LITTAFI: Daƙiƙa Talatin
MARUBUCI: Ado Ahmad Gidan Dabino, MON
KAMFANI: Gidan Dabino Publishers, Kano
SHEKARA: 2015
SHAFUKA: 115
FARASHI: N300
ISBN: 978-8082-15-7
‘Daƙiƙa Talatin’ wasan kwaikwayo ne wanda Malam Ado Ahmad Gidan Dabino ya rubuta, inda ya bada labarin wata matashiyar gurguwa, Zannira, da ta kafa ƙungiya don tallafa wa naƙasassu da masu ƙaramin ƙarfi. Ta na gab da cimma nasara sai ƙaddarar rasa miji ta afka mata, sa’anni kaɗan bayan an ɗaura auren su da Yassar.
Da shawarwarin Aminu, abokin Yassar, da Amina ƙawar ta kuma budurwar Aminu, ta ci gaba daga inda ta tsaya har ta cimma nasara.
Sai dai cikin da ta samu ya haifar da zargi daga jama’ar gari da ƙawar ta Amina a kan Aminu ne ya yi cikin.
Wannan ta sa dole aka shiga kotu, domin waliyyan Yassar sun ce ba za su karɓi cikin ba a matsayin na ɗan su.
WARWARAR JIGO
• Marubucin ya nuna zaman banza saboda naƙasa ba shi da fa’ida, kuma Allah na taimakon duk naƙasasshen da ya tashi tsaye, babban misali daga Zannira gurguwa.
• Rungumar ƙaddara da karɓar shawara daga ma’abota hankali abu ne mai kyau, misalin yadda Zannira ta karɓi shawarar su Aminu.
• An nuna illar amfani da waya lokacin da ake tuƙi, domin haka ne ya yi sanadiyyar Alh. Bashir ya kaɗe ango Yassar.
• Mugun nufi ba ya sa a samu abin da ake so, misali daga abin da Samira ta yi wa Zannira saboda kishi.
ZUBI DA TSARI
An zuba wasan ne a kan kashi-kashi har guda takwas. Kashi na 2 zuwa na 8 su na ƙunshe da fitowa daga 2 zuwa 10, in ka ɗauke kashi na 6 mai shiga 19. Akwai gabatarwa a kowace shiga har 50.
A tsarin wasan, ana kawo sunan kowane ɗan wasa da abin da ya faɗa a gaban sunan, da kuma aikin sa cikin rubutu tafiyar tsutsa.
SALO DA SARRAFA HARSHE
Salon labarin ya ƙayatar, domin salo ne na ban-tausayi da raha. An nuna gwanintar sarrafa harshe ta hanyar amfani da karin magana, habaici da sauran su.
TAURARI
Zannira da Yassar su ne manyan taurarin wasan, duk da Yassar ya mutu kafin wasan ya yi nisa. Ƙananan taurarin sun taimaka wa babbar tauraruwar labarin don kada ta yi ƙasa a gwiwa, wato Amina da Aminu.
ƘA’IDOJIN RUBUTU
Ƙa’idojin rubutu sai sambarka, domin an kiyaye su yadda ya kamata, face ‘yan kurakuran da ba a rasa ba.
ABUBUWAN YABAWA
– Fito da littafin ‘Daƙiƙa Talatin’ da Malam Ado ya yi a ’yan shekarun nan abin a jinjina masa ne, musamman da ake fama da ƙarancin littattafan wasan kwaikwayo a wannan lokacin.
– Littafin ya samu kyakkyawan bugu fiye da sauran littattafai takwarorin sa da aka yi a baya, tun daga kan tsarin bango mai santsi zuwa fararen takardu da kuma uwa-uba shi kan sa labarin. Abin ya ƙayatar matuƙa.
KURAKURAI
• Shafi na 7: Samira ta buge Zannira da mota, ba ta tsaya ba ta gudu, amma Ɗanladi har ya haddace lambar motar, kamar abin da ya samu Zannira bai dame shi ba.
• Anya kuwa Zannira za ta iya gane na cikin motar da ta kaɗe ta mace ce ko namiji? Domin ta ce mace ce a shafi na 8. A can kuma shafi na 12 Samira ta ce ta yi wancakali da keken guragun, har sai da ya yi ƙuli-ƙulin kubura. Shin ta haka yaya za a yi Zannira ta gane mace ce a motar ko namiji ta na halin ɗimauta?
• Shafi na 20: Yassar ya ce, “…ke ma kin san haka sai dai ki ƙi sani da gangan:, maimakon “…ke ma kin san haka sai dai ki take da gangan”.
• Shafi na 31-32: Taken ƙungiyar Zannira, sai aka rubuta “Babu Nakassahe sai Kasasshe” madadin “Babu naƙasasshe sai kasasshe”.
• Yaya aka yi maganar cikin Zannira ta bayyana a shafi na 69? Marubucin ya nuna cewa Zannira ba ta yi niyyar faɗa wa kowa ba a hirar su da Amina a shafi na 67-68.
• Shafi na 96-97 A kotu da ma mutum ne ke yin rantsuwar zai faɗi gaskiya ko ɗanwanka ne ke rantsar da shi?
Madalla da ƙoƙari Malam Ado.
![]()







