FITACCIYAR jaruma kuma furodusa Ruƙayya Umar Santa (Dawayya) ta bayyana cewa ita ganau ce ba jiyau ba game da yadda tsaro ya samu a Jihar Katsina.
Dawayya ta yi wannan bayanin a hirar ta da mujallar Fim ne bayan ta saki wata sabuwar waƙa da ta shirya wa Gwamnan Jihar Katsina mai taken ”Katsina Tsaro Ya Samu”.
Waƙa ce wadda gamayyar mawaƙan Hausa su ka yi.
Mawaƙan sun haɗa da Nazifi Asnanic, Ibrahim Ibrahim, Maryam Saleh (Fantimoti), da wasu waɗanda duniya ba ta san su ba sosai.
Jaruman da su ka fito a bidiyon waƙar sun haɗa da Dawayya, Hannatu Bashir, Bilkisu Abdullahi, Nazifi Asnanic, Ibrahim Ibrahim, Jamilu Ibrahim, Lawan Ahmad, da sauran su.
Aminu S. Bono ne ya bada umarni a ɗaukar bidiyon waƙar.
An ɗauki bidiyon waƙar a Katsina don nuna irin ƙoƙarin da Masari ya yi wajen tabbatar da tsaro a jihar.
Kamfanin jarumar mai suna ‘Dawayya Movies’ shi ne ya ɗauki nauyin shirya ta.
A bayanin da ta yi wa mujallar Fim kan dalilin yin waƙar, Dawayya ta ce, “Abin da ya sa na yi waƙar ‘Tsaro Ya Samu a Jihar Katsina’ shi ne saboda tsaron ya samu.
“Na yi yawo a ƙananan hukumomi 34 da ake da su a Jihar Katsina a lokacin da ake fama da matsalar tsaro, na je har sansanin ‘yan gudun hijira na ga yadda su ke rayuwa.
“Bayan gwamna ya yi sasanci da Fulanin daji, na koma na ga yadda mutane su ka koma gidajen su, su na ci gaba da aiwatar da ayyukan su na yau da kullum.

‘Kuma da kan su sun tabbatar min da cewa wannan sasancin ya yi silar samuwar tsaro a Katsina.
“Sannan abubuwan da mu ka gani a zahiri su ne mu ka faɗa wa mutane a waƙar, saboda idan mu ka ce sai mun faɗi duk abin da ya faru, aƙalla waƙar za ta iya ɗaukar awa biyu ana yin ta.
“Bugu da ƙari, tun da na tashi na yi wayo, na ga ana mulki a jihohi daban-daban.
“A matsayi na na ‘yar wasan kwaikwayo na yi harkokin siyasa kala-kala, amma abin da mutane ke faɗa a tarihin Jihar Katsina ba a taɓa gwamnan da ya tallafi al’umma ya rungumi matsalolin su ba, musamman na tsaro, irin Aminu Bello Masari.”
Ita dai wannan waƙa, Dawayya ta sake ta ne a shafin ta na YouTube.