DUK da cewa tsohuwar jaruma, marigayiya Hannatu Umar Sani, ta daɗe da barin masana’antar shirya finafinai ta Kannywood, abokan sana’ar ta ba su manta da ita ba. Sun nuna kaɗuwa da alhinin rasuwar ta da ta faru a yau a Abuja, musamman ganin ba jinya ta yi ba. Duk inda ka leƙa a soshiyal midiya sai addu’ar Allah ya jiƙan ta za ka gani. Hakan ya nuna ta zauna lafiya da abokan sana’ar ta.
Bayan labarin rasuwar ta da mujallar Fim ta buga a yau, mutane da dama sun riƙa tambayar wacece Hannatu Umar Sani? Wasu ba su ma san ta a fim ba saboda ta daɗe da barin industiri, ciki kuwa har da da dama daga cikin ‘yan fim maza da mata na wannan zamanin domin ba su yi rayuwa da ita a masana’antar ba.
Hannatu ta rasu ba zato ba tsammani, ta na da kimanin shekaru 34 a duniya.
Mujallar Fim ta gano cewa ita ce ‘yar’auta a ɗakin su. Ta rasu ta bar yayyen ta 10 a raye.
Hannatu dai ta fara yin fim ne a kamfanin ‘Lerawa Production’ na fitaccen furodusar nan mazaunin Kaduna, wato El-Sa’eed Yakubu Lere.
Yakubu Lere, wanda shi ma mutuwar ta girgiza shi, ya faɗa wa mujallar Fim cewa sunan fim ɗin da Hannatu ta fara yi shi ne ‘Ummi’, inda ta fito tare da Safiya Musa da Sadiya Gyale a matsayin jarumai. Jarumin fim ɗin shi ne Sani Musa Danja.
Hannatu da Sani sun yi waƙa a fim ɗin mai taken “Da Soyayya Na Fito Yarinya Da Soyayya Zan Koma Gida.”
Ya ce a lokacin, shekarun ta 14 kacal.
“Ta shiga harkar fim ne da amincewar iyayen ta duka.” Ya ce baki da baki mahaifin ta ya ba shi amanar ta a lokacin da ya sanya ta a fim.
Domin ya taimaka mata a harkar fim, Lere ya ɗauki Hannatu ya kai ta Kano ya haɗa ta da Sani Danja, kuma na yi wanda a lokacin ya na soyayya da Maryam Abubakar (Jankunne), sai ya kasance Hannatu da Maryam su ne jarumai mata na kamfanin 2-Effects Empire na su Sani da Yakubu Muhammad.
Daga nan Sani ya shiga soyayya da ita, kuma ƙaunar da ke tsakanin su ta ɗore har mai rabawa ta raba.
Marigayiyar ta yi finafinai da dama a kamfanin 2-Effects da ma wasu kamfanonin, wanda ya sa kusan sai da ta danne wasu daga cikin jaruman Kannywood da tauraron su ke haskawa a wancan lokacin.
Daga baya ta yi aure, to amma sai auren ya mutu. Kuma ba ta haihu ba.
Ta ɗan yi ƙoƙarin komawa harkar fim, inda Sani Danja ya ɗan riƙa jefa ta a cikin wasu finafinai, sai dai ba ta yi tasiri sosai ba da yake ba ta dawo harkar gadan-gadan ba, kuma ma ta koma karatu a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Ba mu san matsayin karatun nata ba kafin Allah ya ɗauki ran ta, amma mun san ta kan je wajen yayar ta da ke aure a Abuja ta ɗan zauna sannan ta koma gida Kaduna.
Ashe wannan zuwan da ta yi inda ta ɗan yi makwanni a Abujan shi ne zuwan ta na ƙarshe. Allahu Akbar!
Kamar yadda mu ka ba ku labari, an yi jana’izar ta a babban masallacin ƙasa (National Mosque) da ke Abuja, aka kuma binne ta a maƙabartar da ke unguwar Gudu.
Allah ya jiƙan ta da rahama, amin.
![]()







