JARUMIN Kannywood, Malam Ibrahim Shu’aibu (wanda aka fi sani da suna Ibrahim 2-Effects) ya bayyana darussan da ya koya a aure a daidai ranar da suka cika shekara goma da aure da matar sa Jamila Yahaya.
A yau Juma’a ne ma’auratan su ka cika waɗannan shekaru goma.
Cikin murna da farin ciki, jarumin, wanda ya ke ɗaya daga cikin yaran kamfanin 2-Efects Empire, ya yi wa Allah godiya a tattaunawar sa da mujallar Fim.
Ya ce, “Alhamdu lillah, alhamdu lillah, alhamdu lillah. Ina matuƙar farin ciki da godiya ga Allah (s.w.t.) da ya nuna mana wannan rana ta cika shekara goma da yin aure.
“Haƙiƙa wannan abin farin ciki ne a tsakanin mu, duba da cewa shekarun kamar wasa har sun kai goma.
“Alhamdu lillah. Ina ƙara yi wa Allah godiya, a tsawon waɗannan shekarun har Allah ya azurta mu da ‘ya’ya huɗu, namiji ɗaya, mata uku. Namijin sunan sa Muhammad, sai Khadija, Hauwa’u da A’isha.
“Idan ban manta ba a shekarar 2014 a watan Afrilu, wannan mujalla ta Fim ta wallafa labarin auren mu da aka yi, wanda yau shekaru goma kenan. A wannan rana mu na matuƙar farin ciki sosai da sosai a wannan rana.
“Bayan nan abin da zan ce, duk wanda ya san gidan aure, ya san menene a cikin shi. Shi ma kusan kamar zaman waje ne kafin auren. Akwai ƙalubale shi ma, musamman ga shi an kwashe shekaru da dama, duk haƙuri mu ke da juna.
“Idan ta yi mani ba daidai ba, ta na ƙoƙarin ba ni haƙuri ko da na ji zafin abin da tai min ɗin, sakamakon zuwa ta ba ni haƙuri, ni kuma sai in ji san yi a rai na, in huce. Daga nan sai in haƙura kamar yadda ta buƙata.
“Haka zalika, ni ma idan na yi mata abin da ba ta ji daɗi ba, har in ta faɗa min ko ba ta faɗa min ba, idan na ga yanayin ta ya canza, sai in same ta in tambaye ta menene ya faru? Da ta faɗa min na ga laifin da na yi mata, sai in ba ta haƙuri, shi kenan komai ya wuce.
“Haka zaman namu ke kasancewa har zuwa wannan lokaci.”
Ibrahim ya ba sauran ma’aurata shawarar cewa su cigaba da zama da junan su lafiya da tausayi ga junan su.
Ya ce: “Babu ɗaukar maganar magulmata, don akwai waɗanda idan sun ga ku na zaune lafiya a ɗakin ku, ba su ƙaunar hakan. Duk yadda za su yi su ga sun lalata zaman naku, shi za su yi ta ƙoƙarin yi.
“Saboda haka mu kula baki ɗayan mu. Allah ya ƙara mana haƙuri da juriyar zama da juna.
“Mujallar Fim mu na miƙa godiya ta musamman a gare ku. Allah ya saka da alkhairi. Na gode.”

![]()







