• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, April 5, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Yadda ‘yan Kannywood su ka haska a bikin rantsar da gwamnan Kano

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
June 1, 2023
in Labarai
0
Dandazon 'yan fim da mawaƙan Kannywood a wajen taron

Dandazon 'yan fim da mawaƙan Kannywood a wajen taron

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

DUK da ɗimbin jama’ar da su ka taru a taron rantsar da sabon Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a ranar 29 g Mayu, hakan bai hana jarumai da kuma mawaƙan Kannywood ɗaukar hankalin mahalarta ba.

‘Yan Kannywood ɗin dai sun haskaka wajen da waƙoƙi da kuma dirama da su ka gabatar a dandamalin taron inda su ka samu kyakkyawan yabo da kuma jinjina daga ɗimbin jama’ar da ta taru domin gane wa idon su rantsarwar.

Fitattun mawaƙan da su ka gabatar da waƙa a wajen sun haɗa da Abubakar Sani, Sadi Sidi Sharifai, Yakubu Muhammad, Sani Danja, Maryam A. Baba, Nazifi Asnanic da jarumar TikTok ɗin nan, Murja Ibrahim Kunya.

Su ma jarumai ba a bar su a baya ba wajen baje kolin tasu fasahar. Fitattun jarumai irin su Abba Al-Mustapha, Rabi’u Daushe, Abdullahi Adamu Abdullahi, da Abale sun gwada fasahar su, kowanne sanye da jar hula ko jan ɗankwali.

Su Sani Danja da Yakubu Muhammad a taron

Baya ga haka akwai wasu masu gudanar da sana’ar fim da su ka halarci wajen, kamar Salisu Muhammad Officer, Umar Ƙofar Mazugal, Sunusi Oscar, da Alhassan Kwalle.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa a baya yawancin ‘yan Kannywood sun ƙaurace wa yaƙin neman zaɓen Abba Gida-Gida, sun tare a inuwar jam’iyyar APC. Hakan ya sa ake ganin kamar gwamnatin sa ba za ta tafi tare da su ba, amma halartar waɗannan manyan jarumai da mawaƙan ya tabbatar da cewa su ma za a dama da su. Tuni ‘yan fim da suke da alaƙa da gwamnatin su ka fara zawarcin kujerar Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano.

Murja Ibrahim Kunya na gabatar da waƙa
Abba Al-Mustapha na ɗaukar salfi
Daga hagu: Tijjani Faraga, Murja, Abale Yakubu, da Sani a taron
Abale da Al-Mustapha
Umar Ƙofar Mazugal (a dama) da Salisu Officer
Rabi’u Daushe
Yahanasu Sani tare da su Abdullahi Adamu Abdullahi Abale
Abba Al-Mustapha da Adam M. Kirfi
Abale na ɗaukar salfi

Loading

Previous Post

Shawarar MOPPAN ga gwamnan Kano: Yi aiki tuƙuru ka ba maraɗa kunya

Next Post

An yi bikin Zainab ɗiyar marubuciya Alawiyya Wada Isa

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Amarya Zainab Sunusi (a dama) tare da mahaifiyar ta, Hajiya Alawiyya Wada Isa a lokacin bikin auren

An yi bikin Zainab ɗiyar marubuciya Alawiyya Wada Isa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!