• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, October 11, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Da ina da iko, da na ba Abba El-Mustapha digirin digirgir – Farfesa Abdalla

by ALI KANO
February 19, 2025
in Labarai
0
Da ina da iko, da na ba Abba El-Mustapha digirin digirgir – Farfesa Abdalla

Abba El-Mustapha ya rusuna yana gode wa Farfesa Abdalla bayan ya kira shi 'Dakta'

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

TSOHON Mataimakin Shugaba (wato Vice-Chancellor) na Buɗaɗɗiyar Jami’ar Nijeriya (NOUN), Farfesa Abdalla Uba Adamu, ya bayyana cewa da yana da hali, da ya ba jarumin Kannywood, Abba El-Mustapha, digirin digirgir.

Farfesa Abdalla ya faɗi haka ne cikin wata sanarwa da aka fitar a yau domin yin ƙarin bayani kan jinjinawar da ya yi wa El-Mustapha, wanda shi ne Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Ɗabi’i ta Jihar Kano, a wurin taron karrama tsofaffin ‘yan fim da ƙungiyar Kannywood Family ta shirya a Kano a shekaranjiya Litinin.

A taron bikin karramawar, lokacin da aka kira shi ya ba shugaban hukumar garkuwar karramawar sa, sai mashahurin malamin ya kira shi da ‘Dakta Abba El-Mustapha’.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa bayan taron, an ga buƙatar a yi ƙarin bayani ganin cewa Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta wallafa wani bidiyo a soshiyal midiya inda ta ambato El-Mustapha yana faɗin cewa Farfesa Abdalla ya jaddada masa da digirin digirgir.

Shi kuwa a ɓangaren sa, malamin jami’ar ya kafa hujja ne da yawan ayyukan da El-Mustapha ya yi a Kannywood da kuma tasirin su a cikin al’ummar Jihar Kano.

Hagu zuwa dama: Abba El-Mustapha yana karɓar kambin karramawar sa daga hannun Farfesa Abdalla Uba Adamu a bikin Legendary Awards da Kannywood Family suka shirya a Kano a ranar Litinin, 17 ga Fabrairu, 2025. (Hoto: Sadamcy)

A ƙarin bayanin, Farfesan ya nuna cewa ba fa digiri ya ce ya ba Abba ba, don kada a lanƙwasa gajeren jawabin da ya yi a taron da wata manufa daban.

Ya ce, “Ni ba ni da ikon da zan ba wa kowa digiri, wannan aikin Majalisar Dattijai ne ta jami’io’i. Amma na san a waɗansu ƙasashen a Turai akan gayyaci mutum ya gabatar da ayyukan sa, watau rubuce-rubuce, ko kuma waɗansu ayyukan basira, a ɗora su a bisa ma’aunin cancanta, a kira shi a ce ya kare.

“Idan ya yi haka, aka gamsu, to ana ba shi doctorate na yaba wa basirar sa.

“To ni manazarci ne fiye da shekaru 25 a masana’antar Kannywood, kuma a kan ido na Abba El-Mustapha ya zama gwarzon finafinai.

“To idan da za a ba ni dama in yi masa jarrabawa, tabbas zan yi masa kuma in ba shi doctorate saboda yawa, inganci da kuma muhimmancin finafinan da ya yi alaƙa da su.

“Saboda haka ne ma nake kiran sa da ‘Dr’ Abba El-Mustapha.

“Sannan kuma ya taka rawar gani a yanzu wajen kawo gyara a masana’antar nishaɗi a Kano ta yadda yanzu an fara gane inda aka nufa. Wannan ma abin yabo ne.”

Shi dai Abdalla Uba Adamu, Farfesa ne a kan tuddan nazari biyu, wato Sashen Kimiyyar Ilimi (Science Education) da nazarin Yaɗa Labarai da Al’adu (Media and Cultural Studies).

Ya koyar a jami’o’i a cikin da wajen Nijeriya, wato har a Amurka da wasu ƙasashen nahiyar Turai.

A yanzu yana sahu na gaba, ko ma a ce masa liman, a fagen nazarin harkar finafinan Hausa.

Loading

Tags: Abba El-Mustaphadigirin digirgirFarfesa Abdalla Uba Adamukarramawa
Previous Post

Jarumar Kannywood Binta Miko Yakasai ta kwanta dama

Next Post

Souleymane Cissé, baban harkar fim a Afrika, ya rasu yana da shekaru 84

Related Posts

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu

October 6, 2026
Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba
Labarai

Za a ƙaddamar da reshen Kaduna na KAFIGAN ranar Asabar

October 1, 2026
Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu
Siyasa

Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu

September 30, 2026
Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa
Siyasa

Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa

September 30, 2026
Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa
Siyasa

Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa

September 29, 2026
Next Post
Souleymane Cissé, baban harkar fim a Afrika, ya rasu yana da shekaru 84

Souleymane Cissé, baban harkar fim a Afrika, ya rasu yana da shekaru 84

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!