• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

‘Yan sanda sun maka jarumar Kannywood Amal Umar a kotu kan zargin ta ba su cin hanci

by ALI KANO
March 20, 2024
in Labarai
0
‘Yan sanda sun maka jarumar Kannywood Amal Umar a kotu kan zargin ta ba su cin hanci

Amal Umar da Ramadan Inuwa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

‘YAN sanda a Kano sun maka jarumar Kannywood Amal Umar a kotu bisa zargin ta nemi ta hana binciken wata almundahanar kuɗi ta hanyar ba da toshiyar baki ga wani ɗan sanda mai bincike.

An gurfanar da ita ne a yau a gaban Kotun Majistare mai lamba 24 da ke Gyaɗi-Gyaɗi, Kano.

Kakakin rundunar ‘Yan Sanda Shiyya ta 1, wato ‘Zone One’, CSP Bashir Muhammad, ya faɗi a cikin wata hira da manema labarai a yau cewa Amal ta yi ƙoƙarin ba da cin hancin ne ga wani ɗan sanda mai suna ASP Salisu Bujama domin ya daina binciken zargin almundahanar da ake zargin wani saurayin ta da aikatawa.

Idan kun tuna, mujallar Fim ta taɓa ba ku labarin cewa a ranar 18 ga Agusta, 2022, wani ɗan kasuwa mai suna Alhaji Yusuf Adamu ya shigar da koke ta hannun lauyan sa, H.I. Dederi, wajen Mataimakin Sufeto mai kula da Shiyya ta 1 ɗin, wato AIG Umar Mohammed Sanda, ya na ƙarar saurayin Amal Umar mai suna Ramadan Inuwa, a kan cewar ya ba shi kuɗin kasuwancin wayar salula har naira miliyan 40, amma tun da ya ba shi kuɗin bai sake ganin sa ba.

CSP Bashir Muhammed ya shaida wa ya shaida cewa jaridar Idongari.ng cewa a binciken da su ke yi a tsawon wannan lokaci ‘yan sanda sun gano cewar daga cikin waɗannan kuɗi Ramadan ya tura wa Amal naira miliyan 13 a asusun ta na banki.

Ya ce sun gayyaci jarumar domin ta amsa wasu tambayoyi inda ta faɗa masu cewa a gaskiya kuɗin da ke cikin asusun ta na saurayin ta ɗin ne, to amma fa naira miliyan takwas ne.

Daga nan su ka ba da belin ta bayan sun riƙe motar ta mai lamba NSR 858 JH domin ana zargin cewa Ramadan ne ya saya mata ita.

Da aka ba da belin ta, sai Amal ta garzaya Babbar Kotun jihar inda ta nemi a hana ‘yan sandan ci gaba da binciken da su ke yi a kan ta.

Da jarumar ta samu wannan damar daga kotun, sai ta je ofishin rundunar ‘yan sandan domin ta karɓi motar ta, inda a can kuma ta yi yunƙurin toshe bakin mai binciken, wato ASP Salisu Bujama, da kuɗi N500,000.

CSP Bashir ya ce jarumar ta ba Bujama kafin alƙalami na N250,000, shi kuma sai ya kama ta da laifin ta ba shi cin hanci.

CSP Bashir ya ce bayan sun samu wannan hujjar ne su ka gurfanar da Amal a gaban kotun majistare da ke Gyaɗi-Gyaɗi bisa zargin ta yi yunƙurin ba da cin hanci ga ɗan sanda wanda hakan ya saɓa wa Sashe na 118 na kundin Finalkod.

Ya ƙara da cewa ogan su, wato AIG Umar Mohammed Sanda, ya gargaɗi ‘yan sandan shiyyar da su ci gaba da yaƙar cin hanci da rashawa, wanda shi ne zai sanya a yi wa wanda aka zalunta adalci kamar yadda Sufeto-Janar na ‘Yan Sandan Nijeriya, IGP Kayode Adeolu Abegketun, ya bayar da umarni.

Ya ce za su ci gaba da gudanar da bincike kan kuɗin da ake zargin sun yi ɓatan dabo a tsakanin Amal da Ramadan don a bai wa kowa haƙƙin sa.

Loading

Tags: 'yan sandaAmal Umarkotuzargi
Previous Post

Dalilin mu na kafa Ƙungiyar Masu Fassara a Kannywood – Jammaje

Next Post

Mahaifin marubuciya Zuwairiyyah Adamu Girei ya rasu

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Mahaifin marubuciya Zuwairiyyah Adamu Girei ya rasu

Mahaifin marubuciya Zuwairiyyah Adamu Girei ya rasu

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!