FITACCEN jarumin masana’antar finafinai ta Amurka, Will Smith, a daren jiya ya kwashe fitaccen jarumin barkwanci Chris Rock da mari a wajen bikin bada kyaututtaka na finafinai mafi girma a duniya, wato Oscars, saboda ya taɓo masa mata a cikin wasu kalaman barkwanci da ya furta.
Rock, wanda shi ne mai gabatarwa a gagarumin bikin da aka yi a birnin Los Anjalis, ya furta cewa, “Jada, na ƙosa in kalli fim ɗin ‘GI Jane’ kashi na 2,” kuma ya faɗi haka ne saboda yadda Jada Pinkett Smith ta zo taron da ƙwaryar molo, wanda ya yi kama da shigar da jarumar fim ɗin ‘GI Jane’, wato Demi Moore, ta yi a fim ɗin wanda aka saki a cikin 1997.
Jada, wadda ita ma fitacciyar jaruma ce, ta na fama da cutar ‘alopecia’, mai sa zubewar suma.
Kalamin ya ɓata wa Smith rai, wanda hakan ya sa ya hau dandamalin bikin, ya taka tinkis-tinkis har zuwa inda Rock ya ke tsaye, ya wanke shi da mari ba zato ba tsammani. Daga nan ya koma kujerar sa ya na faɗin, “Kada bakin ka mai… (sai ya haɗa da ashariya a nan) ya ƙara ambaton mata ta.”
Daga bisani, Smith ɗin ne ya lashe matsayin Jarumin Jarumai a gasar ta Oscars ta bana.
Lokacin da ya ke gabatar da jawabin karɓar karramawar, Smith ya bada haƙuri ga Majalisar Masu Shirya Finafinai ta Amurka (Academy of Motion Picture Arts and Sciences) saboda abin da ya aikata.
Haka kuma cikin hawaye ya bada haƙuri ga dukkan abokan karawar sa a gasar. To amma bai bada haƙuri ga Chris Rock ba.
Smith ya lashe gasar a matsayin Jarumin Jarumai ne saboda rol ɗin da ya taka a fim ɗin ‘King Richard’ inda ya fito a matsayin mahaifin shahararrun ‘yan wasan ƙwallon tennis ɗin nan Venus da Serena Williams.
A jawabin sa na karɓar karramawar, ya yi bayanin cewa, “Aikin hikima ya na kyaikwayon rayuwar gaske. Na yi kama da mahaukacin uba, kamar dai yadda su ke faɗi game da Richard Williams. Amma soyayya na iya sanyawa ka yi abubuwan hauka.”

Ya ƙara da cewa Richard Williams mutum ne “mai tsananin kare iyalin sa” sannan kuma shi kan shi “Allah ya ɗora masa” wani nauyi a rayuwar sa na “son jama’a tare da kare jama’a.”
Ya yi ta magana cikin shauƙi har ya na zubar da hawaye, har sai da manyan jarumai biyu, Denzel Washington da Tyler Perry, su ka janye shi daga dandamalin tare da ba shi magana.
Majalisar Masu Shirya Finafinai ta Amurka, wadda ita ce ke shirya gasar Oscars ɗin, ta wallafa saƙon tuwita inda ta ce ita “ba ta amince wa duk wani irin aikin tashin hankali ba.” Hakan ya sa ake zaton ƙila ta janye karramar da ta yi wa Smith.
Ita kuma hukumar ‘yan sanda ta birnin Los Anjalis, cewa ta yi Rock ya “ƙi ya shigar da ƙara ga ‘yan sanda” a kan al’amarin, amma a shirye ta ke ta gudanar da bincike idan ya kai mata maganar. Wato za ta kama Smith kenan saboda abin da ya kamata.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa sauran waɗanda su ka yi nasara a gasar sun haɗa da Jessica Chastain wadda ta ci muƙamin Jarumar Jarumai Mata da fim ɗin ‘The Eyes of Tammy Faye’; sai Jane Campion wadda aka ba Daraktar Daraktoci, da fim ɗin ‘The Power of the Dog’; sai wani fim da kamfanin Apple TV ya ɗauki nauyin sa, mai suna ‘Coda’, wanda aka ba Gwarzon Fim.
Ariana DeBose ce ta lashe gasar Matallafiyar Jarumar Jarumai saboda fim ɗin ‘West Side Story’, yayin da Troy Kotsur ya lashe Matallafin Jarumin Jarumai saboda rol ɗin sa a fim ɗin ‘Coda’, wanda kuma shi ne shirin da ya lashe labarin fim na aro (adapted screenplay) da ya zarce saura.
Shirin ƙirƙirar kimiyya mai suna ‘Dune’ ya ci jimillar matsayi shida, ciki har da sassan ƙwarewa da su ka haɗa da ingancin sarrafa hoto (visual effects) da tsara fim (cinematography).
Mujallar Fim ta ce kusan duk abubuwan burgewar da aka yi a bikin an manta da su, an tsaya ana cece-ku-ce a faɗin duniya kan marin da Will Smith ya yi wa Chris Rock, inda wasu ke cewa Smith bai kyauta ba mari, amma wasu na cewa marin ya yi daidai domin Rock ya jima ya na shigar wa Jada hanci da ƙudundune, don haka gara da mijin ta ya fidda raini a tsakanin su, ya yi maganin sa.