• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 30, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Yanzu ba ruwan mu da Hukumar Tace Finafinai, inji masu gidajen kallo na Kano

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
January 3, 2022
in Labarai
0
Sharu Rabi'u Ahlan, shugaban ƙungiyar masu gidajen kallo ta Jihar Kano

Sharu Rabi'u Ahlan, shugaban ƙungiyar masu gidajen kallo ta Jihar Kano

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƘUNGIYAR masu gidajen kallo a Jihar Kano ta bayyana cewa a yanzu ba ta ƙarƙashin kulawar Hukumar Tace Finafinan ta jihar, don haka kada wani ɗan ƙungiya ya biya kuɗaɗen da hukumar ke cewa su bayar.

Hakan ya fito ne a wani taro da ƙungiyar ta shirya wa ‘ya’yan ta a yau Litinin a gidan kallo na Lahai da ke Titin Abdullahi Bayero a garin Kano.

Shugaban ƙungiyar, Sharu Rabi’u Ahlan, ya ce sabuwar dokar Hukumar Buɗe Ido Da Yawon Shaƙatawa ta Jihar Kano ta ambaci gidajen kallon ƙarara, wato ‘viewing centres’, a cikin kulawar ta, wanda hakan ya nuna cewa gidajen kallon sun bar kulawar Hukumar Tace Finafinai.

Sharu ya ƙara da cewa daga yanzu duk masu gidajen kallo za su maida lamarin su ne zuwa waccan hukuma, kuma hakan wata dama ce da za ta ƙara inganta al’amura da samun daidaito a sana’ar su.

Dandazon mahalarta taron ƙungiyar masu gidajen kallo ta Jihar Kano da aka yi a Lahai a yau

Da ya ke ƙarin bayani dangane da wani saƙo da Hukumar Tace Finafinai ke aika wa masu gidajen kallo ina ta  umarce su da su biya wasu kuɗaɗe, Sharu Rabi’u ya ce wa ‘yan ƙungiyar su dakata kada su biya har sai abin da ƙungiya ta umarce su.

Haka zalika, ya yaba da irin goyon bayan da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ke ba ƙungiyar tasu.

Ya ce ya zama wajibi ƙungiyar ta yaba wa gwamnati tare jaddada bin dokokin gwamnati, musamman wannan sabuwar doka da ta ɗauke su daga ƙarƙashin Hukumar Tace Finafinai.

Taron ya samu halartar masu gidajen kallo da dama daga sassa daban-daban na jihar.

Loading

Tags: Dakta Abdullahi Umar Gandujegidajen kalloKano State Censorship BoardSharu Rabi'u Ahlanviewing centres
Previous Post

Marubuci, ɗan siyasa kuma ɗan kasuwa, Bashir Othman Tofa, ya rasu ya na ɗan shekara 75

Next Post

Alhaji Bashir Tofa: Ba Rabo da gwani ba….

Related Posts

Wani mai suna Bashir Abdullahi ya damfare ni miliyan bakwai da rabi, inji Halisa
Labarai

Wani mai suna Bashir Abdullahi ya damfare ni miliyan bakwai da rabi, inji Halisa

July 28, 2025
Gaskiyar magana kan ji-ta-ji-tar ‘mutuwar’ Aminu Ala
Labarai

Gaskiyar magana kan ji-ta-ji-tar ‘mutuwar’ Aminu Ala

July 28, 2025
KADIFF 2025: Uganda ta fi yawan finafinai a bikin baje-kolin na Kaduna – Israel Kashim Audu
Labarai

KADIFF 2025: Uganda ta fi yawan finafinai a bikin baje-kolin na Kaduna – Israel Kashim Audu

July 25, 2025
Karya dokar liƙi: Kotu ta ɗaure G-Fresh da Hamisu Breaker tsawon wata biyar-biyar
Labarai

Karya dokar liƙi: Kotu ta ɗaure G-Fresh da Hamisu Breaker tsawon wata biyar-biyar

July 24, 2025
‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar
Labarai

‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar

July 23, 2025
Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Next Post
Marigayi Alhaji Bashir Othman Tofa

Alhaji Bashir Tofa: Ba Rabo da gwani ba....

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!