‘YAR darakta a Kannywood, Marigayi Malam Nura Mustapha Waye za ta yi aure ranar Lahadi, 1 ga Disamba, 2024.
Za a ɗaura auren Hauwa’u Nura Mustapha Waye (Walima) da sahibin ta Musa Abdullahi (Musa Values), da ƙarfe 11:00 na safe a masallacin Juma’a na Malam Musa Bakin Ruwa da ke Goron Dutse, Jihar Kano.
Abokan sana’ar mahaifin ta ne su ka ba da sanarwar ɗaurin auren.
Shahararren mawaƙin siyasa a Kannywood, Alhaji Dauda Adamu Abdullahi (Rarara) ya bada gudummawar kayan abinci da kuɗi N500,000, domin yin hidimar bikin.

Idan ba ku manta ba, Marigayi Nura Mustapha Waye, shi ne darakta kuma marubucin fim ɗin jarumi Lawan Ahmad mai suna ‘Izzar So’.

Nura ya rasu ne a safiyar Lahadi, 3 ga Yuli, 2022 da misalin ƙarfe 8:00 na safe a wani asibiti a Kano.