Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta ɗauki matsaya akan Ƙungiyar Daraktocin da za ta yi mu’amala da ita a hukumce wajen gudanar da aikin ta.
Shugaban Hukumar ne Abba El-Mustapha ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi a taron rantsar da shugabannin Ƙungiyar Daraktoci, ‘Professional Film Directors Association of Nigeria,’ wato PROFDA wanda aka gudanar a ƙarshen mako a Tahir Guest Palace.
Abba El-Mustapha ya ce “Daga yanzu ba zan yi duk wata ƙungiya ta daraktoci ba idan har ba su haɗa kan su ba, domin na samu kaina a cikin wani yanayin da idan na zauna da wata ƙungiya ta daraktoci, sai wasu ma su zo su ce ai su ne shugabannin ƙungiyar daraktocin, bayan nan ma sai wasu ma su ƙara zuwa, to sai na zama kamar an mayar da wani abu na daban.
“To amma a yanzu an haɗu an mayar da ƙungiyar ta zama PROFDA ita ce za ta rinƙa magana da yawun daraktoci da murya ɗaya.
“Wannan ya sa na fi kowa murna, musamman ma da na ga an zaɓo jajirtacce wanda ni tun sani na da shi kawai shi ya Kannywood za ta je inda ya kamata ta je a mafarki da muke yawan yi. Don haka muna kira ga Nasiru B Muhammad da ya sani akalar harkar fim a yanzu tana hannun sa.
“Don haka mu ta ɓangaren hukuma duk abin da ya zo za mu yi iya ƙoƙarin mu mu ga an samar wa da wannan ƙungiyar ci gaba, musamman ɓangare na samun horo, don haka muna son mu shirya wani taron bita wanda za mu gayyato ƙwararru ko daga ina ne a duniya su zo su fara horas da daraktocin mu.
“Don haka ba za mu yi wani aiki ba sai tare da PROFDA don haka duk wani wanda yake tunanin ma ko ya bijirewa PROFDA ya dawo a haɗa m kai da shi, domin idan ba ta PROFDA ya zo ba, mu ba mu ma san shi ba, kuma ba za mu yi aiki da shi ba, don haka da PROFDA kaɗai za mu yi aiki a matsayin Ƙungiyar Daraktoci,” inji Abba El-Mustapha.
![]()







