• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, June 4, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Za mu yi wa ‘yan fim na Jihar Kaduna jagoranci tsakani da Allah – Uwaisu Abubakar

by DAGA ABBA MUHAMMAD
March 28, 2022
in Labarai
0
Sabon shugaba, Alhaji Uwaisu Abubakar

Sabon shugaba, Alhaji Uwaisu Abubakar

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SABON shugaban Ƙungiyar Furodusoshi ta Jihar Kaduna (Kaduna Guild of Producers), Alhaji Uwaisu Abubakar, ya sha alwashin cewa shi da abokan aikin sa za su yi aiki domin Allah, su yi tafiya tare da kowa da zuciya ɗaya, kuma za su yi wa kowa adalci a kan abin da ya shafe shi a kan ƙungiyar don daƙile dukkan wani ƙalubale da ka iya tasowa.

Haka kuma ya gode wa Allah da aka samu nasarar rantsar da su a matsayin sababbin shugabannin ƙungiyar.

Uwaisu ya bayyana haka ne a cikin tattaunawar da ya yi da mujallar Fim jim kaɗan bayan an rantsar da shugabannin ƙungiyar a jiya Lahadi, 27 ga Maris, 2022 a Kaduna.

An zaɓi shugabannin ne bayan da kwamitin  zaɓe da haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) da kuma jama’ar da aka yi zaman majalisi (congress) da su a ranar da aka yi zaɓen MOPPAN ɗin su ka amince da umartar dukkan shugabannin riƙo na ƙungiyoyin da ke ƙarƙashin  MOPPAN da su shirya wa kan su zaɓe bayan zaɓen da wata ɗaya.

A ranar Asabar, 25 ga Disamba, 2021 aka yi zaɓen ƙungiyar furodusoshi, wanda ya gudana a gidan Hajiya Fatima Ahmad Ibrahim Lamaj (Lamaj) da ke unguwar Rigachikun, Kaduna, wanda Malam Murtala Aniya ya jagoranta.

Ana rantsar da sababbin shugabannin

Sai dai kuma bayan zaɓen an samu wasu daga cikin ‘yan ƙungiyar da ‘yan MOPPAN da su ka ƙi amincewa da wannan zaɓe, sai da aka sake saka rana, sannan aka yi zama na musamman aka samu haɗin kai da fahimtar juna sannan sauran jama’a su ka amince da zaɓen da sabbabin shugabannin.

Tun bayan zaɓen da kusan wata uku kenan, sai jiya aka rantsar da sababbin shugabannin ƙungiyar. Ba dai wani gagarumin taro aka yi ba.

An fara taron rantsarwar da misalin ƙarfe 2:30 na rana, bayan shugabannin taron samu isowa ɗakin taro.

Bayan an buɗe taro da addu’a, mai gabatarwa Yahuza Ilu ya umarci mataimakin shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya finafinai reshen Jihar Kaduna, wato Sulaiman Sha’ani, da ya sanar da mahalarta taron maƙasudin taron. 

Sha’ani ya ce, “Yau Lahadi, 27 ga Maris, 2022 ƙungiyar MOPPAN za ta rantsar da sababbin shugabannin Ƙungiyar Furodusoshi ta Jihar Kaduna.”

Saboda ƙarancin lokaci, nan take aka buƙaci Barista Rabi’u Muhammad da ya rantsar da shugabannin.

Bayan an rantsar da su, an roƙi alfarmar mutum uku da su tashi ɗaya bayan ɗaya su yi jawabi a taƙaice. 

Tsohon shugaban MOPPAN na ƙasa, Alhaji Abdullahi Maikano Usman, shi ne mutum na farko da ya yi jawabi a taƙaice, ya ce, “Duk abin da za ka yi a duniya Allah zai tambaye ka ranar tashin alƙiyama. Haka kuma babu wani abu da za a ce babu ɓangaren addini a cikin sa. 

“Saboda haka ku san da sanin cewa maganar ku, rayuwar ku, ayyukan ku, za ku tashi ranar alƙiyama a ɗaure, ayyukan ku su za su kwance ku, gaskiyar da ku ka yi ita za ta fitar da ku. Ko kuma a ce ka na da aboki don kun saɓa ra’ayi shi kenan ka watsar da shi, wannan ba Musulunci ba ne. Gaskiya ita ce gaskiya, kuma a kullum gaskiya ta na matsayin gaskiya ne. Saboda haka babu gaba, ‘yan’uwa mu ke, kuma mu zama tsintsiya maɗaurin mu ɗaya. Don Allah kada a ce wani ya zama shafaffe da mai, ku riƙe mu, mu membobin ku ne. 

