• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, August 24, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Nasarorin Hukumar Tace Finafinai a 2017, cewar Afakallahu: Mun yi abin da ya kamata

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
March 28, 2018
in Labarai
0
Nasarorin Hukumar Tace Finafinai a 2017, cewar Afakallahu: Mun yi abin da ya kamata
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
SHUGABAN Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Malam Isma’il Na’abba (Afakallahu) ya bai wa kan sa babban maki wajen lissafin nasarorin da ya samu a cikin shekarar 2017 da ta shude.

 

Yayin da ya ke bayyana haka a hirar sa da mujallar Fim, Afakallahu ya ce, “An cimma abubuwa da dama wadanda idan aka ce za a nuna mana su a majigi kafin mu zo wannan lokaci, to za mu iya cewa ba za mu iya cim musu ba saboda irin kalubalen da mu ka zo mu ka tarar.

“Kalubalen farko shi ne a dauko ka a cikin al’ummar da ka ke tare da ita kuma a ce yau kai ne za ka ja ragamar wannan al’ummar. Amma Allah abin godiya, sai Ya ba mu damar da za mu zo mu daga kai mu ce mu mu ka yi kaza domin ci-gaban wannan sana’a. 

 

“Kuma mu na godiya ga shi gwamna da ya yi wannan tunani ya ga cewar Allah Ya na shugabantar da  al’umma ne daga cikin jinsin su, to ka ga babbar ni’ima shi ne yau a ce jagoran ku naku ne na cikin ku. Shi ya sa Allah da Ya ke aiko annabawa ya na aiko su ne a cikin jinsin mutane ba mala’iku ba.

“To don haka nasara da mu ka samu ta gaba ita ce samar da hadin kan masu harkar finafinai su ka zamo masu magana da murya daya. Don na zo na samu harkar kowa da inda ya sa gaba; ko ni kai na akwai inda na sa gaba, amma na samar da tsarin da aka gudanar da zabe tun daga kan dukkanin wani rassa na harkar fim. 

“To wannan zabe ya samar da yanayi mai kyau da aka gudanar da babban zabe na MOPPAN wanda shi Gwamnan Kano shi ne ya bada kudi miliyan daya da rabi don a gudanar da zaben sannan rarar kudin aka kama ofis aka zuba kujeru ka ga wannan ci-gaba ne. 

“Sannan gwamnati ta samar da ilimi ta hanyar horaswa domin gwamna ya bada dama da mu yi hadaka da National Film Institutional Media Studies domin mu samar da ilimi, inda mu ka dauko daga tushe tun daga kan rubutu script har zuwa kallon sa a talbijin. Kuma sai ya zama kowane bangare aka dauko mutum 15 wanda idan aka hada za su ba ka mutum 45 kuma wannan gagarumar nasara ce da ba a taba yi ba a masana’antar mu ta fim. 

”Sannan mun fito da ofisoshi na rassa wanda za a rinka tuntuba a wannan hukumomi 44 da mu ke da su a Jihar Kano wadanda su na sanya ido a kan finafinan da ake sayarwa da kuma wadanda ake nunawa a gidajen kallo ta yadda masu sana’ar za su yi alaka da su ta hanyar yadda zai je ya kai kayan da ya sayar.

 
“Sannan su kan su ’yan kasuwar an samar da hanyar yadda za su san kasuwancin zamani saboda shi fim ya na da hanyoyin da ake bi wajen sayar da shi tun kafin ya shiga kasuwa, amma sai ya zama mu namu kasuwar kadai su ka rike. Wannan ya haifar da matsalolin da harkar ta samu kan ta a ciki.

 

“To amma a yanzu an samar da hanyar ilimantarwa, don haka sai mu ke samar da tsarin gidan kallo guda dari biyar yadda gwamnati ta shiga cikin harkar ta yi masu tsari wanda za a samar masu da kayan kallo na zamani. Ka ga wannan zai magance yawan fitowar finafinai domin a da sai ka ga fim hamsin ya shiga kasuwa lokaci guda, kuma ba mai iya saya saboda fim ana yin sa ne don a samu ilimi. Sai mu ka rage ya koma goma ; a yanzu ma ya koma biyar. 

“Duk da haka ba mu tsaya ba sai da mu ka samar da wani kwamiti a karkashin Hamisu Lamido Iyan-Tama wanda za su zo su zauna su kalli yadda za a kawo ci-gaba a harkar kasuwancin nan. Kuma da shawarwarin da su ka bayar za mu yi amfani don ganin an habaka kasuwancin fim.

“To ka ga wannan duk abubuwa ne da aka gudanar don ganin an dora ita sana’ar a kan ingatancciyar hanya wanda zai zamo ana yin finafinai da su ke wakiltar Malam Bahaushe.

“Don ka ga lokacin da na zo gidan nan ba mu da mota sai da tawa na rinka amfani. A yanzu an samar mana da motoci har guda biyar, wanda bayan wannan ita kan ta masana’antar fim mun samar mata da mota, wadda ranar da za a yi biki na yaye daliban da aka horar Gwamna zai gabatar da wannan mota ga masana’antar fim gaba daya don a saka ta ya zama kowa ya na amfana. Don haka za a saka ta a karkashin wani kwamiti, don ba za a bar ta kamar yadda aka bari a baya ba, su ka salwanta, ba a san inda su ke ba. 

“Don mu na son mu gadar da duk wani abu da ko da ’ya’yan mu sun zo su san mun yi abin da ya kamata.”

 
 

Loading

Tags: Nasarorin Hukumar Tace Finafinai a 2017Finafinai
Previous Post

ABBA NA

Next Post

Asabe Madaki: Buri na shi ne duniya ta san ni

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
DAGA MUKHTAR YAKUBU

Asabe Madaki: Buri na shi ne duniya ta san ni

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!