• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Abin da ya sa mu ka soke lasisin harkar fim na furodusa A’isha Amart – Hukuma

by MUKHTAR YAKUBU
March 1, 2024
in Labarai
0
Abin da ya sa mu ka soke lasisin harkar fim na furodusa A’isha Amart – Hukuma

Hajiya Aisha Amart da Alhaji Abba El-Mustapha

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Tace Finafinai ta Jihar Kano ta bayyana dalilin ta na soke lasisin gudanar da harkar fim na babbar furodusa a Kannywood , A’isha Amart, wanda hukumar ta ba ta.

Kwanan nan dai labari ya bazu cewa hukumar ta dakatar da furodusar daga gudanar da harkar fim, har wasu a masana’antar su na ganin an take mata haƙƙi ne.

Hajiya A’isha dai babbar mai shirya finafinai ce wadda kan saki fim ɗin ta a YouTube, sai ta sayar da fostar shirin ga masu gidajen kallo a Jihar Kano da ‘yan dawunlodin masu sauko da shi su na saka wa mutane a waya bisa wani guntun farashi.

Majiya ta faɗa wa mujallar Fim cewa babu wani furodusa da ya fi ta ƙarfi a wannan fagen na hulɗa da masu gidajen kallo.

Majiyar ta ce kwanan baya sai aka samu saɓani tsakanin furodusar da masu gidajen kallo da dama da su ke sayar da fim ɗin ta ba tare da sun biya kuɗin haƙƙin nuna fim ɗin nata ba, wanda hakan laifi ne.

Ita kuma sai ta riƙa yawo da ‘yan sanda ta na bin irin waɗannan masu karya dokar haƙƙin mallakar ta na kama su.

Da yawa a Kannywood sun yi mamakin jin cewa hukumar tace fim ta soke lasisin furodusar, ana cewa rashin jituwa ne ya shiga tsakanin ta da Shugaban hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha.

To amma Jami’in Yaɗa Labarai na hukumar, Malam Abdullahi Sani Sulaiman, ya faɗa mujallar Fim cewa an ɗauki wannan matakin ne sakamakon laifin karya doka da kuma rashin ladabi da Hajiya Aisha ta aikata.

Ya ce: “Gaskiya ne Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta soke lasisin ta. Kuma hakan ya biyo bayan wasu abubuwan da ta ke aikatawa da ya saɓa wa dokokin hukumar.

‘Domin ta na bin ƙananan hukumomi ta na kamen masu tura finafinai a waya tare da cin su tara wanda tun tuni da aka ga ƙorafin ya yi yawa aka kira ta aka zauna da ita cikin sirri. Sannan daga baya aka kira su masu tura finafinai, duk a ƙoƙarin yadda za a yi a samu daidaito ta yadda su za su rinƙa cika ƙa’idar tura finafinai ta hanyar sayen fim daga su masu haƙƙin mallakar sa da sauran dokokin su don a haɗu a taimaka wa ita masana’antar.

“Sannan ita kuma ya zama ba za ta ci gaba da yin kamen da ta ke yi ba sai da sanin Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano da kuma hukumar ‘yan sanda.

“Hakan ya sa har aka fitar da tsari na fitar da fim kuma aka ce daga lokacin babu wani mutum shi kaɗai da zai yi gaban kan sa ya je ya kama masu tura finafinai a waya sai da sanin Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano da kuma wakilcin jama’an tsaro.

“To ita sai ta karya wannan tsarin, ta je Rano, ta je Minjibir ta yi, kuma su masu sana’ar su ka sanar da hukuma cewa ga ta ta zo ta na ci gaba da yi.

“Wannan ya sa aka kirawo ta amma sai ta ƙi zuwa sai da ta yi wajen kwana uku da sanar da ita. Duk da haka aka ba ta dama aka karɓi uzirin ta. Amma a lokacin ana cikin ganawa da darakta mai kula da ɓangaren fim sai ta fusata ta ke zagin daraktan.

“Wannan abin bai yi wa kowa daɗi ba a gidan saboda yadda ta fito ta na zagin babba a gidan kuma gaba da gaba.

“To, waɗannan abubuwan su ne su ka dagula lamarin, tunda ga ka ga babu mutunci, ga shi ta yi laifi na karya doka kuma ta zo ta na zagi ta na nuna babu wani da ya isa ya faɗa mata yadda za ta yi, kawai za ta yi abin da ta ga dama ne.

“Wannan ya sa Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta soke lasisin nata.

“Don haka a yanzu mun soke lasisin ta, ba za ta ci gaba da harkar kasuwancin fim ba a Jihar Kano.”

Wata majiya ta faɗa wa mujallar Fim cewa Hajiya A’isha ta bi duk hanyoyin da za ta bi domin a sa Abba El-Mustapha ya janye matakin da ya ɗauka a kan ta, ta hanyar ganin manyan mutane a Kano, amma abin ya ci tura.

Loading

Tags: Abba El-MustaphaAisha Amartgidajen kalloHukumar Tace Finafimai ta Jihar Kanolasisi
Previous Post

Ran Juma’a ‘yan Kannywood za su yi saukar Alƙur’ani don Zainab Booth da ‘yan fim magabata

Next Post

Shawarar ‘yan Kannywood ga Sheikh Daurawa: Kada ka juya baya ga aikin taimakon Musulunci

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Shawarar ‘yan Kannywood ga Sheikh Daurawa: Kada ka juya baya ga aikin taimakon Musulunci

Shawarar 'yan Kannywood ga Sheikh Daurawa: Kada ka juya baya ga aikin taimakon Musulunci

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!