• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, May 14, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Kama ’yan fim: Yanzu na fara, inji Afakallahu

by DAGA ABBA MUHAMMAD
August 18, 2019
in Labarai
0
Alhaji Isma'il Na'abba (Afakallah)

Alhaji Isma'il Na'abba (Afakallah)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
*’Kama Sunusi Oscar bai da alaƙa da siyasa’
 
BABBAN Sakataren Hukumar Tace Finafanai ta Jihar Kano, Alhaji Isma’ila Na’abba (Afakallah), ya bayyana cewa in dai batun kama ’yan fim masu laifi ne, to yanzu ma ya fara. Kuma ya ce kama darakta Sunusi Oscar 442 da hukumar ta yi ba ya da alaƙa da siyasa kamar yadda wasu ke iƙirari.
 
A hirar sa da mujallar Fim kwana ɗaya bayan kotu ta tura daraktan gidan maza, Afakallah ya ce, “A gaskiya wannan abu ba shi da alaƙa da siyasa. Kuma ita Hukumar Tace Finafinai duk lokacin da ka yi waƙa, ballantana waƙar da aka haɗa da hotuna, wannan darakta ya saki wata waƙa mai suna ‘So Na Amana’, wadda waƙar nan abu ne aka nuna na tsiraici, fitsara da kuma ɓata tarbiyyar mutanen Jihar Kano. 
 
“Don haka babu wani abu da ke alaƙa da siyasa, tunda a kotu aka gurfanar da shi, kuma a kotu ba a ce don ya yi wani abu na siyasa ba ne, an karanta masa abin da ita hukuma ta ke tuhuma a kan abin da aka yi. Wanda kuma a kotu kamar yadda lauyan mu ya tabbatar mana cewa ya amsa cewa shi ne ya bada umarnin waƙoƙin nan da sauran su. Don haka kotu ta ɗage zama har zuwa 20 ga wata. Don haka babu maganar siyasa.
 
“Tun kafin zuwan wannan gwamnatin ake haka, duk wanda ya karya dokar wannan hukuma, wannan hukuma ta na gurfanar da  shi a kotu kamar yadda ya faru a baya. Don haka wannan ba shi ne karo na farko ba, akwai mutane da su ma sun yi irin wannan, kuma doka ta yi aiki a kan su. Don haka duk wanda ya yi wani abu ko wace siyasa ya ke, za a ɗauki mataki a kan shi, domin duk al’umma zaman doka su ke yi. 
 
“Kuma babu yadda za a yi mu bar wani ya kawo wani abu da zai ɓata tarbiyyar mutane. Don haka dole za ka bar mutane su faɗi abin da su ke so. 
 
“Ba mu hukunta kowa don siyasa. Ka san ba a kawo laifin da mutum ya yi, sai a juya abin zuwa wani manufa na daban. 
 
“Hukumar Tace Finafinai an kafa ta ne don tarbiyyar al’umma. Idan mu ka zuba ido ba mu yi abin da aka ba mu amana ba, mun ci amanar al’ummar Jihar Kano. 
 
“Dalilin da ya sa kenan mu ka tashi tsaye da tabbatar da cewa lallai-lallai sai mun ladabtar da duk wanda ya yi ba daidai ba.
 
“Kuma tun da mu ka zo ba shi ne na farko ba, kuma an hukunta su a kai. Kuma wannan ba shi ne zai zama na ƙarshe ba. 
 
“Wannan hukuma a tsaye ta ke don ganin ta hukunta duk wanda zai karya doka ya zo ya yi wani abu na gaban kan sa domin ya na siyasa ko ya na fakewa da siyasa  ko wani abu, wallahi ba za mu ƙyale shi ba, ba za mu bar wannan abu ba, domin shi ne amanar da Allah Ya ɗora mana, kuma dole mu yi amfani da abin da Allah Ya ɗora mana don mu ga mun sauke wannan nauyin. 
 
“Kuma ko wace gwamnati ta zo ba za ta bar abu cikin rashin tsari ko tarbiyya ba. Don haka ba za mu yarda da ire-iren waɗannan abubuwa na ɓata tarbiyya ba.
 
“Ka ga an ba yarinya wasu irin kaya na rashin tarbiyya, wanda ba zai iya ba ƙanwar sa ko ‘yar sa ba, don me ‘yar wani ko ƙanwar wani? Jihar Kano mu na da tsare-tsare na fim, mu na da tsare na waƙa tun daga rubutu har zuwa fitar da ita, to dole sai ka bi wannan tsari, in kuma haƙura za ka yi da sana’ar ko kuma ya bar ta a Kano.
 
“To abin abin da ya yi ba shi da alaƙa da siyasa, taka doka ya yi kuma doka ta yi aiki a kai, shi ya sa mu ka kai kotu. Don haka idan har abin da ya yi ba hurumi ko kuma ba mu da ta cewa a kai, kotu za ta tabbatar.
 
