TSOHON shugaban Ƙungiyar Furodusoshi ta Jihar Kano kuma dattijo a harkar fim, Malam Auwalu Isma’il Marshall, ya bayyana matan da ke cikin Kannywood a matsayin babbar matsalar da ta ke ci wa masana’antar tuwo a ƙwarya.
Malam Auwalu ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke jawabi a taron addu’a ga marigayi darakta Nura Mustapha Waye da aka gudanar a yammacin ranar Laraba, 13 ga Yuli, 2022 a Majalisar Matasa ta Tarauni da ke Court Road, Gyaɗi-Gyaɗi, Kano.
Da ya dubi matan da su ka halarci taron, sai ya ce: “Maganar gaskiya, ku mata ku ne matsalar wannan harkar, domin duk wata matsala da ta ke fitowa, to idan aka duba sai a ga daga wajen matan ta fito. Don haka ku ne ku ka fi samar da matsala a cikin wannan masana’antar.”

Ya ci gaba da cewa, “Ba wai mu na gudun ku ba ne, mu iyayen ku ne, amma ina jawo hankalin ku da ku gyara al’amuran ku domin kiyaye mutuncin kan ku da kuma na harkar fim ɗin, domin a yanzu zaman da mu ka yi mu na taron addu’a ne ta wani daga cikin mu da Allah ya yi masa rasuwa, to kun ga a ko da yaushe mutuwa za ta riske mu. Don haka mu san tanadin da za mu yi na zuwan tamu mutuwar.”
Malam Auwalu, wanda jigo ne a masana’antar, ya yi kira ga shugabannin masana’antar da su riƙa ɗaukar kowa a matsayin ɗa, ta yadda za a hukunta shi idan ya yi ba daidai ba.
![]()






