ALLAH ya yi wa jarumar Kannywood Hajiya Binta Miko Yakasai rasuwa a safiyar yau a Kano.
Shekarun ta 54.
Hajiya Binta ta rasu a gidan iyayen ta da ke unguwar Yakasai, kwana biyar bayan an sallamo ta daga asibiti inda ta kwanta.
Ta rasu sakamakon sankarar ƙonewar jini wadda ta daɗe tana fama da ita, wanda wannan larura ta sa aka riƙa canza mata jini a duk bayan mako biyu.
Ana gobe za ta rasu, ciwon nata ya tashi har ana ganin kamar ba za ta kai safe ba. Washegari ana shirin mayar da ita asibiti, wajen ƙarfe 10 ta ce ga garin ku.
Idan kun tuna, a watannin baya mujallar Fim ta ba da labarin rashin lafiyar da ke damun daɗaɗɗiyar jarumar, tare da bayanin yadda Dauda Rarara, Ali Nuhu da wasu ‘yan fim suka ba ta gudunmawar tallafi domin ta je asibiti a duba ta.
Yayin da Rarara ya bayar da tallafin N150,000 ta hannun Shugabar Ƙungiyar Tsofaffin Jaruman Kannywood Mata Masu Aure (KAHOWA), wato Hajiya Sakna Gadaz Abdullahi, Ali Nuhu, wanda shi ne Manajan Daraktan Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC), ya ba da gudunmawar N100,000.
Kafin wannan agajin, sai da ‘yan fim da suke cikin guruf na Kannywood Vanguard bisa jagorancin Nasiru Gwangwazo suka haɗa mata N55,000 aka kai mata domin taimakawa a game da rashin lafiyar tata.
Marigayiyar ta taɓa kwanciya a Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammed da ke Kano, a ɓangaren bayar da agajin gaggawa.
Ashe ciwon ta ba na tashi ba ne.
Ta rasu ta bar ‘ya’ya uku – ɗaya namiji, biyu mata – da jikoki bakwai.
Iyayen ta sun jima da rasuwa.
Ɗaya daga cikin ƙawayen ta, Hajiya Halima Adam Yahaya, ta faɗa wa wakilin mu cewa, “Wannan rasuwa ta Hajiya Binta ta taɓa ni sosai. Na kaɗu matuƙa.
“Tun cikin dare yaran ta sun kira ni sun sanar da ni halin da take ciki, na ce su daina yi mata kuka, su dinga yi mata addu’a. Da safe, ina shirin tafiya gidan su domin mu kai ta asibiti sai yaran suka kira ni suka ce mani ai ta rasu.”

Hajiya Binta dai tsohuwar jaruma ce tun a farkon kafa Kannywood.
Kafin rasuwar ta, ma’aikaciyar jinya ce a asibitin Unguwa Uku da ke ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Tarauni cikin birnin Kano.
Allah ya rahamshe ta, ya sa mutuwar hutu ce.