ƘUNGIYAR Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ta bayyana cewa ta kaɗu game da murabus ɗin da Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya yi a yau.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Habibu Barde Muhammad, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata takardar sanarwa ga manema labarai wadda Kakakin ƙungiyar na ƙasa, Malam Al-Amin Ciroma, ya fitar a yau.
A takardar, wadda mujallar Fim ta samu kwafe, MOPPAN ta ce, “Sheikh Daurawa ya aje muƙamin nasa ne bisa dalilin rashin ƙwarin gwiwa daga ɓangaren gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf.”
Ƙungiyar ta ce ta na sane da kuskuren da Hisbah ta yi wanda gwamna ya nuna damuwar sa a kai. Amma duk da haka ta ce akwai buƙatar samun haɗin kai da daidaiton da hukumar don amfanin al’umma.
MOPPAN ta yi kiran gaggawa ga Sheikh Daurawa da ya sake nazari kan murabus ɗin da ya yi, sannan ya ci gaba da aikin sa a matsayin shugaban hukumar ta Hisbah.
Haka kuma ta jadadda muhimmacin Sheikh Daurawa a matsayin malamin Musulunci, kuma ta ƙarfafa masa gwiwa da kada ya juya daga alhakin shiryuwar ɗabi’un al’umma.
“Ƙungiyar na sane da girman lamarin tare da kira da a fahimci juna tsakanin Sheikh Daurawa da gwamnatin Kano. Ƙungiyar ta aminta kan cewa tattaunawa da fahimtar juna na da matuƙar muhimmanci wurin daidaita dukkan ɓangarorin,” inji ta.
Haka kuma MOPPAN ta ce, “Lallai Hisbah na taɓukawa a ƙarƙashin jagorancin Sheikh Daurawa saboda an shaida yadda ake samun raguwar baɗala a cikin al’umma, musamman masu shirin fim, a dalilin jagorancin da ya ke yi wa Hisbah.”
A ƙarshe, MOPPAN ta bayar da shawarwari masu ƙudiri a tsakanin ɓangarorin da abin ya shafa da jaddada buƙatar ci gaba da haɗin gwiwa wajen inganta rayuwar al’umma.
![]()