“Kuma maganar an ƙi yarda a gan shi, ai ba ɗaukar lokaci aka yi ba da aka kama shi shi. Jiya aka kama shi, kuma wannan kotun tafi-da-gidan-ka ce;  ko a ƙofar gidan ka za ta yanke maka hukunci. Don haka ba mu da wani abu da ya wuce mu yi tsari don ganin mun yi abin da za mu tsaftace wannan jiha.
 
“Kuma kowa ya na ganin abin da ya ke faruwa a masana’antar nan. Kuma kada ka manta, ni ma fa ]an masana’antar nan ne. 
 
“Tunda ƙungiyoyi sun kasa, mu ba za mu zuba idanu ba mu na barin abin. Kuma da ma hukuma ta na da doka wadda aka yi ta tun shekarar 2001, don haka ba sabon abu ba ne ko kuma a ce Afakallahu ya ƙirƙiro ko wannan gwamnatin ta ƙirƙiro. 
 
“Mu ba mu da hurumin da za mu bada damar ganin sa, saboda wannan hurumi ne na kotu. 
 
“Kuma yanzu haka akwai abubuwan da ba za mu yi magana ba, saboda kada mu yi wani abu da ya saɓa wa doka da sauran su. 
 
“Yanzu hukuma ta ɗauki matakin  duk wanda zai yi fim a Kano ko za ka kawo kasuwancin fim ɗin ka a Kano wallahi sai ka zo mun tace ka. Yara su na shigowa, musamman mata. 
 
“Dole mu tsaftace waɗannan abubuwan ko ba don komai ba, saboda amanar da Allah Ya ba mu. Allah Ya gani, ga shi nan, da babu abin da ya yi ko waƙa ce aka yi ta wani abu daban ko kuma bai yi ba, da shi ne za a ce siyasa. Amma ga shi ana gani mun ɗauki abin da aka taka dokar hukuma. 
 
“Kuma shi ma ya ɗauki lauya, kuma da lauyan nasa aka yi, da wanda ya je ya gani da mutanen sa wanda su ke ganin su na tare da shi sun je. 
 
“Abu ne aka karanto masa, kuma lauyan sa ya tashi ya yi magana, ba wani ba ne ya sa masa lauyan, shi ya kawo lauyan sa. 
 
“Saboda haka wannan abin mu bari mu ga abin da doka za ta yi. 
 
“Sannan ina ƙara tabbatar wa wannan gidan jarida da duniya baki ɗaya wannan abu ba shi da alaƙa da siyasa. Kuma waƙoƙin da ake tuhumar sa su ne ‘So Na Amana’ da kuma wani kundin waƙoƙi mai suna ‘Hasashe’. 
 
“Ita waƙar ‘So Na Amana’, wata yarinya ce Rakiya Moussa ’yar ƙasar Nijar, da Garzali Miko su ka yi ta. Duk wanda ya kalli wannan waƙa ba zai iya kallo da iyalin sa ba. 
 
“Yanzu abin da aka koma, idan yarinya ta zo sai a ce ta kawo N200,000 a yi mata waƙoƙi, a ba ta wanduna ta sa, shi kenan a harba ta. Wannan kan ta ta na taɓa sana’ar. 
 
“Mu fa ba wai mu zauna kawai mu na tacewa ba, mu fito da hanyar da za mu bunƙasa sana’ar. Bunƙasa sana’a ta na samar da daraja a cikin sana’a ta inda mutane za su riƙa ganin mutunci. 
 
“Saƙo ya na zama mai daraja idan ɗan saƙo ya zama mai daraja. Ya kai da za ka kai saƙo ba ka da daraja, ya za a yi saƙon da ka kai ya yi daraja? 
 
“Shi ya sa Allah Ya aiko da Manzon Allah da saƙo, duk duniya babu wanda ya kai Manzon Allah daraja. Shi ya sa Musulunci ya zama ya na da daraja fiye da kowane addini. Ya za a yi kai ba ka faɗaka ba, kai ka faɗakar da wasu? Yanzu ba ga finafinai ana yi ba. 
 
“Fim na shiga kallo shekaranjiya, fitowa mu ka yi mutane su na kuka, saboda ya taɓa zuciyar su. An yi fim ɗin da ya taɓa rayuwar al’umma. An shirya fim ɗin ne a kan fyaɗe. Mutane su na kallo su na jin daɗi. 
 
“Mu kullum aikin mu yaya za a yi kada a ɓata rayuwar al’umma. Wannan shi ne.”
 
 
 
 

Loading

Previous Post

Jamilu Yakasai ya zama shugaban Arewa bayan zaɓe cikin hargitsi

Next Post

Mai Martaba ya naɗa Adamu Nagudu Sarkin Mawaƙan Borgu

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Adamu Hassan Nagudu

Mai Martaba ya naɗa Adamu Nagudu Sarkin Mawaƙan Borgu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!