TUN daga lokacin da ake ta rubibi na rubuce-rubuce a kan zancen wanki da mace za ta yi wa miji nakl ke tunani tare da neman gano shin me ya kawo wannan ne? Irin mu da Allah ya yi wa rufin asiri na kasancewa da mata biyu fiye da shekaru 20 zuwa yau, sai mutum ya kalli meye zancen wanki a cikin hulɗa ta aure?
Na fi ganin wannan ga talauci, ƙuruciya da rashin tunani a kan masu yaɗa wannan don kuwa ƙima, ɗaukaka da daraja ta auratayya sun fi ƙarfin zancen yi wa miji wanki.
Wani lokaci sai na yi rubutu in goge, musamman dangane da matan da ke ganin kan su ‘indepedent’ daga ikon mazaje saboda tsabar wayewa ko rayuwa ta zamani. Hakan ya sanya na ɗan saurara, sai yanzu ma ake gaya mani wasu da ke ta yaɗa wannan shaiɗanci. Tun haihuwa har lokacin girman su iyaye mazaje ke ɗauke da nauyin su, tun daga abinci, sutura, motar hawa har gidan da su ke barci; sakamakon mazajen aure sun yi ƙamfa saboda ganin halayyar su da ganin irin rayuwar da su ke ciki ta wayewa.
Sai dai na tabbata akwai irin Malala a cikin su waɗanda idan su ka yi wuf da namiji tabbata ba su sake surutu.
Fahimtar su a kan namiji ta game kowa, saboda sun samu matsala da namiji ɗaya ko biyu a aure ko hulɗa, dalilin su kenan a kan ɗaukar namiji ba ɗan goyo ba, ko kuma amincewa da kalmar ‘Duk wadda ta ɗauki namiji uba, tabbata za ta kwana marainiya’ ko da yake sun fitar da nasu iyaye daga cikin lissafi saboda son kai da dabbanci na daƙiƙancin tunani irin na son kai.
Duk da wannan, akwai wasu mata da ƙaddara ce ta rayuwa ba fankama ko jahilci ya sanya su ke ƙin namiji ba, wasu ma saboda wahalar rayuwa da su ka fuskanta a lokacin aure ko hulɗar su; musamman bayan sun fitar kutsu ta rayuwa. Sai dai hangen Dala, ba shiga Kano ba.
Duk yadda matan bariki, ‘yan zamani da su ke tinƙaho da ilimi, wayewa ko kuɗi za su yi wa mazaje kuɗin goro; tabbata wasu daga cikin su na da zaɓoyyayun mazajen da ke yi masu hidima ko ta hulɗa ko ta aiki ko ma ta biyan buƙatun su.
Wasu matan ma har girki su ke yi su na kai wa wasu mazajen duk da irin cin fuskar da su ke yiwa jinsin su a hanyoyin sadarwa ko gabatar da ƙasidu na tarurruka.
Muhimmiyar shawara gare mu baki ɗaya, mu mutunta tare da girmamma iyakokin juna tare da tsare amana da gaskiya a kan zamantakewa tsakanin ma’aurata da ma hulɗa da juna.
Ba wata mace mai lafiya da kuzari da za ta rayu babu namiji tare da ita, muddin har dai ta samu tarbiyya ta iyaye da kakanni.
Fata ɗaya da ya dace mu yi wa waɗannan matan ita ce Allah ya aza su a kan hanyar haƙuri da fahimtar addini da tarbiyya ta mutunci don kada su shiga wani mummunan yanayi na rayuwa.
* Malam Yusuf Ɗingyadi ɗan jarida ne a Sokoto