A RANAR Lahadi, 21 ga Janairu ne furodusa a Kannywood, Malam Mukhtari Isah PRP, zai aurar da ‘yar sa ta biyu, wato Sumayya, ga Bakir Saminu Rabi’u.
Za a ɗaura auren a Kano a unguwar Briged Kwana Huɗu Bus Stop, a layin Mai Unguwa Nasiru, da misalin ƙarfe 11 na safe.

Mukhtari Isah PRP dai mashiryin fim ne da ya daɗe ana damawa da shi a cikin harkar fim sama da shekaru 20, inda ya bada umarni da kuma ɗaukar nauyin shirya finafinai masu yawan gaske.
A yanzu shi ne mai samar da wajen aiki da kayayyaki a shirin wasan kwaikwayo na ‘Kwana Casa’in’ na tashar talabijin ta Arewa 24.
![]()







