DARAKTA a Kannywood kuma kansilan mazaɓar Tudun Wada ta Kudu a Kaduna, Honarabul Abubakar Labaran Haruna Gambo, wanda aka fi sani da Abu Sarki, ya bayyana cewa ɓarayi masu garkuwa da mutane sun kashe ƙanen sa a jiya kamar yadda su kashe masa mahaifi shekara uku da ta gabata.
Haka kuma ya ce shi da mahaifin da ƙanen nasa sun taɓa tattaunawa kan irin artabun da za su iya yi da ‘yan kidinafin wata rana.
Ya ce kila shi ma irin wannan gisan killar za a yi masa.
A wani rubutu mai ban-tausayi da mamaki da ya yi a Facebook a yau Laraba, 19 ga Oktoba, 2022, daraktan ya faɗi irin muhawarar da su ka yi tsakanin su da mahaifin su da ƙanen sa wata rana su na dawowa daga gona game da masu garkuwa da mutane.
Abin ikon Allah, masu garkuwa da mutanen ne ajalin mahaifin da kuma ƙanen nasa da su ka kashe jiya a garin Udawa, kafin a ƙaraso Buruku.
A rubutun da ya yi a Facebook, Abu Sarki ya ce: “Yau shekaru uku kenan mu na tafiya mu uku, kamar misalin ƙarfe 3:00 na rana, mu na dawowa daga gona, kowa da gasasshiyar masara a hannun sa cikin motar mu, sai baban mu marigayi Alh. Labaran Haruna Gambo, ya ke cewa, ‘Abu Sarki, ba fata ake yi ba, amma duk ranar da Allah ya haɗa mu da ‘yan kidinafin sai dai su kashe ni, domin ni ba zan yarda namiji ɗan’uwa na ya tasa ni a gaba kamar tunkiya ya kora ni daji ba. Sai dai su kashe ni!’
“Sai ƙane na, Abba Labaran Haruna Gambo, ya ƙara da cewa ai ko shi ma ba zai bi su ba, sai dai duk abin da zai faru ya faru kawai.
“Daga nan ni ma na ce, ‘Ba zai yiwu ba, dole sai an fafata. Idan na yi nasara na kashe su, idan kuma sun yi nasara a kai na, shi kenan, Allah ya yi min rahama!’
“Watanni kaɗan sai Allah ya ƙaddara haɗuwar su da baban mu Alh. Labaran Haruna Gambo, su ka kuma buɗe masa wuta, ya yi shahada. Jiya kuma Allah ya ƙara ƙaddara shahadar Abba Labaran Haruna Gambo a hannun su ta hanyar kisan gilla kamar yadda su ka yi wa mahaifin sa. Yau mun kai Abba kabarin sa a gefen na Alh. Labaran.”
Abu Sarki ya ci gaba da cewa, “A cikin mu ukun nan yau sai ni kaɗai na rage a raye, kuma duk sun tafi ne sakamakon kisan gilla a hannun ‘yan kidinafin. Ina jin ni ma nan ba da daɗewa ba ni ma zan bi su. Ta yiwu ni ma ta hanyar da baba na da ƙane na su ka bi ta nan zan bi. Ni dai na san ba zan shiga hanyar ‘yan kidinafin ba, amma su za su iya shiga hanya na.
“‘Yan’uwa, iyaye da abokan arziƙi, ina roƙon ku da addu’a a duk yayin da ku ka samu labarin mutuwa ta.
“Mahaifiya ta, ƙanne na da kuma ‘ya’ya na Allah ya zama gatan su.”
A jiya Talata, 18 ga Oktoba, 2022 Allah ya yi wa Abdullahi Labaran Haruna Gambo, wanda aka fi sani da Abba, rasuwa.
Abba ya rasu sakamakon harbin da masu garkuwa da mutane su ka yi masa a hanyar sa ta dawo gona daga garin Udawa, Jihar Kaduna, shi da wani Inyamiri abokin tafiyar sa, da misalin ƙarfe 6:00 na yamma.
An yi jana’izar sa a safiyar yau Laraba, 19 ga Oktoba, da misalin ƙarfe 8:00 na safe.
Kamar yadda Abu Sarki ya sanar wa mujallar Fim, ƙanen nasa sun je gonar ne tare da ƙanen mahaifiyar su da wannan Mista Geoge, domin ɗauko samfur na wani dutse mai daraja (precious stone), wanda da ma akwai shi a gonar Abban wanda ya ci gado, don har an fara haƙar dutsen sai daga baya su ka dakatar da haƙar. Shi kuma Geoge dama harkar sa ce, sai ya buƙaci ya na son dutsen, shi ne su ka tafi ɗauko samfur. A kan hanyar su ta dawowa ‘yan kidinafin su ka tare su, inda a take su ka kashe Abba da Geoge, shi kuma ƙanen mahaifiyar su Allah ga kuɓutar da shi.
Allah ya jiƙan Abba da rahama.
Allah ya gafarta musu. Shawarata ga shi Darakta, shi ne ya cire jinncewa ya kusa haduwa da azzaluaman nan. Ya rungumi addu’ar tsari, ya kuma sa a rika yi masa addu’a. Allah ya tsare mu baki daya.