AN bayyana Jamilu Ahmad Yakasai a matsayin sabon shugaban Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Arewa (Arewa Film Makers Association of Nigeria, AFMAN), reshen Jihar Kano, bayan wani zaɓe da aka gudanar a cikin ruɗani da tada jijiyar wuya.
Da ma dai shi wannan zaɓe, wanda aka gudanar a yau ranar 17 ga Agusta, 2019, ya zo ne cikin wata kwantacciyar rigima da ta daɗe ta na cin wuta ta ƙarƙashin ƙasa, domin kuwa an shirya gudanar da shi ne sama da shekara biyu da su ka gabata, amma dalilin shigo da siyasa cikin ƙungiyar ya sa zaɓen ya ƙi yiwuwa.
Sai da ta kai har hukumar tsaro ta farin kaya ta shiga cikin lamarin, ta dakatar da shirya zaɓen ana dab da za a gudanar da shi. Daga baya gwamnatin Jihar Kano ta bada damar a yi zaɓen tare da cewar su jira gwamnati ta ba su tallafin kuɗin da za su gudanar da zaɓen, amma har aka cinye zangon mulkin ba a su samu tallafin ba.
A yanzu da su ka sake yin wani shirin sai kawai su ka shirya zaɓen ba tare da sun jira abin da gwamnati za ta ba su ba, kawai su ka shirya zaɓen tare da sanar da hukumomin tsaro domin ba su kariya.
Tun kafin ranar, an yi wani irin yaƙin neman zaɓe mai cike da hayaniya da ruɗani a tsakanin ‘yan takarar da su ka nemi shugabancin ƙungiyar su uku, wato Jamilu Ahmad Yakasai, Abdallah Tahir Al-Kinanah, da Rasheeda Adamu Abdullahi.
Kowannen su ya riƙa nuna ƙarfin gwiwar sa a kan shi ne zai yi nasara, don haka sauran duk su na raka shi ne. Da irin wannan cin alwashin ‘yan takarar su ka shiga filin zaɓen. Hakan ya sa aka yi ta samun musayar magana a tsakanin magoya bayan su.
Zaɓen dai za a iya cewa ya kafa tarihi a masana’antar finafinai ta Kannywood, domin kuwa ba a taɓa yin zaɓen da aka ba shi muhimmanci kamar sa ba.
Idan ka je filin zaɓen sai ka zata zaɓen gwamna ko na ɗan majalisa ne za a yi, ganin yadda aka rinƙa sayen ƙuri’un ‘yan ƙungiya; ana gewayewa da su baya ana ba su ƙulli na ɗan abin sakawa a aljihu.
Hakan ne farkon abin da ya so wargaza zaɓen kafin daga baya a shawo kan lamarin.
A haka aka shafe tsawon yini guda ana tantancewa tare da gudanar da zaɓen.
Bayan an kammala, sai kwamitin shirya zaɓen ya bada sanarwar cewa Jamilu Ahmad Yakasai ne ya yi nasara da ƙuri’u 37, sai Abdallah Tahir Al-Kinanah da ƙuri’u 32, yayin da ita kuma Rasheeda Adamu ta zo ta uku da ƙuri’u 28.
Sai dai wannan sakamakon ya zo wa sauran ‘yan takarar da ba-zata, don haka su ka ce sam ba su amince da shi ba, kuma ba za su rattaba hannu a takardar sakamakon ba, domin bai cika ƙa’idar dokar da aka tsara ta gudanar da zaɓen ba.
Al-Kinanah shi ne ya fara nuna rashin amincewar sa, inda ya ce an hana magoya bayan sa da dama su yi zaɓen, sannan an shigo da wasu da ba sa cikin masu kaɗa ƙuri’a da sunan “dattawan ƙungiya” sun gudanar da zaɓen duk da yake ba sa cikin lissafin masu zaɓen kamar yadda ya ke a rubuce.

Ya ƙara da cewa, “A ƙa’idar zaɓen, adadin mutanen da za su yi zaɓen su 150 ne amma sai mutane 94 su ka yi zaɓen, aka ce wai takardar kaɗa ƙuri’a ta ƙare. To ina aka kai sama da hamsin da aka hana magoya bayan mu su yi zaɓen? Don haka mu na ƙalubalantar wannan zaɓen, kuma za mu ci gaba da ƙalubalantar sa har zuwa gaban kotu matuƙar ba a ɗauki matakin da ya dace ba.”
Ita ma Rasheeda ta bayyana zaɓen a matsayin aikin banza, inda ta zargi wani jami’in gwamnati da ya shigo wajen zaven da shirya maguɗi.
Ta ce ba za ta yarda da irin zaluncin da aka yi masu ba.
Sai dai ta yi kira ga magoya bayan ta da su kwantar da hankalin su a kan lamarin.
Duk da cewar akwai jami’an tsaro a wajen, amma bayyana sakamakon zaɓen ya so ya jefa wajen cikin tashin hankali, don haka ma daga faɗar sakamakon ‘yan kwamitin su ka yi sauri su ka sulale daga wajen, su ka bar sauran mutane su na surutan su.
Mutanen da aka bayyana a matsayin waɗanda su ka ci zaɓen su ne:
* Jamilu Ahmad Yakasai – Shugaba
* Lawan Ahmad – Mataimaki
* Sadiq Salisu Hussaini – Sakatare
* TY Shaban – Mataimakin Sakatare
* Ahmad Amaryawa – Ma’aji
* Abubakar GBoy – Sakataren Yaɗa Labarai
* Rabi’u Mustapha The King – Sakataren Tsare-tsare
* Habib Abubakar Torore – Mai Bincike na 1
* Suwaiba Abubakar – Mai Bincike ta 2
* Hannatu Bashir – Sakatariyar Kuɗi
* Halima Yusuf Atete – Jami’ar Walwala