• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, June 7, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Zargin ina nuna wariya ko na gaza yin aiki ba gaskiya ba ne – Minista Sadiya

by DAGA ALI KANO
August 16, 2022
in Nijeriya
0
Hajiya Sadiya Umar Farouq ta na raba kayan tallafi ga mata a Dutse, Jihar Jigawa, a makon jiya

Hajiya Sadiya Umar Farouq ta na raba kayan tallafi ga mata a Dutse, Jihar Jigawa, a makon jiya

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAR Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta bayyana cewa ba gaskiya ba ne iƙirarin da wasu ke yi cewa wai ba ta rarraba ayyukan ka a dukkan sassan Nijeriya, sai wani wuri kaɗai, sannan kuma wai ba ta yin aikin ta yadda ya kamata.

Ta ce ita ayyukan ta ta na gudanar da su ne a kowace jiha a ƙasar nan da kuma Gundumar Babban Birnin Tarayya.

Ministar ta yi wannan kalami ne a raddin da ta yi wa wani wai shi Bibi Dogo wanda ya saka talla a jaridar Daily Trust ta ranar Litinin, 9 ga Agusta, 2022 inda ya yi kira ga Shugaba Buhari da ya kore ta saboda wai ba ta yin aikin ta yadda ya kamata.

A sanarwar da mai agaza wa ministar a fagen yaɗa labarai, Nneka Ikem Anibeze ta bayar, ta bayyana cewa a zahiri Dogo, wanda ya ce shi dattijo ne a jam’iyyar PDP a Ƙaramar Hukumar Bauchi, ya yi magana ne a madadin wasu waɗanda ke adawa da ministar, waɗanda za a iya gane su ta hanyar ƙarairayin da su ke yaɗawa. 

Ta ce iƙirarin da ya yi ba gaskiya ba ne ko kaɗan, kawai ya wawuko shaci-faɗi ne a kan ministar da ofishin ta.
 Misali, Dogo ya ce wai ministar ta na amfani da dukiyar gwamnati ta na yin “katsalandan” a siyasar Jihar Bauchi, sannan wai ta na yin haka ne domin mara wa siyasar mijin ta baya a takarar zama gwamnan jihar da ya ke yi a ƙarƙashin tutar jam’iyyar APC.

Minista ta na zantawa da wasu zabaya a taron ƙaddamar da shirin raba kuɗi ga mabuƙata a Kalaba, Jihar Kuros Riba, a makon jiya

Haka kuma ya ce ministar ba ta yi komai ba wajen taimakon matan jihar ta ta Zamfara.
 A cewar Anibeze, manufar wannan mutum wanda bai ma san kakakin jam’iyyar su na yanzu ba, shi da masu ɗaukar nauyin sa, ita ce su yaudari mutane da labaran ƙanzon kurege tare da haifar da tsana da gaba, sannan su ɗauke hankalin ma’aikatar tare da shafa wa aikin ta kashin kaji.

Ta ce in ba domin kada wasu tsiraru su gaskata ƙarairayin sa ba, to da ma’aikatar ba ta ce masa ƙala ba, amma ya zama wajibi a amsa masa don gyara illar da ya ke son kawowa kuma a tabbatar wa da masu ruwa da tsaki da kuma miliyoyin mabuƙata masu amfana da ma’aikatar a faɗin ƙasar nan cewa zargin sa ba gaskiya ba ne. 
Ta ce a Arewa-maso-gabas akwai jimillar masu cin moriyar shirin N-Power su 167,412 kuma a cikin su mutum 31,942 ‘yan Bauchi ne, yayin da ‘yan makarantar firamare da ma’aikatar ke ciyarwa a yankin sun kai 1,603,617 waɗanda yara 444,099 daga Bauchi ne.

Na biyu, wannan dattijon ya yi ƙaryar wai mutanen yankin Kudu-maso-gabas su na zargin ministar da nuna masu wariya, wai ba ta kai aikin tallafi a jihohin su ba. 

