• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, May 14, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Illa ga ‘Farin Wata’, ɓarayin intanet sun ƙara sace wa Adam Zango shafin Instagram

by DAGA ABBA MUHAMMAD
August 22, 2021
in Labarai
0
Illa ga ‘Farin Wata’, ɓarayin intanet sun ƙara sace wa Adam Zango shafin Instagram
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

‘YAN dandatsa (hackers) a jiya sun ƙara samun nasarar ƙwace wa Adam A. Zango shafin sa na Instagram, wanda wannan shi ne karo na uku da su ka yi masa haka.

Wani mai lura da al’amuran Kannywood ya faɗa wa mujallar Fim cewa babu shakka sace shafin zai illata yunƙurin da fitaccen jarumin ya ke yi na tallata sabon fim ɗin sa mai dogon zango na ‘Farin Wata Sha Kallo’.

Zango, wanda kuma fitaccen mawaƙi ne, ya fara shiga wannan tsaka-mai-wuya ne tun daga lokacin da ɓarayin intanet masu kutse su ka fara ƙwace masa shafin Instagram mai ɗauke da mabiya sama da miliyan ɗaya da dubu ɗari takwas (1.8m).

Bayan an sace shafin nasa a wancan lokacin, jarumin ya yi iyakacin ƙoƙarin sa don ganin an dawo masa da shi, amma abin ya faskara. Wannan dalilin ya sa ya buɗe sabon shafi, amma ba a kwana biyu ba su ka sake ƙwace shi.

A lokacin, har Zango ya ce ya haƙura da buɗe shafi a Instagram, domin ya na da yaƙinin cewa magabtan sa ne su ka taso shi a gaba.

Daga baya kuma, bisa shawara tare da damuwar makusantan sa da masoyan sa, sai ya sake buɗe wani shafin mai suna @officially_a_zango.

Shafin ya samu sama da mabiya 82,000 ya zuwa jiya Asabar, 21 ga Agusta, 2021, lokacin da aka ƙwace shi.

Wasu da dama har sun fara tunanin jarumin ya fara bulokin ɗin mutanen da bai aminta da su ba ne, sai daga baya aka gane ashe an sake ƙwace sabon shafin nasa ne. 

Ɗaya daga cikin yaran Zango, Umar Bigshow, shi ne ya bada sanarwar sace shafin da aka yi, inda ya tura saƙon hoton shafin jarumin ɗauke da jan rubutu cewa ‘Hacked’, daga ƙasa kuma ya rubuta, “Allah ya fi ku.”

Al’amarin ya baƙanta wa masoyan Zango rai matuƙa, musamman a daidai wannan lokaci da ya ke amfani da Instagram wajen tallata fim ɗin sa na ‘Farin Wata Sha Kallo’.

Mutane da dama na mamakin yadda irin wannan abu ya ke faruwa ga babban manishaɗanci kamar Zango amma ya kasa shawo kan matsalar. Akwai ƙananan jarumai da mawaƙa da ma sauran jama’a da irin haka na faruwa da su, amma kuma cikin ƙanƙanen lokaci su ke samun nasarar dawo masu da shafukan su.

A shekarun baya, ɓarayin intanet sun taɓa yin kutse a shafin Facebook na Ali Nuhu, sai nan da nan jarumin ya biya wani ɗan ƙasar Indiya kuɗi, ya samu nasarar dawo masa da shafin nasa. Wannan dalilin ne ya sa Alin ya koma amfani da sunan “Ali Nuhu Mohammed” a Facebook.

To ko shi ma Adam A. Zango zai yi irin wannan tunanin na Ali Nuhu don ya samu gyara wannan matsalar da ya ke fuskanta? Ko kuma daga wannan sabon harin da aka kai masa zai haƙura ne da yin Instagram gaba ɗaya? Za mu gani.

Loading

Tags: Adam A. ZangoFarin Wata Sha KalloHackershausa filmsInstagramKannywood
Previous Post

Yadda na soma zama darakta – mawaƙiyar Kannywood Farida Ajebo

Next Post

Hotuna: Dinar auren Garzali Miko

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Hotuna: Dinar auren Garzali Miko

Hotuna: Dinar auren Garzali Miko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!