“Ina roƙon Allah ya jiƙan magabatan mu, ya saka masu da gidan Aljanna, in kuma tamu ta zo ya sa mu cika da imani.”

Haka shi ma shugaban MOPPAN reshen Jihar Kaduna, Alhaji Hamisu Jibril Goma, ya taya sababbin shugabannin murnar samun nasara, sannan kuma ya ba su shawara a kan alƙawarin da su ka ɗauka. 

Goma ya yi masu addu’ar Allah ya ba su ikon sauke nauyin da ke kan su. Haka kuma ya yi masu jan hankali game da shugabanci da kuma yadda za su samu nasara a game da shugabancin da su a kai. 

A ƙarshe, ya ba su shawarar kada su yarda su aje iyayen ƙungiya; duk abin da ya shige masu duhu, su nemi iyayen ƙungiyar don neman mafita.

Kakakin MOPPAN na ƙasa kuma fitaccen darakta, Malam Al-Amin Ciroma, shi ma ya tofa albarkacin bakin sa inda ya ja hankalin sababbin shugabannin, musamman shi shugaban, a kan neman haɗin kan membobin sa. 

Haka kuma ya yi magana a kan rashin ganin wasu a wurin taron, wanda har da wasu daga cikin zaɓaɓɓun shugabannin, wanda ya ke ganin akwai wani abu a ƙasa. Don haka ya nemi alfarmar sabon shugaban da ya bi su har gida don ganin an samu maslaha, domin ciyar da ƙungiya da harkar fim gaba.

An buƙaci ɗaya daga cikin mata biyu kacal da su ka halarci taron,  A’isha Usman, da ta ce wani abu, sannan ta rufe taro da addu’a. 

Daga hagu: Muhammad Goce, Ibrahim Shebe da Abubakar Hunter a wurin taron

A’isha, wadda ita ce sabuwar sakatariyar kuɗi ta ƙungiyar, ta yi addu’ar samun nasara a kan shugabancin da ya hau kan su, sannan kuma ta yi addu’ar rufe taron.

An tashi daga taron da misalin ƙarfe 3:30 na rana.

Bayan an tashi taro, mujallar Fim ta tuntuɓi sabon shugaba, Uwaisu Abubakar,  game da sabon nauyin da ya hau kan sa. 

Sai ya ce, “Farko mu na yi wa Allah godiya da ya ba mu ikon ganin wannan rana da aka rantsar da mu a matsayin shugabannin Ƙungiyar Furodusoshi ta Jihar Kaduna. Babu shakka, wannan rana ce mai matuƙar tarihi da ya kamata mu gode wa Allah a kan ganin ta. Don haka babu abin da za mu ce sai godiya ga Allah a kan wannan rana.”

Ganin cewa ƙungiyar na da ƙalubale, ko akwai wani tsari su ka yi don ganin an daƙile matsalolin? Uwaisu ya amsa, “Ai kowane shugabanci akwai ƙalubale a kan shi, sai dai wani shugabanci ya zama ya fi wani ƙalubale. 

“Babban abin da za mu ɗauka wurin maganin ƙalubale shi ne mu yi aiki domin Allah, mu kuma riƙe ƙungiyar saboda Allah, mu tafi da kowa, mu yi wa kowa adalci a kan abin da ya same shi game da wannan ƙungiya. Kuma mu raya ƙungiyar a Jihar Kaduna, ya zama ƙungiyar ta na amfanar mutanen Jihar Kaduna, ba wai kawai ta zama shiru kamar yadda ake cewa ta yi shiru ɗin ba. Wannan shi ne fatan mu.”

A game da furodusoshi da ba su da rijista, Fim ta tambaye shi ko akwai wani tsari da shugabannin za su yi don ganin kowane kamfani zai yi rijista. Sai ya amsa da cewa, “Akwai abubuwa da dama da Jihar Kaduna ta ke buƙata, ba kawai rijista ba ne. Ita Jihar Kaduna kamar gida ne da ke a buɗe a yanzu, dole sai an bi hanyoyi da za a yi masa ƙyaure, don ya zama ana rufe shi saboda ɓatagari da za su iya shigowa ciki. 

