inji jarumar Kannywood Ummah Shehu

by DAGA IRO MAMMAN
August 21, 2021
in Labarai
0
A manyan ‘yan Hisbah akwai manema mata, inji jarumar Kannywood Ummah Shehu
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCIYAR jaruma Ummah Shehu ta bayyana cewa wasu daga cikin shugabannin  Hukumar Hisbah ta Jihar Kano manema mata ne.

Jarumar ta masana’antar finafinan Hausa ta Kannywood ta faɗi haka ne jiya lokacin da ta ɓara kan kama jaruma kuma furodusa Sayyada Sadiya Haruna da ‘yan Hisbah su ka yi jiya Juma’a a Kano, ta ce sam ba a yi wa Sadiyar adalci ba.

Idan kun tuna, ‘yan Hisbah sun kama Sadiya ne saboda irin kalaman batsa da ta ke amfani da su wajen tallata kayan gyaran aure da na gyaran jiki a soshiyal midiya.

Hukumar ta ce za ta gurfanar da ‘yar kasuwar a kotu a kan tuhumar yaɗa baɗala ta hanyar kafofin sada zumunta na zamani.

Wannan kamu da aka yi mata ya ɓata ran Ummah Shehu har ta yi nuni da cewa su ma masu kamun ai ba ma’asumai ba ne, kuma idan ta fallasa sunayen manema mata da ke cikin manyan su za a sha mamaki.

Mujallar Fim ta kwafo kalmomin da jarumar ta furta cikin saƙon bidiyo mai tsawon minti uku wanda ta wallafa a Instagram, inda ta yi iƙirarin cewa, “Ko ‘yan Hisban, ni in na ce zan kira suna ma za a ji ba daɗi. Akwai masu neman matan, su ma. Wallahi, wallahi in ka ce za ka kira suna sai an yi mamaki – ‘yan Hisbah, kuma manyan su!”

Ummah ta ɗauki bidiyon saƙon ta ne a lokacin da ta ke tuƙa motar ta, su na tafiya a cikin gari tare da wata ƙawar ta mai suna Zizi. 

Tare da farawa da sallama, ta ce, “Na ji an ce wai an kama Sadiya Haruna. Ikon Allah! Sadiya Haruna ta yi laifin da wai yanzu za a kama ta! Ba za ku iya gaya mata gaskiya ba in ta yi ba daidai ba, amma kun ce kun kama ta wai za ku gurfanar da ita a gaban kotu. 

“Ubangiji ne ya ce, ‘Kar ka shiga tsakani na da bawa na.’ To meye naku? Meye naku? 

Ummah Shehu da ƙawar ta Zizi a cikin bidiyon da jarumar ta wallafa sannan ta goge shi daga baya

“Ni wannan abu ya na ba ni mamaki. Abin da ba ruwan ka daɗin kallo ne da shi. In ka na tare da ita ka gaya mata gaskiya, in kuma ba za ka gaya mata gaskiya ba, ka sa mata ido. Allah ya ce, ‘Kar ka shiga tsakani na da bawa na’, amma kun zo kun yi kane-kane.

“Wai ‘yan Hisba sun shiga: meye naku a ciki? Meye nasu? ‘Kar ka shiga tsakani na da bawa na,’ haka Ubangiji ya faɗa, amma sun shiga.

“Su ma wannan abin da su ka yi, laifi ne wallahi. Wallahi, wallahi laifi ne tunda Allah bai ce, ‘Ka shiga tsakani na da bawa na’ ba. 

“Ba dai ta amshi kalmar shahada, ‘La ilaha illallah Muhammadar rasulullahi sallallahu alaihi wa sallam’ ba? To meye naku? 

“Menene naku na shiga ku yi kane-kane saboda Sadiya Haruna ta na wani abu mara kyau? To a cikin mara kyau ɗin in ta na yin mai kyau fa? Allah zai iya shirya ta wata rana. Wallahi in ta na yin mai kyau, Zizi, wata rana za ta iya bari.”

A daidai nan, sai ƙawar jarumar, wato Zizi, ta karɓe da cewa: “Sannan kuma wani abu shi ne wannan abin da ta ke yi, tsakanin ta da Allah ne. Yau in da Sadiyar nan ta zagi Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ne, duk gaban kotun da za a kai ta, ba ‘yan Hisbah ba, duniya ma sai ta zage ta. 

“Shi rayuwan nan kowa ya yi abin da ya ga zai iya shi ya ke yi.”

