BAYAN tsawon lokaci da aka shafe ana tafka shari’a tsakanin tsohon Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Malam Isma’il Na’abba (Afakallah) da jarumin barkwanci Yusuf Baban Chinedu, kotu ta kai ga yanke hukuncin ƙarshe.
A zaman da ta yi na ranar Talata, 5 ga Yuni, 2023 Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke zaman ta a Filin Hoki da ke unguwar Hausawa, Kano, wadda Mai Shari’a Malam Abdullahi Halliru ya ke jagoranta, ta yanke hukunci a kan shari’ar da aka shafe kusan shekaru huɗu ana tafkawa.
An gurfanar da Baban Chinedu ne bisa tuhumar ya ɓata wa Afakallahu suna da ya ce wai ya cinye kayan auren ɗiyar jarumin barkwanci marigayi Rabilu Musa Ɗanlasan (Ibro).
Baban Chinedu ya yi zargin ne a wani faifan bidiyo da ya wallafa a Facebook tare da sauran shafuka, inda ya yi iƙirarin cewa Gwamnan Jihar Kano na lokacin, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bai wa Afakallahu kuɗin sayen kayan ɗakin a lokacin da za a yi wa yarinyar aure.
Ya ce wai Afakallahu ya yi amfani da kuɗin ne ta wata hanyar ba tare da ya saya mata kayan ɗakin ba.
A nasa ɓangaren, Afakallahu ya nemi Baban Chinedu da ya janye kalaman nasa ko kuma su gurfana a gaban kotu, amma shi kuma Baban Chinedun ya ƙi janyewar. A ƙarshe Afakallahu ya garzaya kotu domin neman haƙƙin sa.
Tun a lokacin dai aka yi ta je-ka-ka-dawo a kan shari’ar ba tare da an kai ƙarshen ta ba, sai wannan Talatar da kotun ta yi zaman yanke hukunci daidai da buƙatar da Afakallahu ya nema.
Lauyan sa, Barista Abdullahi Laraye, ya yi ƙarin bayani da cewa: “An ɗauki tsawon lokaci ana shari’a, kamar shekaru huɗu, to Allah ya kawo ƙarshen abin; yau kotu ta yanke hukunci. Kuma duk abin da Afakallahu ya nema, kotu ta amsa. Na farko, ta ce shi Baban Chinedu ya rubuta wasiƙa a rubuce ya aika wa shi Afakallahu ya janye kalaman da ya yi a wannan bidiyon nasa, sannan ya ba shi haƙuri, kuma ita wannan takarda ya sadar da ita ga gidajen rediyo guda biyu a nan Kano da kuma gidajen talbijin guda biyu su ma a nan Kano, saboda duniya ta ji cewa ga abin da ya faru. Don haka kotu ta sa shi ya ba da hakuri tun da bai tabbatar da zargin da ya yi ba.”
Sai dai kuma lauyan Baban Chinedu, Barista Sidi ya bayyana cewa bai san da hukuncin ba, kuma zai ɗaukaka ƙara. Ya ce, “Gaskiya ni ban san an yi hukunci ba. In ma an yi hukunci, to daga bakin lauyan sa aka ji, don haka ni ban san an yi wani hukunci ba.
“Tun shekarar da ta gabata da mu ke wannan shari’a, wata rana mu ka zo ba su zo ba, kotu ta ɗaga, aka ba mu dama wani lokacin mu zo, kuma lokacin ya zo ba mu samu zuwa ba, kuma mu ka aika da takarda cewa ba mu samu damar zuwa ba, a ba mu wata ranar. To ba a sake aiko mana da wata takarda ba, ko mu a kan kan mu ko kuma shi wanda ake ƙara, ballantana mu san wannan shari’a ta na ci gaba da tafiya, domin wajibin kotu ne idan mutum bai samu zuwa ba ta sai ta yi abu guda biyu, ko dai a aika masa da takarda, ko kuma a je a liƙe masa a wajen da ya ke a wajen da ya ke cewa kotu za ta ci gaba da sauraron shari’a, don haka kotu ta ci gaba da shari’a har zuwa yanke hukunci, wanda kwata-kwata ba mu ma sani ba.
“Sai dai tunda an riga an zartar da hukunci, za mu ɗaukaka ƙara mu nemi kotu ta dakatar da wannan hukunci har sai an ji abin da kotun sama ta yi.”
![]()






