A LAFIYA, babban birnin Jihar Nasarawa, za a gudanar da babban zaɓen haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya finafinai ta Nijeriya (Motion Picture Practitioners Association of Nigeria, MOPPAN).
A wata sanarwa da ya bayar a madadin ‘yan kwamitin zaɓen a yau, Sakataren Hukumar Zaɓen MOPPAN, Dakta A.S. Bello, ya bayyana cewa kwamitin da aka ɗora wa alhakin shirya zaɓen ne ya kuma yanke shawarar cewa za a yi zaɓen a ranar 19 ga wannan watan na Oktoba 2021.
Dakta Bello ya ce kwamitin nasu ya kammala dukkan shirye-shiryen yin zaɓen, don haka ya yi kira ga dukkan masu niyyar son tsayawa takara da su hanzarta zuwa sayen fom ɗin su kafin ranar 15 ga wata, wadda ita ce ranar da za a rufe sayar da fom ɗin.
Sakataren ya ƙara jaddada bayanin da yi kwanan baya cewa duk mai son sayen fom ɗin zai zuba kuɗin fom ɗin sa ne a asusun banki na ma’ajin kwamitin zaɓen, kamar haka:
Mohammed Ibrahim Gumel,
Access Bank,
0040001335.
Haka kuma ya ce, “Kwamitin ya na ƙara kira ga jihohin waɗanda ba su yi zaɓen su a matakin jiha ba da su hanzarta yin zaɓe kafin ranar zaɓe na ƙasa kamar yadda kundin tsarin mulkin MOPPAN ya tanada.”
Idan kun tuna, kwanan nan mujallar Fim ta ba ku labarin cewa MOPPAN ta fito da ƙa’idojin tsayawa takara a ƙungiyar sannan ta faɗi kuɗin fom na kowane muƙami da mutum ya ke so ya nema.
Farashin fom-fom na tsayawa takara dai shi ne kamar haka:
i. Shugaba – N50,000
ii. Mataimakin Shugaba na 1 zuwa na 3 – N40,000
iii. Sakatare – N40,000
iv. Ma’aji – N30,000
v. Sakataren Kuɗi – N30,000
vi. Mataimakin Sakatare – N30,000
vii. Kakaki – N30,000
viii. Mai Binciken Kuɗi N30,000
ix. Mataimakin Sakatare – N30,000
x. Mai Kula da Walwala (mace kawai) – N30,000
Shugaban kwamitin shirya zaɓen shi ne fitaccen daraktan nan Ahmad S. Alkanawy.