Akasin hakan, a cewar mataimakiyar,akwai ‘yan makarantar firamare 778,450 da ake ciyarwa, sannan a ƙarƙashin shirin N-Power akwai mutum 136,629 a yankin. 
Na uku, ya yi iƙirarin wai sama da masu cin moriyar N-Power su 80,000 ba a biya su kuɗin su na watanni biyar ba.

Ta ce wannan ma ƙarya ce domin mutum 14,021 da ba a biya kuɗin wata biyar ba su ne su ka jawo, domin komfutar tsarin biyan alawus na Gwamnatin Tarayya da ake kira ‘Payment system Government Integrated Financial Management Information System’ (GIFMIS) ita ce ta dakatar da biyan su a watan Maris na 2020 saboda dalilai daban-daban.

Dalilan sun haɗa da: mallakar asusun banki sama da ɗaya, da yadda masu cin moriyar shirin su ke amfani da asusun wajen karɓar kuɗaɗe (na albashi ko alawus) daga hukimomi daban-daban na Gwamnatin Tarayya ko kuma su ma’aikatan dindindin ne ko sun shiga wasu shirye-shiryen na gwamnati. 

Ta ba da misali da Jihar Bauchi, inda tsarin GIFMIS ya warware matsalolin mutum 191 masu cin moriyar shirin har an biya su kuma sun fita daga shirin. 
Su kuma ‘yan N-Power na rukunin ‘Batch C’ an kasa su gida biyu ne, wato C1 da C2. A cikin Satumba 2021 aka ɗauki ‘yan C1 kuma za su kammala shirin a wannan watan na Agusta 2022 bayan sun cika wa’adin watanni 12 a cikin shirin.

Ta ce babu wata ƙumbiya-ƙumbiya wajen biyan, kawai mutum ya yi amfani da tsarin da gwamnati ta amince da shi wajen biya, wato NASIMS, inda duk wani mai cin moriyar shirin zai iya ganin dalilin da ya sa aka biya shi ko aka ƙi biyan shi, misali saboda ƙin zama ya yi aiki.

Su kuma ‘yan rukunin C2 da aka zaɓa, sun gama tirenin da tantancewar gani da ido ta hanyar abokan aikin ma’aikatar na hukumar NYSC. An fara tura mutum 490,000 aiki a ranar 1 ga Agusta inda za su fara shiga gurbin masu cin moriyar N-Power mutum miliyan ɗaya da Shugaban Ƙasa ya amince a ɗauka. 

A ƙarshe, ta tabbatar wa da jama’a da abokan hulɗa cewa wannan ma’aikatar ta na nan ba gudu ba ja da baya wajen sauke nauyin da aka ɗora mata. 

Ta ce ta lura da yadda ake ɗaukar nauyin wasu domin su kai wa ma’aikatar da ministar hari a kafafen yaɗa labarai don a ɓata masu suna, amma wannan duk yarfen siyasa ne maras amfani. Saboda haka ba za ta tsorata ba ko a ɗauke mata hankali daga kan turbar da ta ke a kai ta kai wa mabuƙata agajin da su ke buƙata.

Loading

Tags: 'yan makarantar firamareagajiAir Mashal Abubakar SadiqueAPCBauchiBibi DogoGIFMISharkokin jin ƙaiinganta rayuwaN-PowerNneka Ikem AnibezeNYSCPDPSadiya Umar Farouqsiyasa
Previous Post

Yanzu masu kallo sun fara bambance finafinan Hausa da za su kalla – Alhaji Sheshe

Next Post

Siyasar Kannywood: Yadda na kawo Mujeedat ‘yar Bola Tinubu garin Kano – Mansurah Isah

Related Posts

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London
Nijeriya

Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London

May 16, 2025
Next Post
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje tare da Mujeedat Folashade Ojo Tinubu (a hagu) da Mansurah Isah

Siyasar Kannywood: Yadda na kawo Mujeedat 'yar Bola Tinubu garin Kano - Mansurah Isah

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!