An ci gaba da gabatar da jawabai tare da bayar da horo a taron KILAF AWARD 24 a rana ta huɗu ta gudanar da taron, wato alhamis 28 ga Nuwamba, 2024 a babban ɗakin taro na Tsangayar Koyar da Aikin Jarida dake Sabuwar Jami’ar Bayero dake Kano.
A farkon buɗe taron da misalin ƙarfe 9 na safe, kwararre kuma masani a kan harkar fim, Yomi Olugbod, ya gabatar da bita akan aikin manajan shirya fim, wato “Production Manager” inda ya yi dogon bayani a game da alaƙar manajan shirya fim da furodusa, darakta da kuma jaruman fim.
Haka nan ya bada misalai da dama akan tasirin manajan shirya fim da kuma ingancin fim da kuma rashin ingancin sa.
Nasiru B Muhammad, shi ne ya yi sharhi tare da ƙarin bayani bayan Mista Yomi Olugbod ya kammala jawabin sa tare ƙarfafa wa mahalarta kan su mayar da hankali a game da abin da suke sauraro, yadda za su ci moriyar darasin da ake koyar da su.
Duk dai a wannan rana shi ma Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa, Dakta Hussaini Shu’aibu, ya samu halartar wajen taron tare da gabatar da dan takaitaccen jawabi tare da nuna farin cikin sa da ya samu halartar wajen duk da ya zo a makare saboda wani aiki da ya taso masa a Legas, amma dai duk da haka ya yi ƙoƙari ya samu zuwa tare da rakiyar na Ofishin shiyyar Arewa maso yamma.

Ya yi fatan alheri tare da ƙarfafa gwiwa ga taron, inda ya ce yana da kyakkyawar fata a kan bunƙasar masana’antar finafinai ta Nijeriya, yadda shekaru masu zuwa za a ci gajiyar ta fiye da wannan lokacin.
Bayan ya kammala jawabin sa ne aka tafi hutun sallah tare da cin abinci, wanda shi ma wani ɓangare ne mai muhimmanci a cikin tsarin taron. Domin kuwa an samar da abincin gargajiyar Afirika wanda ya dace da mutanen Afirika yadda duk inda mutum ya zo daga ƙasashen Afirika zai samu kalar abincin gargajiyar da yake buƙata.
Hakan ya bayar da dama ga sanin abincin gargajiyar kala kala da ake amfani da su a ƙasashen Afirika.
An ci gaba da taron da misalin ƙarfe uku na rana tare da gabatar da Charlas Okwuowubu don ya gabatar da nasa jawabi.
Ya yi dogon bayani a game matakin tace fim bayan an kammala aikin sa wato ‘Editing Process’.
Haka nan ya yi bayani a kan yadda mai ɗaukar hoto zai yi amfani da fitila da kuma kalar hasken da ya kamata ya yi amfani da shi a kowanne sin da zai ɗauka, da yin amfani da waje da kuma lokacin da ya kamata.
An kammala zaman taron na wannan rana da kallon wasu gajerun finafinai ne guda uku– ɗaya daga Nijeriya mai suna Tarnaki, sai Fatimmah Zarah daga ƙasar Marocco da LiLa daga ƙasar Ruwanda.
Daraktocin finafinan dai sun sha tambayoyi daga wajen mahalarta taron, har zuwa lokacin da aka rufe taron da misalin ƙarfe shida na yamma. Za kuma a ci gaba da taron a gobe Juma’a da za ta kasance rana ta biyar a jadawalin taron.