SHUGABAN shirya bikin karrama gwarazaye mai suna ‘2023 Arewa Heroes and Philanthropic Awards of Excellence’, Ambasada Nyam Terry, wanda aka fi sani da MC Terry, ya bayyana dalilin shirya taron tare da nuna farin cikin sa game da yadda aka fara taron bikin lafiya, aka gama lafiya.
Da ya ke zantawa da mujallar Fim bayan kammala taron, Terry ya ce, “Abin da ya sa mu ka shirya wannan ‘programme’, mun kai shekara 24 da mu ke yin wannan ‘programme’, kuma mun shigo Kaduna a shekarar da ta gabata. Da mu ka zo, mun buɗe ‘portal’, mu ka ce mutane su zaɓi mutanen da su ka yi aiki a Arewa, sai aka yi ‘nominating’ wasu sunaye, wannan dalilin ya sa mu ka zo nan wurin yau. Kuma mun gode wa Allah mun gama lafiya.
“Sannan kuma ina kira ga jama’a duk abin da za mu yi, mu yi shi da kyau, mu sa Allah a gaba, saboda Allah shi ne komai.
“Ina kuma godiya ga ‘team’ ɗi na da waɗanda su ka ɗauki nauyin wannan biki, domin in ba don su ba, ba za mu gama wannan abu ba. Ga shi mun gama lafiya. Na gode masu sosai.”
An fara gudanar da taron da misalin ƙarfe 12:50 a ɗakin taro na Arewa House, Kaduna.
Da farko, Nyam Terry ya fara da bada haƙuri na rashin fara taron da wuri.
Ya ce, “Ban zo da wani saƙon barka da zuwa mai tsawo ba, sai dai ina yi wa kowa barka da zuwa.”

Ya ci gaba da cewa, “A shekarar 2018, ina da gidan talbijin na onlayin da gidan rediyo na onlayin. Duk na rufe su, amma zan dawo da su Kaduna, kuma duk su na aiki ƙwarai. Amma dawowa da su Kaduna zai sa mutum sama dubu biyar su amfana.”
Bayan ya gama jawabin sa ne, ya yi magana a kan za a dakatar da taron, domin Musulmai su je su yi sallah.
Bayan dawowa daga sallah, sai aka fara miƙa kambin karramawa ga wasu daga cikin gwarazan.
A karo na farko, an karrama Abubakar Bashir Maishadda, Maikuɗi Cashman, marigayi Rabilu Musa (Ibro), wanda ɗan sa Hannafi ya karɓa, sai Sani Musa Danja.
Sani Danja da Maishadda ba su samu halarta ba, don haka jarumi Rabi’u Rikadawa ya karɓar masu.
An ci gaba da sauran abubuwa, kamar naɗa ‘yan matan da su ka yi nasara a zaɓen Fuskar Kaduna da kuma Fuskar Arewa.
A karo na biyu, an karrama Misis Kala Abdulmalik, Hajiya Safaa M.U. Adam, Prince Ɗahiru Bala da marigayi Janar Hassan Katsina, Rabi’u Rikadawa, Wassh Waziri Hong, Malam Musa Mohammed Abdullahi, Abba Muhammad (Mujallar Fim) da Hajiya Rabi Saulawa (Shugabar Jam’iyyar Matan Arewa).
A karo na uku kuma, ‘MACA Peace Ambassadors and Unity Affair Africa’ ta naɗa Rikadawa, Malam Musa Mohammed Abdullahi, Wassh Waziri Hong, Prince Ɗahiru Bala, Misis Kala Abdulmalik, Safaa M.U. Adam, Hajiya Rabi Saulawa a matsayin jakadun zaman lafiya (wato ‘peace ambassadors’).

Haka kuma, Mista Terry ya ƙaddamar da makarantar koyar da fim mai suna ‘G-Film Academy’. Sannan ya yi bayanin yadda za a shiga makarantar, ya ce, “Ga masu sha’awar shiga makarantar, da farko za su yi rijista a kan N10,000. Bayan biyan kuɗi, za mu tantance ɗaliban, daga nan kuma sai su biya N15,000, wanda a ciki za a ba su kayan rubutu da riga mai ɗauke da sunan makarantar. Zangon karantun kuma, akwai na mako huɗu, akwai na mako takwas.”
An tashi daga taro da misalin ƙarfe 4:00 na yamma.
Sai dai da yawa daga cikin waɗanda aka ayyana cewa za a karrama ba su halarta ba, musamman manyan mutane.
Wasu daga cikin waɗanda su ka halarci bikin sun haɗa da Naseer Khan, Abubakar Hunter, A.A. Rasheed Kabala, Sagir Baban Kausar, Sabi’u Gidaje, Abdulrasheed Muhammad, Shu’aibu, Modibbo Muhammad, Jamila Ibrahim Dassi, Al-Amin Abdullahi Albani da Ibrahim Ɗanbuzu.



![]()







