• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ƙungiyar Kadawood ta barranta da ayyukan baɗala da  Aliyu Mero yake yaɗawa a soshiyal midiya

by ALI KANO
December 10, 2025
in Labarai
0
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

 

ƘUNGIYAR masu shirya finafinai ta Kadawood da ke Kaduna (Kadawood Filmmakers and Entertainers Association) ta nesanta kan ta daga ayyukan da wani matashi ɗan fim mai suna Aliyu Musa (Mero) yake aikatawa a soshiyal midiya, ta ce iskanci da rashin tarbiyya ne.

A cikin ‘yan kwanakin nan, an ga wasu guntayen bidiyo a kafofin sada zumunta inda Mero yake aikata wasu abubuwa da suka danganci batsa, abin da bai yi wa ‘yan Kannywood da dama daɗi ba.

A cikin wata sanarwar musamman da ya fitar a yau, Shugaban Kadawood, Malam Nura MC Khan, ya ce: “Muna so mu sanar da al’umma cewa hukumar Kadawood Filmmakers and Entertainers Association ta samu labarin wani yaro mai suna Aliyu Musa (Mero) wanda yake wallafa bidiyo masu ɗauke da iskanci, rashin tarbiyya, da abubuwan da ba su dace da al’ada da ƙimar al’umma ba.

“Muna bayyana a fili cewa:

1. Babu wata alaƙa ko haɗin kai tsakanin mu da wannan yaro.

2. Ba ma goyon bayan duk wani abu da ya shafi irin waɗannan munanan halaye.

3. Irin waɗannan bidiyo ba sa wakiltar masana’antar film na Jihar Kaduna ko ƙa’idojin da muka tsaya akai.”

Ƙungiyar ta yi kira ga duk ‘yan fim, masu shirya fim, da sauran ƙungiyoyin masana’antar film a Jihar Kaduna da su fito fili su barrantar da kan su daga Aliyu, “domin kada a danganta wannan iskanci da harkar fim.”

Ta ƙara da cewa, “Muna kuma ba da shawara mai ƙarfi cewa kada a sake saka shi a cikin kowace irin harkar fim ko ɗaukar aiki a ƙarƙashin dukkanin ƙungiyoyi ko kamfanonin shirya finafinai.

“Masana’antar fim ta Kaduna masana’antar tarbiyya ce, wadda take fitar da saƙo mai ma’ana ga jama’a—not wurin yada abin da zai ɓata tarbiyya ko karya mutunci.”

Ta yi godiya ga duk masu goyon bayan tsaftar harkar fim, tare da addu’ar “Allah ya ƙara mana zaman lafiya da cigaba.”

Loading

Tags: Aliyu Musa MerobaɗalaKadawoodNura MC Khansoshiyal midiya
Previous Post

Abin da ya sa na buɗe kantin kayayyaki – jarumar Kannywood Fauziyya Maikyau

Next Post

Za a yi bikin naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa a Daura ranar Asabar

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Za a yi bikin naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa a Daura ranar Asabar

Za a yi bikin naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa a Daura ranar Asabar

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!