• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

An ɗaure fitaccen daraktan fim shekaru biyu da rabi saboda damfarar Netflix miliyoyin daloli

* Yana hawa kan kuɗin sai ya shiga bushasha abin sa, har da sayen motoci biyar ƙirar Rolls-Royce

by IRO MAMMAN
June 30, 2026
in Labarai
0
An ɗaure fitaccen daraktan fim shekaru biyu da rabi saboda damfarar Netflix miliyoyin daloli

Carl Erik Rinsch a wajen bikin New Directors' Showcase a ranar 23 ga Satumba, 2015 a birnin Los Angeles, California. (Hoto: John Sciulli/Getty)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

AN yanke wa fitaccen daraktan finafinan Amurka, Carl Rinsch, wanda aka fi sani da ba da umurni a fim ɗin ’47 Ronin’ a cikin 2013, hukuncin ɗaurin shekara biyu da rabi (watanni 30) a gidan yari bayan an same shi da laifin tafka wa kamfanin shirya finafinai na Netflix damfarar miliyoyin daloli.

Masu gabatar da ƙara a birnin New York ne suka bayyana hakan a ranar Litinin.

Tun a bara ne aka samu Rinsch da laifin karkatar da dala miliyan 11 da Netflix suka ba shi a shekarar 2020 domin samar da fim mai dogon zango kan kimiyyar ƙirƙira (science fiction) mai suna ‘White Horse.’

A cikin wata sanarwa, lauyan Gwamnatin Tarayya na Kudancin Gundumar New York, Jay Clayton, ya ce: “Maimakon ya yi amfani da kuɗin wajen shirya fim ɗin, sai Rinsch ya saka su cikin hadahadar sayen hannayen jari masu matuƙar haɗari da kuma kuɗaɗen dijital na kirifto (cryptocurrency), sannan ya kashe miliyoyin daloli wajen sayen kayayyakin alatu domin amfanin kan sa.”

An yi zargin cewa yana hawa kan kuɗin sai ya shiga bushasha abin sa, ya sayi kayayyaki da suka haɗa da tufafin alfarma, kayan ɗaki masu tsada, mota ƙirar Ferrari ja, da kuma motoci biyar ƙirar Rolls-Royce.

Baya ga hukuncin ɗaurin shekara biyu da rabi da aka yanke masa, kotun ta kuma umurci Rinsch, mai shekara 48, da ya mayar da dala miliyan 11.

Lauyoyin sa sun roƙi kotu da ta sassauta masa hukunci, suna masu cewa karkatar da kuɗin ta faru ne sakamakon matsin lambar da yake fuskanta a harkar aikin sa da kuma rikicin mutuwar auren sa.

Ko da yake masu gabatar da ƙarar ba su ambaci sunan Netflix kai-tsaye ba, a baya an ruwaito cewa Rinsch ya shiga taƙaddama da kamfanin kan wani fim mai dogon zango da aka fara sanya wa suna ‘White Horse’, amma daga baya aka canja sunan zuwa ‘Conquest’.

Bisa ga takardun kotu, an tsara labarin fim ɗin mai dogon zango ne kan wani masanin kimiyya da ya ƙirƙiri wasu kwafe (clones) masu ƙarfi, waɗanda aka kora zuwa wani yanki mai katanga a wani birni a ƙasar Birazil. A can ne za a ga sun fara haɓaka fasahohi na zamani tare da shiga rikici da mutane da kuma tsakanin su.

Shi dai Rinsch, ya fara shahara ne a matsayin daraktan babban fim da fim ɗin ’47 Ronin’, wanda fitaccen jarumi Keanu Reeves ya ja.

Kafin a yanke masa hukunci, Reeves ya rubuta wa alƙalin kotun wasiƙa yana roƙon a yi wa tsohon daraktan nasa sassauci tare da tausayawa, yana mai bayyana shi a matsayin “ƙwararren mai fasaha” wanda ya jefa kan sa cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi.

Loading

Tags: Carl RinschdamfaraɗauriHollywoodKeanu ReevesNetflix
Previous Post

Mawaƙi Ado Gwanja yana kwance ba lafiya

Next Post

Furodusa a Kannywood, Fatima Lamaj ta zama shugabar AFMAN reshen Jihar Kaduna

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Furodusa a Kannywood, Fatima Lamaj ta zama shugabar AFMAN reshen Jihar Kaduna

Furodusa a Kannywood, Fatima Lamaj ta zama shugabar AFMAN reshen Jihar Kaduna

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!