ƘUNGIYAR Masu Shirya Finafinai ta Arewa (AFMAN) ta nemi Hukumar ’Yan Sandan Nijeriya da ta gaggauta sakin jarumar Kannywood Khadija Mainumfashi, wadda aka kama a Kano aka kai ta Legas.
Buƙatar ƙungiyar tana cikin wata buɗaddiyar wasiƙa wadda shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Salisu Muhammed Officer, ya rubuta wa Sufeto Janar ’Yan Sanda a yau Asabar.
Ƙungiyar ta bayyana damuwar ta kan yadda aka tsare jarumar ba bisa ƙa’ida ba bisa zargin ɓatanci ga wani mutum mai suna Kabiru Musa daga Legas ya yi.
AFMAN ta ce abin da aka yi ya saɓa wa ’yancin ɗan’adam da kuma doka, musamman ganin shekarun ta bai haura 18 ba.
Ƙungiyar ta bayyana cewa jarumar marainiya ce da ke ƙarƙashin kulawar mahaifiyar ta, kuma ta shiga harkar fim ne da jagorancin ƙungiyar, ba kara-zube ba.
Don haka AFMAN ta yi kira da a binciki lamarin yadda ya kamata tare da tabbatar da gaskiya da adalci.
Ƙungiyar ta kuma buƙaci Sufeto-Janar ɗin da ya sa baki wajen ganin an saki jarumar tare da kare ta daga duk wata barazana da take fuskanta.
A ranar Jumaʼa, 24 ga Oktoba, 2025 ne dai wasu ‘yan sanda suka kama jarumar a Kano, sannan suka tafi da ita Legas, bayan wani ce-ce-ku-ce da ta yi a TikTok tsakanin ta da wata ƙawar ta mai suna Marwat Dallatu ‘yar Jihar Katsina, inda batun shi Kabiru Musa ya fito.

![]()







