A YANZU haka dai fitaccen marubuci, furodusa kuma jarumi a Kannywood, Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, ya na shirin fito da wani sabon littafi mai suna ‘Dausayin Fasaha’ wanda ya ƙunshi waƙoƙin soyayya da na al’amuran yau da kullum da ya rubuta.
Littafin, wanda zai fito nan gaba kaɗan, kuma zai zama wani sabon salo ga masu karatu kasancewar Malam Ado ya ɗauki lokaci mai tsawo bai fito da littafi ba sannan kuma wannan shi ne karo na farko da ya wallafa littafin da ya ƙunshi waƙoƙi kaɗai.
A tattaunawar da mujallar Fim ta yi da shi, marubucin ya bayyana manufar sa ta fitar da wannan littafi, inda ya ce, “To wannan tsarin da na fito da shi a littafin ‘Dausayin Fasaha’ ba wani sabon salo ba ne, domin shi rubutun adabi ya ƙunshi abu uku ne: akwai rubutun zube da na waƙa, sai na wasan kwaikwayo. To ina rubutun waƙa da na wasan kwaikwayo amma wanda mutane su ka fi sani na da shi shi ne rubutun zube, sai wasan kwaikwayo.
“Amma ko a cikin zuben za su ga akwai waƙa. To, saboda haka duk wanda ya yi rubutun zube kuma ya saka waƙa a cikin sa, ana sa ran ya ɗan fahimci wani abu a ɓangaren waƙa.
“To abin da na yi shi ne ina son na cike gurbi na uku, na waƙa kenan. Shi ya sa na tattaro waƙoƙin da na yi waɗanda su ke a cikin littafi da waɗanda ba sa cikin littafi, sai na haɗa su na yi littafi. Aƙalla ya kai shafi saba’in.
“Wannan shi ne yadda aka yi na samar da littafin waƙar.”
Gidan Dabino ya yi nuni da cewa ba wai duka sababbin waƙoƙi ba ne a cikin sabon littafin, akwai waƙoƙin da su ke tun na 1990 da waɗanda su ka biyo baya, shi ne ya harhaɗa su.
Akwai kuma wani salon da ya zo da shi. Ya ce, “Kowace waƙa ina rubuta yadda na yi ta da lokacin da kuma dalilin yin ta da shekarar da aka yi ta. Kuma na yi hakan ne saboda na sauƙaƙa wa masu bincike, kada su zo su na tambayar ya aka yi kaza. Ka ga ko da bayan ba na nan, in Allah ya ɗauki rai na, mutane ba sai sun sha wahalar bincike ba.”
A game da lokacin da littafin zai fito da kuma kasuwar da za a sayar da shi kuwa, sai sha’irin ya ce, “To shi littafin a yanzu na kammala shi, yanzu abin da ya rage na bai wa malaman da su ka shafi adabin waƙa su gani su sa albarka a ciki don idan aka masa a kan abin to in-sha Allah littafin zai fito.
“Kuma ba wai a onlayin za mu fitar da shi ba, za mu fitar da shi ne haka, a bayar da na bayarwa kuma masu buƙata don sha’awa su saya. In kuma Allah ya yi wasu makarantu masu nazarin Hausa za su saka shi a tsarin karatun su, nan ma ka ga za a iya samun wata dama ta sayar da shi yadda zai zama littafin nazari kenan.
“To wannan shi ne abin da mu ke fata. Amma dai a cikin shekarar nan za a fito da shi in-sha Allah, don yanzu dai na riga na gama, malamai masu nazari na ke so su sassa hannu.”
Sai dai ya yi wani tsokaci, da ya ce, “Amma dai ba lallai ba ne a same shi a kasuwa, saboda yanzu ka san wajen sayar da littattafan ba kamar a baya ba ne, don a yanzu sai ka zaɓi su wa za ka bai wa, kuma ka san akwai littafin da ba wai damuwa aka yi da sayen sa sosai ba, kamar littafin waƙoƙi ko na wasan kwaikwayo, in ba an saka shi a manhajar karatu ba. To shi ya sa mu ke fatan a saka shi yadda yara za su neme shi kuma a karanta shi a jami’o’i da kwalejojin ilimi.
