KWAMITIN zaɓen Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta a Nijeriya (MOPPAN) ta ƙasa a yau ya fitar da jerin sunayen ‘yan takarar da za su yi a babban zaɓen ƙungiyar bayan sun sayi fom.
Jerin sunayen ya nuna cewa mutanen Zariya guda biyu, wato Umar Maikuɗi (Cashman) da Adamu Muhammad Bello (Ability) su ne za su gwabza a wajen neman kujerar shugaban ƙungiyar.
Takardar sanarwa mai ɗauke da sa hannun sa, Sakataren kwamitin zaɓen, Malam Ibrahim L. Ibrahim, tana da kanu kamar haka: “Jerin sunayen ‘yan takarar da suka yi nasarar samu tare da cike fom ɗin su na ofisoshi daban-daban a zaɓen ƙasa na ƙungiyar MOPPAN da ke tafe.”
Ibrahim ya ce: “Ya kamata duk masu neman tsayawa takara su binciko sunayen su tare da tabbatar da cewa ba a cire sunayen su ba ko kuma a yi masu kuskure.
“Za a fara atisayen tantancewa ne nan gaba kaɗan da kwamitin zaɓen za ta sanar.”
Sakataren kwamitin ya shawarci dukkan ‘yan takara su bi ƙa’idojin tsarin zaɓe kamar yadda kwamitin zaɓen ya zayyana.
“Muna yi masu fatar samun nasara da cimma burin su da kuma ƙarfafa yin adalci da gaskiya,” inji shi.
‘Yan takarar da muƙaman da suke nema su ne:
SHUGABA
- Umar Maikudi (Cashman)
- Adamu Bello (Ability)
MATAIMAKIN SHUGABA – AREWA TA TSAKIYA
- Dakta Kamal Adamu
- Bala Kufaina
- Umaru Ravi
MATAIMAKIN SHUGABA – AREWA MASO YAMMA
- Shehu Hasan Kano
- Sanusi G. Kalambaina
MATAIMAKIN SHUGABA – AREWA MASO GABAS
- Haruna Mohammed Godowoli
- Ibrahim Amarawa
- Murtala Baba Muri
SAKATARE
- Mohammed Ibrahim Gumel
MATAIMAKIN SAKATARE
- Kwamared Lawal Rabe
- Al-Amin Ciroma
- Nasir Umar Gwandu
MA’AJI
- Hajiya Fatima Lamaj
- Falalu Ɗorayi
- Kwamared Adamu Musa Okonkwo
SAKATAREN KUƊI
- Lawan Ahmed
- Arch. A.M. Kasarawa
MAI BINCIKEN KUƊI
- Haruna Talle Maifata
MAI BINCIKEN KUƊI NA BIYU
- Hayatudden Yakubu
JAMI’IN HULƊA DA JAMA’A
- Habibu Mu’azu
JAMI’IN HULƊA DA JAMA’A NA BIYU
- Murtala A. Hassan
WALWALA
- Wasila Isma’il
SAKATAREN TSARE-TSARE
- Haladu Muhammad
Sai dai jim kaɗan bayan fitar da sunayen, sai Al-Amin Ciroma ya wallafa sanarwar ficewar sa daga takarar.
Ciroma, wanda shi ne Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na MOPPAN a yanzu, ya rubuta takardar ne da Turanci, wadda mujallar Fim ta fassara kamar haka:
“JANYEWA DAGA ZAƁEN MOPPAN NA 2025
“Zuwa ga Kwamitin Zaɓen MOPPAN,
“Ina miƙa kyakkyawar gaisuwa a gare ku tare da ɗimbin godiya kan ɗimbin goyon baya da ba da ƙwarin gwiwa da kuka ba ni a dukkan tsawon lokacin da na yi muradin yin takarar muƙamin Mataimakin Sakatare na Ƙasa a zaɓuɓɓukan MOPPAN na 2025 da ke tafe.
“Bayan kyakkyawar lura tare da zurfin tunani kan abubuwan da ke gaba na kankin kai na da kuma aiki na, na yanke shawarar in janye takara ta a wannan zaɓe.
“Sai da na yi tunani mai yawa kafin in yanke wannan shawara, domin kuwa sha’awar da nake da ita ta ganin bunƙasa da cigaban MOPPAN yana nan bai ragu ba ko kaɗan.

“Duk da haka, na yi amanna da cewa wannan matakin da na ɗauka ya yi daidai da ayyukan da ke gaba na a yanzu da kuma abubuwan da nake so in cimmawa a nan gaba.
“Ina nan cikin sadaukarwar da nake da ita ga muradi da burukan MOPPAN kuma zan ci gaba da ba da gudunmawa ta ga ayyuka da tsare-tsaren da za su haɓaka cigaban ƙungiyar da ma industirin baki ɗaya.
“Ina da matuƙar tabbacin cewa zaɓen zai samar da ƙwararrun shugabanni masu sadaukarwa, waɗanda za su harba MOPPAN zuwa ƙarin matakan cigaba.
“Su kuma sauran ‘yan takarar da muka shiga wannan tsere da su, ina miƙa fatan alheri a yi zaɓe cikin nasara wanda zai kawo alfanu. Na tabbatar kowannen ku yana da ƙwari da zurfin hangen nesa da zai kawo wanda zai amfani ƙungiyar.
“Ina ƙara gode maku saboda fahimtar ku, amincin ku, da goyon bayan ku. Masha Allah. Ina sa ran haɗa gwiwa da shugabanni da membobin MOPPAN a nan gaba kaɗan.
“Allah Hokku en jam, ameeena.
“Naku har abada.”
![]()







