• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 15, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Souleymane Cissé, baban harkar fim a Afrika, ya rasu yana da shekaru 84

Ya rasu ana gobe zai tafi bikin finafinai na FESPACO a Wagadugu

by IRO MAMMAN
February 20, 2025
in Labarai
0
Souleymane Cissé, baban harkar fim a Afrika, ya rasu yana da shekaru 84

Darakta Souleymane Cissé a wurin Bikin Finafinai na Tribeca a birnin New York City na Amurka a ranar 29 ga Afrilu, 2011. (Hoto: Jemal Countess / AFP)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Shahararren daraktan fim ɗan ƙasar Mali, Souleymane Cissé, ya rasu a daren jiya a babban birnin ƙasar, wato Bamako, yana ɗan shekara 84 a duniya.

Cissé, wanda yana daga cikin iyayen da suka yanke wa harkar fim cibi a nahiyar Afrika, ya rasu ne a wani asibiti.

‘Yar sa Miriam Cissé ta ce: “Baba ya rasu yau a Bamako. Dukkan mu muna cikin kiɗimewa. Ya sadaukar da dukkan rayuwar sa ga ƙasar sa, ga harkar fim da kuma aikin fasaha.”

Saƙwannin ta’aziyya sun shiga kwararowa daga sassa daban-daban, ana alhinin rasuwar Cissé wanda ayyukan sa na tsawon sama da shekaru hamsin suna nuni da irin sadaukarwar sa ga yadda ‘yan Afrika ke ba da labarin kan su ta hanyar fim, da tsantsar mutuntaka da zurfin sako al’amuran siyasa.

Wani darakta ɗan’uwan sa ɗan Mali, wato Boubacar Sidibe, ya faɗa a wani saƙon Facebook cewa industirin fim ta wannan ƙasa da ke yankin Sahel tana cikin jimami mai zurfi na wannan rashi.

Shi kuma Ministan Al’adu, Mamou Daffé, ya yi baƙin cikin rasuwar “wannan babban jigo na harkar sinima a Afrika.”

Cissé ne ya lashe gasar alƙalan Bikin Finafinai na Cannes na shekarar 1987 a ƙasar Faransa da fim ɗin sa ‘Yeelen’, wanda aka gina kan labaran tatsuniyoyi irin na ‘yan ƙabilar Bambara da ke yankin Afrika ta Yamma.

A cikin 2023, mashirya bikin Cannes sun ƙara karrama shi da kyautar Carrosse d’Or, wadda awad ce da ake ba daraktocin da suka “ɗabbaka tarihi a fagen sinima da bajintar su, da ingantaccen matakin su, da kuma yadda suka bayyana bambancin tsara wasa”.

“Wannan awad ɗin ta ƙara mani ƙwarin gwiwar shirya sababbin finafinai, in sake fito da kai na kuma in sauya alƙiblar da nake fuskanta,” inji daraktan a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na AFP a lokacin da ya halarci bikin a gaɓar French Riviera.

Ita wannan awad ɗin dai an sace ta a gidan sa a 2024, kafin daga baya a gano ta.

Souleymane Cissé a bikin FESPACO a Wagadugu, ƙasar Burkina Faso cikin Maris 2013

Cissé yana daga cikin mashirya fim biyu kacal waɗanda suka lashe babbar kyauta har karo biyu ta Bikin Finafinai da Talabijin ta Nahiyar Afrika (wato Panafrican Film and Television Festival, FESPACO), da ake yi shekara-shekara a Burkina Faso, wanda yana ɗaya daga manya kuma mafi daraja a gasannin fim a Afrika.

An shirya cewa a yau Alhamis ne Cissé zai hau jirgin sama zuwa babban birnin Burkina Faso, wato Wagadugu, inda zai jagoranci kashi na 29 na FESPACO da za a fara a ranar 22 ga Fabrairu, sai Allah ya yi masa rasuwa.

A wata hira da ya taɓa yi da AFP a cikin 2011, Cissé ya yi kira ga sababbin jinin masu shirya fim a Afrika da su guji dogara da samo kuɗi daga nahiyar Turai don shirya fim.

Ya ce: “A yau matasa sun koma ‘yan ma’abba wajen neman shirya fim, sun zama almajirai masu roƙo ko da yaushe na a ba su kuɗi daga Turai,” inji shi.

Cissé ya kasance zakara a harkar fim a ƙasar sa da ma nahiyar baki ɗaya har zuwa ƙarshen rayuwar sa. A hirar da AFP suka yi da shi a wurin bikin Cannes a 2023, ya soki lamirin “tacewa” da “kyara” da ake amfani da su wajen hana finafinan Afrika su yaɗu a ƙasashen duniya.

Ko a ranar da ya rasu, sai da ya yi kira ga shugabannin mulkin soja na Mali – wadda ta ayyana 2025 da sunan shekarar al’adu – da su taimaka wa industirin ƙasar don ta kamo inda abokan hamayyar ta a nahiyar suka kai.

Ya ce: “A ce an yi fim kawai bai wadatar ba, tilas ne kuma a gan shi. Da fatan shugabannin mu za su taimaka mana wajen gina gidajen sinima,” ya faɗa a wajen wani taron manema labarai a safiyar jiya Laraba. “Wannan shi ne kiran da zan yi a gare su kafin mutuwa ta, idan Allah ya kawo ta.”

(Tare da rahoton AFP)

Loading

Tags: FESPACOMalirasuwaSouleymane Cissé
Previous Post

Da ina da iko, da na ba Abba El-Mustapha digirin digirgir – Farfesa Abdalla

Next Post

Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai

Related Posts

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
Next Post
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai

Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!