“Amma wanda ya ke ba neman sa ake yi ba, sai dai ka bugo kaɗan a ajiye a matsayin gwaji. Don haka ko a yanzu ba ko’ina za ka samu littafi na ba saboda yanayin kasuwar, sai dai idan ana nema a makarantu za a buga wa ɗalibai kamar 500 har zuwa 1,000 ma. To ka ga da na samu wannan damar sai ya zama kasuwar ta koma can kamar jami’o’i da wasu cibiyoyin ilimi. Amma dai a kasuwar mu na kai kaɗan ba da yawa ba.”
Dangane da abin da ya bambanta wannan littafin da sauran waɗanda ya wallafa a baya kuwa, sai Gidan Dabino ya ce, “To, bambancin su shi ne waƙa ce. Waƙa kuma ta sha bamban da waƙar baka ko labari ko zance. Wanda ba shi da sha’awar karanta waƙa ba zai saurare shi ba, shi ya sa za ka ga da wasan kwaikwayo da waƙa ba su cika yin farin jini ba a kasuwa kamar rubutun zube. Kamar yadda na faɗa, sai idan an saka shi a manhaja ko idan an ce a je a neme shi za a yi bincike ko wata buƙata ta musamman. Saboda haka bambancin su shi ne waƙa ta bambanta da sauran rubutu; ita shiryayyiyar magana ce wadda ake yin ta da ɗango da ƙafiya.

“Kuma ban taɓa rubuta littafin waƙa ba sai a wannan karon, amma dai ina rubuta waƙoƙi a karanta su ko a tarukan mu na marubuta ko na shiga gasa da su, ko gasar da aka yi a Sokoto wadda aka yi a kan matsalar tsaro, na shiga kuma na jarraba sa’a ta. Ka ga bambancin su kenan.
“Kuma ban buga littafin waƙa don lallai sai na yi cinikin sa da yawa ba, na buga ne don lallai a san na yi kuma ya shiga hannun masana da manazarta kamar yadda ake ganin babu wasu ayyuka na waƙoƙi a rubuce da yawa. To wannan zai taimaka a ƙara ci gaba, don ina ganin zan ci gaba, ba wai na tsaya daga haka ba, don akwai wasu waƙoƙin waɗanda ko dai na ƙara na ci gaba ko kuma na ƙara fitar da wani littafin, duk dai yadda ta kama, don ka na yin littafi ba don kawai a sayar ba sai don ka bayar a karanta ka samu ladar.
“Don haka abin da zan ce, wanda shi ne na ƙarshe, na yi littafi na wasan kwaikwayo wanda shi ne masana wasan kwaikwayo su ke cewa a ƙasar Hausa ba a taɓa yi ba, wanda a ce littafi ne na wasan kwaikwayo aka yi shi na ɗaya da na biyu, wato wasan kwaikwayo na ‘Malam Zalimu’. A tsari na babu ci gaban sa, amma shi Abba El-Mustapha da ya ɗauki nauyin shirin a kamfanin sa da su ka ji daɗin labarin sai su ka ce a ci gaba, wanda aka samar da ‘Malam Zalimu Sabon Yanka’. To kuma da zan yi sabon littafi, tun da ci-gaba ne, sai na tambayi masana ko ana yin hakan? Sai su ka ce ana yi a ƙasashen Turai, amma dai a adabin Hausa ba a taɓa yi ba. To wannan littafin na wasan kwaikwayo ba a taɓa yin sa ba a ƙasar Hausa sai wanda na yi. To wannan shi ne tarihin da na ke son na ci gaba da samarwa a adabin Hausa.”