“Mu na ganin ya zame mana wajibi, ƙalubalen mu na farko da za mu daƙile shi ne a sabunta rajistar furodusoshi, domin mu san adadin yawan furodusoshin mu a Jihar Kaduna. A wannan ɓangaren kenan. 

“A wani ɓangare kuma ƙungiyar ita kan ta za ta samu kuɗin shiga da za ta  iya amfanar da al’ummar Jihar Kaduna da su. Don haka abin da za mu tunkara, ita kan ta Jihar Kadunar ba wannan ƙungiyar ba kaɗai ta samu ɗinkewa a inda ake ganin akwai ɓaraka a cikin ta.”

A ƙarshe, mun tambaye shi abin da zai ce ga membobin sa da sauran mabiya. Sai ya ce, “Abin da zan ce, mu sani dai wannan amana ce Allah ya ba mu, kuma babu shakka shugabanci dole ne sai Allah ya tambaye ka a kan  yadda ka gudanar da shugabanci. 

“Mu yi wannan shugabancin tsakani da Allah, mu aje tunanin wane ba ya yi na ko wane ya na yi na ko wane na da matsala. Idan mu ka tafi da kowa, mu kalli nauyin da ke kan mu ba mu tsaya kallon abin da ya ke na rigingimu a cikin ƙungiya, wanda kowace ƙungiya ta gaji irin waɗannan rigingimun, kuma in an tsaya kallon su a ƙarshe sai a kasa sauke nauyin da Allah ya ɗora mana. 

Daga hagu: Abdullahi Maikano Usman, Hamisu Jibril Goma da Sulaiman Sha’ani a wurin taron

“Ni abin da zan ja hankalin membobi na, mu aje duk wani abu da ke tsakanin mu da wasu, mu tunkari aikin ƙungiya kuma mu yi wannan aiki saboda Allah.” 

Ga jerin muƙaman:

Ciyaman – Uwaisu Abubakar (Zariya)

Mataimakin Ciyaman – Garba Shehu PS (Kaduna)

Sakatare-Janar – Falalu I.M. Sani (Kafanchan)

Mataimakin Sakatare Janar – Ibrahim Abubakar

Ma’aji – Yusuf M. Gidaje (Kaduna)

PRO – Khalid Gamagira – (Kaduna)

Sakataren Kuɗi – Aisha Usman – (Kaduna)

Sakataren Tsare-tsare – Ibrahim Captain (Kaduna)

Odita – Aminu Mirror (Zariya)

Welfare – Abubakar Ɗanmasani

Ex-officio:
1. Ibrahim Tahir – (Zaria)
2. Adamu Ibrahim (Kaduna)
3. Musa Shehu (Kafanchan)
4. Tukur Alwadawi

Shugabannin kafin a rantsar da su
Hoton sada zumunci bayan taro

Loading

Tags: Abdullahi Maikano UsmanAisha UsmanAl-Amin CiromaFatima Lamajfilm producersHamisu Jibril GomaJihar KadunakungiyaMOPPANMurtala AniyarantsarwashugabanniUwaisu AbubakarYahuza Ilu
Previous Post

Yadda jarumin Amurka Will Smith ya tsinke jarumi Chris Rock da mari a bikin karramawar finafinai ta Oscars

Next Post

Tsohuwar jarumar Kannywood Naja’atu Muhammad da ɗan ƙwallo Abdullahi Shehu sun samu ƙaruwa

Related Posts

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim
Labarai

MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim

June 2, 2025
Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22
Labarai

Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22

May 20, 2025
Hukuma ta rufe gidajen gala a Kano har sai bayan Ramadan
Labarai

Gwamnatin Kano ta dakatar da haska finafinan Kannywood 22 a intanet da talbijin 

May 19, 2025
Labarai

Gwamnan Kano ya ɗauki nauyin ‘yan Kannywood 5 zuwa Hajjin bana

April 17, 2025
Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu
Labarai

Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu

March 28, 2025
Next Post
Abdullahi Shehu da matar sa, tsohuwar jaruma Naja'atu Muhammad, tare da ɗan su, Abdulhameed

Tsohuwar jarumar Kannywood Naja'atu Muhammad da ɗan ƙwallo Abdullahi Shehu sun samu ƙaruwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!