WASU zauna-gari-banza da ba a san ko su waye ba sun banka wa gidan mawaƙi Dauda Abdullahi Kahutu (Rarara) wuta a safiyar yau, a wani hari da bai rasa nasaba da siyasa.
‘Yan iskan sun kai harin ne jim kaɗan bayan da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan Jihar Kano. Ya kayar da Dakta Nasiru Gawuna na APC a zaɓen.
Rarara fitaccen magoyin bayan Gawuna ne a yaƙin neman zaɓen, inda ya rera waƙoƙi da dama na yabon gwanin nasa tare da ƙasƙantar da abokan adawa.
A cikin ‘yan kwanakin nan, wasu mutanen Kano sun riƙa sukar mawaƙin a kafafen yaɗa labarai, har ana yi masa yarfen cewa shi ba ɗan Kano ba ne, wai ya koma Jihar Katsina ya yi harkar sa ta siyasa a can.
Ita ma jaruma A’isha Ahmed Idris (Ayshatulhumairah), wadda mai taimaka wa Rarara ce ta musamman kuma wadda ta nuna goyon bayan ta muraran ga Gawuna, ta gamu da fushin masu irin wannan tunanin, su na cewa ita ma ta koma jihar ta ta Borno, ta bar Kanawa da siyasar su.
A ranar Asabar da ta gabata wasu mutane sun so su hana ta yin zaɓe, su na iface-iface a mazaɓar ta a Kano, amma Allah ya kiyaye.

A da, Rarara ya goyi bayan ɗan takarar gwamna na jam’iyyar ADP ne, wato Sha’aban Ibrahim Sharaɗa, saboda ɓatawar sa da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, kafin su sasanta ya koma APC.
Majiya ta faɗa wa mujallar Fim cewa waɗanda su ka kai hari a gidan mawaƙin a yau, sai da su ka fara da farfasa kayayyakin gidan kafin su banka masa wuta.
Daga baya ‘yan sanda sun je sun tarwatsa masu kai harin, amma wuta ta ci gaba da ci, kuma ba a ga zuwan ‘yan kwana-kwana ba don su kashe ta.
Wani wanda aka yi abin a gaban sa, Yusuf Abdullahi, ya faɗa wa jaridar News Point Nigeria cewa: “Ba ka jin komai sai ƙarar fashewar kayayyaki daga gidan, a yayin da wutar ta ci gaba da lalata kayayyaki.”
Mujallar Fim ba ta gano ko Rarara ya na gidan a lokacin harin ba, da kuma ko wani daga cikin iyalan sa ya ji rauni.