• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, October 11, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Halin da ‘yan fim ke ciki: Kannywood tana neman taimakon gaggawa – AFMAN 

by ALI KANO
October 23, 2025
in Labarai
0
Halin da ‘yan fim ke ciki: Kannywood tana neman taimakon gaggawa – AFMAN 

Alhaji Salisu Mohammed Officer, Shugaban AFMAN na Ƙasa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƘUNGIYAR Masu Shirya Finafinai ta Arewa (AFMAN) ta yi gargaɗin cewa masana’antar shirya finafinai ta Kannywood tana cikin wani mawuyacin yanayi a yau wanda idan ba a kawo mata ɗauki ba zai jawo babban rasa aikin yi ga ɗimbin mutanen da ke cikin ta.

Shugaban ƙungiyar na Ƙasa,  Alhaji Salisu Mohammed Officer, shi ne ya yi wannan kiran a cikin wata takardar sanarwa da ya fitar mai taken “Gaskiyar Labarin Kannywood: Kira Don Taimakon Gaggawa” wadda ya fitar a yau.

Ya ce: “Muna yin kira ga gwamnati a matakai daban-daban, abokan haɗaka don kawo cigaba, da ‘yan kasuwa masu kishin ƙasa tare da zuba hannun jari, na su taimaka mana.”

Tun da farko, sai da Officer ya bi tarihin yadda masana’antar ta taso da ƙarfin ta, har zuwa yadda ta zama abar tausayi.

Ya ce: “Masana’antar Kannywood, wadda take abar alfaharin matasan Arewacin Nijeriya, ba ta fara da kuɗin gwamnati ko tallafin ƙasashen waje ko haɗin gwiwar wasu manyan mutane ba. Ta fara ne da tsantsar sha’awa, sadaukarwa, da burin matasa masu hangen nesa waɗanda suka ƙudiri niyyar su bada labaran su, su yaɗa al’adun su, kuma su dogara da fim a matsayin wajen neman abincin su.

“A farkon shekarun 1990, a lokacin da arewacin Nijeriya bai da wani tsarin nishaɗi a hukumance, waɗannan matasa ne suka samar tare da rainon harka, ta hanyar haɗa kai, tattara ‘yan kuɗaɗen da ke hannun su, aro kyamarori, raba rubutun labarai a tsakanin su, tare da yin atisaye a fili. Tun daga tushe ne suka gina wannan masana’anta, bisa ƙirƙira da fata kaɗai.

“Duk da cikas da rashin tallafi daga kowace hukuma, Kannywood ta bunƙasa, ta zama ɗaya daga cikin manyan masana’antun finafinai na ‘yan ƙasa a nahiyar Afrika.

“Harkar fim ta zama hanyar samun kuɗi, tallafawa, tare da zaburarwa ga dubban matasa a jihohin Arewa da ma wasu sassa.”

Ya ce amma a yau masana’antar mai cike da ƙwazo da karsashi tana fuskantar mawuyacin hali.

Ya ƙara da cewa a yau Kannywood tana fama da matsaloli masu tsanani da suka haɗa da satar haƙƙin mallaka wadda ta hana masu fim samun riba; rashin damar samun jari wanda ya taƙaita samar da finafinai; rushewar hanyoyin rarraba kasuwa wanda ya tagayyara kasuwanci, da kuma mafi muni, wato “rashin wani tsarin gwamnati da ke karewa ko tallafa wa wannan muhimmiyar sana’a.”

Shugaban ya ce: “Matasan mu da a da suke aiki tuƙuru a ɗakin gyara hoton bidiyo ko rubuta labarai, yanzu da dama sun zama marasa aikin yi. Ƙwarewa na lalacewa, mafarkai na dusashewa, kuma talauci yana ƙaruwa.”

Takardar sanarwar da AFMAN ta saki a yau

AFMAN ta yi gargaɗin cewa wannan koma-baya ba fa batun fim kaɗai ba ne, koma-baya ne ga makomar dubban matasan Nijeriya.

Ta ce: “Kannywood ba nishaɗi ba ce kawai, hanya ce ta bunƙasa tattalin arziki, jawo matasa a jiki tare da sama musu abin- yi, alkinta al’adu, da kuma ilimantar da al’umma.

“Sai dai, idan ba a samu tallafin gaggawa daga gwamnati, ko masu zuba jari, samar da ƙudirorin haɓaka harkar, wannan mafarki zai gushe.”

Don haka ƙungiyar ta yi kira ga gwamnati a matakai daban-daban, abokan haɗaka don kawo cigaba, da ‘yan kasuwa masu kishin ƙasa tare da zuba hannun jari, na su taimaka mata.

“A taimaka mana wajen sake farfaɗo da masana’antar nan, da kuɗaɗe, horo, gina cibiyoyi (samar da ababen more rayuwa), da samar da tsari mai kyau na dokoki,” inji ta.

A takardar sanarwar wadda Sakataren AFMAN na Jihar Kano, Malam Mustapha Shariff Anwar, ya fassara daga Turanci, ƙungiyar ta yi nuni da cewa, “Idan aka samu tallafi mai inganci, Kannywood tana iya zama wata dukiyar ƙasa, mai samar da kunzumin ma’aikata da yawa, sannan kuma muryar ci gaba.”

Ta kammala da cewa, “Lokaci ya yi da za mu yi hoɓɓasa ga wannan jajirtacciya, haɓakakkiya kuma masana’antar da biyan buƙatun jama’a ne a gaban ta, tun kafin lokaci ya ƙure mana.”

Loading

Tags: AFMANagajiArewamatasaSalisu Mohammed Officer
Previous Post

Ƙungiyar AFMAN ta nemi ‘yan sanda su saki jarumar Kannywood Khadija Mainumfashi

Next Post

Za a ƙaddamar da sabuwar ƙungiyar ‘yan fim ta KAFIGAN yau a Kaduna

Related Posts

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu

October 6, 2026
Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba
Labarai

Za a ƙaddamar da reshen Kaduna na KAFIGAN ranar Asabar

October 1, 2026
Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu
Siyasa

Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu

September 30, 2026
Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa
Siyasa

Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa

September 30, 2026
Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa
Siyasa

Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa

September 29, 2026
Next Post
Za a ƙaddamar da sabuwar ƙungiyar ‘yan fim ta KAFIGAN yau a Kaduna

Za a ƙaddamar da sabuwar ƙungiyar 'yan fim ta KAFIGAN yau a Kaduna

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!