Zizi ta yi kira ga ‘yan Hisbah da cewa, “Don Allah don Annabi a daina shiga hurumin da ba na mutane ba, maganar gaskiya! Ba kyau wallahi tallahi. Haba!

“Duk ɗan’adam ba wanda ba ya da laifi wurin Ubangiji, kowa ya na da laifi wurin Ubangiji.”

A nan kuma sai Ummah Shehu ta ce: “Wallahi tallahi ni abin na ɗaure min kai. Meye na ‘yan Hisbah na shiga abin da ba ruwan su? Me ya sa za su kama Sadiya Haruna? Laifin me ta yi masu? 

“Sadiya Haruna laifin ta tsakanin ta da Ubangiji ne. Ku kun isa ku je lahira ku ce kun zo za ku   hukunta Sadiya Haruna ne saboda ta yi wani abu? Wannan hukuncin na Ubangiji ne, ba nasu ba ne.

“Mu yi ma kan mu adalci; ka yi da kan ka kafin a yi da kai.”

A cikin hassala, Ummah Shehu ta ce, “Ko ‘yan Hisban, ni in na ce zan kira suna ma za a ji ba daɗi. Akwai masu neman matan, su ma. Wallahi, wallahi in ka ce za ka kira suna sai an yi mamaki – ‘yan Hisbah, kuma manyan su! Bari in gaya miki.

“Wallahi ba wanda bai da laifi sai wanda ya fi kowa ya na da laifi wajen Ubangiji. Ba wanda ya ke zama ma’asumi, na rantse da Allah. Wannan wane irin rayuwa ne?”

Ummah ta kwatanta Kano da Kaduna inda ta ke da zama, ta ce, “Ni fa shi ya sa na ke son garin mu, saboda mu ba a yi mana wannan. Shi dai Malam (Gwamna El-Rufa’i) sai abin da doka ta kama, shi ya ke yi.”

Daga nan ta yi kira ga ‘yan Hisbah na Kano da su saki Sadiya Haruna. Ta ce, “Sadiya Haruna, gaskiya ku sake ta. Ni ban ga amfanin shiga hurumin da ba naku ba. Ni dai ban gani ba. Ba ku da hurumin da za ku shiga hurumin Sadiya Haruna ko tsirara ta ke yawo, ko tsirara ta ke yawo!”

A ƙarshe, jarumar ta jaddada mamakin ta kan abin da ya faru, ta ce, “Wai za a gurfanar da ita a gaban kotu, sai ka ce ta kashe mutum! Sadiya fa ba Manzon Allah ta zaga ba.”

Wannan saƙo da Ummah Shehu ta tura dai ya fara jawo mata surutai. Mutane da dama a soshiyal midiya sun fara zagin ta, har wasu na kiran ta da wadda ba ta san addinin Musulunci ba.

Mujallar Fim ta lura da cewa har wasu daga cikin masu sukar ta ɗin sun kwafo guntun bidiyon wata hira da jarumi Aminu A. Shariff (Momoh) ya taɓa yi da ita a filin sa na hira da ‘yan fim a tashar talbijin ta Arewa24 inda jarumar ta kauce wa amsa wasu tambayoyi da ya yi mata.

Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Malam Haruna Ibn Sina

A bidiyon dai an tambayi Ummah sunan wadda ta shayar da Anbabi (s.a.w.), ita kuma cikin dariya ta amsa da cewa: “Ya za mu zo nan kuma? Ya za ka yi min haka?”

Momoh ya kuma tambaye ta idan ta sauke Alƙur’ani da kuma ko izifi nawa ta yi, tambayoyin da ba ta bada gamsassun amsoshi ba.

Ganin caa da aka yi mata dai sakamakon wannan kare Sadiya Haruna da ta yi, sai Ummah Shehu ta goge bidiyon nata daga shafin ta na Instagram.

Ɗazu da mujallar Fim ta duba, sai ta ga babu shi babu alamar sa.

Copyright © Fim magazine. All rights reserved
www.fimmagazine.com

Loading

Tags: hausa actorshausa filmsHukumar HisbahKannywoodKano State Hisbah BoardMalam Haruna Ibn SinaSadiya HarunaUmmah Shehu
Previous Post

Me ya farraƙa Adam Zango da Ummi Rahab?

Next Post

Yadda na soma zama darakta – mawaƙiyar Kannywood Farida Ajebo

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Farida Usman

Yadda na soma zama darakta - mawaƙiyar Kannywood Farida Ajebo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!