ƘWARARREN mai kwalliya a Kannywood, Auwal Muhammad Ɗanja, wanda aka fi sani da Ambasada Auwal Ɗanja, ba baƙo ba ne a masana’atar. Ya daɗe ana damawa da shi, musamman a kamfanin ubangidan sa, Adam A. Zango.
Ganin an daina jin ɗuriyar sa a ‘yan watannin nan, wakilin mujallar Fim ya nemi jin ta bakin sa a game da hanlin da ya ke ciki. Auwal ya amsa tambayoyin da aka yi masa kamar haka:
FIM: Da farko, ina ka shige aka ka daina jin ɗuriyar ka a Kannywood?
AUWAL ƊANJA: Ina nan, babu inda na je, sai dai nuƙusani na ɗan samu sakamakon wasu ayyuka da su ka ɓoye ni. Da ma ba wai harkar fim kaɗai na ke yi ba. Amma dai ko ma dai yaya ne ba ka cin zamanin ka ka ci na wani.
FIM: Ina ka sa gaba a yanzu a game da harkar Kannywood?
AUWAL ƊANJA: Mu na teburin mai shayi ni da ita; ta na kallo na, ina kallon ta. Kuma ba gudu, ba ja da baya kasantuwar ita ce ni, ni ne ita. In dai akwai lokacin da zan iya badawa a ko da yaushe a cikin sabgogi na, to ita ma akwai nata lokacin da na ware mata nata na kan ta.

FIM: Ganin yanzu harkar finafinai ta ja baya, ba kamar yadda ake yi ba a baya, har yanzu ka na samun aikin kwalliya kuwa?
AUWAL ƊANJA: A’a, yaushe rabon Auwal Ɗanja da kwalliya?! Ai an kwana biyu. Ba kuma hakan ya na nufin ba na yin kwalliya ba ne, a’a, sai dai kwalliya ta musamman ko kuma kamar sauran ƙasashe in sun shigo nan gida Nijeriya, misali kamar BBC, DW, Unicef, Muryar Amurka, da sauran su.
FIM: Ka goya raya a masana’antar nan. Ya alaƙar ka ta ke da su a yanzu?
AUWAL ƊANJA: Hmmm, kai dai bari kawai! Na goya yara kai-tsaye ba zan iya ce maka mutane nawa ba ne, amma akwai wanda yanzu ko lambar waya ta ma ba su da ita bare ma mu gaisa da su. Amma in sun gan ni a hanya kamar su goya ni, da zarar mun bar wurin to fa shi kenan sauran abin da zai biyo baya kuma hmmm.
FIM: Har yanzu ka na da yaran da ka ke koya wa aikin kwalliya?
AUWAL ƊANJA: A’a, ba ni da yaro ko ɗaya in dai a masana’antar fim ne. Amma akwai waɗanda na ke koya ma wa a ƙarƙashin kamfani na, amma duk mata ne.
FIM: Ya alaƙar ka ta ke da ubangidan ka, Adam A. Zango, a yanzu?
AUWAL ƊANJA: Babu abin da ya canza, sai dai abin da ya ƙaru.
FIM: Menene tunanin ka game da Kannywood a nan gaba?
AUWAL ƊANJA: Allah shi ne masani.
FIM: Ka na da kamfani ne na

FIM: Ka na da kamfani ne na koyar da kwalliya?
AUWAL ƊANJA: Ƙwarai, ina da shi: A.A. Ɗanja Production.
FIM: Ka na shirya fim?
AUWAL ƊANJA: Ina shiryawa. Yanzu haka ina da labarai masu dogon zango har guda biyu. Shirye-shirye ya yi nisa, nan da bayan zaɓe zan fita aikin su, in-sha Allahu. Abin da ya tsayar da ni ina da maigida da ya ke takarar Majalisar Tarayya a Rano, Kibiya, da Bunkure, Dakta Aliyu Musa Aliyu Kibiya (Zannan Rano). Wannan dalilin ne ya sa na tsagaita tukuna, da yanzu na yi nisa da fara ɗaukar shirin.
FIM: Menene tunanin ka game da finafinai da ake yi yanzu masu dogon zango?
AUAWAL ƊANJA: To gaskiya su na buƙatar ingantawa fiye da yadda ake yin su a yanzu. Don kuwa in ka ce yanzu da wane fim da wane fim ne masu matuƙar muhimmanci, ba su da yawa. Kowa burin sa a ce dai ya na yi ba tsayawa. Za mu ga wace irin gudunmawa za mu ba da kafin mu yi, sai dai amma abin sai addu’a.
FIM: Me za ka ce game da harkar YouTube? Ka na ganin ita ce hanya mai ɓullewa ga ‘yan Kannywood?
AUWAL ƊANJA: To a yanzu dai ita ce, kafin Allah ya kawo mana wata mafitar, kuma in ma da wata hanyar da tafi ta, to Auwal Ɗanja wallahi bai san ta ba.
FIM: Waɗanne irin nasarori ka samu a Kannywood?
AUWAL ƊANJA: Ba su misaltuwa, tun daga neman aure na, wurin zama na, wurin ayyuka na na yau da kullum, kasuwanci na, wallahi ba su misaltuwa, sai dai fatan gamawa da duniya lafiya, amma wallahi ni Ambsada Auwal Muhammad Ɗanja harkar fim ta yi min komai. Duk wani babban mutum a ƙasar nan da na sani – ko mai sarauta ko mai kayan sarki ko masu muƙami na siyasa – a harkar fim na same su.
FIM: Mecece shawarar ka ga abokan sana’ar ka?
AUWAL ƊANJA: Mu riƙe gaskiya da amana da soyayyar Manzon Allah (s.a.w.) ga duk wasu mutane da su ke mu’amala da su, shi ne shawara ta.

FIM: Menene saƙon ka ga masoyan ka?
AUWAL ƊANJA: Wallahi baki na ba zai iya yi masu godiya ba, don kuwa komai zan faɗa masu gani na ke ya yi kaɗan. Amma dai duk da haka ina godiya mara iyaka a gare su, da fatan Allah ya sa mu gama da duniya lafiya, Allah ya ƙara mana son Manzon Allah (s a w.). Don Allah masoya na a matsayi na na ɗan’adam mai cike da kurakurai in sun ga na yi ba daidai ba su kira ni su faɗa min ta layi na, 08026277779. Ba na kulle waya, ba na ƙin ɗaukar waya, sai in ina wani aiki.
FIM: Mahaifin ka ya rasu watan da ya gabata. Me za ka ce game da rashin sa?
AUWAL ƊANJA: Mahaifi na Muhammad Shafi’u, ya rasu ranar Juma’a, 16 ga Disamba, 2022, da misalin ƙarfe 9:30, a General Hospital, Funtua, ya na da shekara 85 a duniya. Ya bar mata biyu, ‘ya’ya 17 – maza 7, mata 9. Ni ne babban ɗan sa namiji. Jikokin sa 50. Allah ya jiƙan shi da rahama.
FIM: Amin ya Allah.