DARAKTAN fim ɗin ‘Mai Martaba’, wato Prince Daniel Aboki, ya bayyana cewa lokacin da ya so shiga harkar fim a Arewa sai ‘yan Kannywood suka ƙi karɓar sa, da ya koma kudu kuma sai su ma ‘yan Nollywood suka ƙi karɓar sa yadda ya kamata.
Jaridar online ta Pulse Nigeria ta ruwaito shi yana cewa dalilin ƙin sa a Arewa, saboda shi Kirista ne, ita kuma Kannywood ta Musulmi ce, yayin da ita kuma Nollywood yawanci ta Kiristocin Kudu ce, ga shi kuma shi ɗan Arewa ne.
Ta ce Daniel Aboki ya yi wannan tsokacin ne a wurin bikin baje-kolin finafinai na shekara-shekara na 2025 da ake kira Nollywood in Hollywood, a birnin Los Anjalis, Jihar Kalifoniya, a ƙasar Amurka.
An yi bikin a gidan wasa na Egyptian Theatre a cikin masana’antar Hollywood da kuma Jami’ar Southern California (USC) daga ranar 28 ga Fabrairu zuwa 1 ga Maris, 2025.
Mashiryin fim ɗin, ma’aikacin rediyo ne wanda a yanzu yake tashe a harkar shirya finafinai ta Nijeriya, musamman daga lokacin da aka shigar da fim ɗin sa na ‘Mai Martaba’ a matsayin wakilin Nijeriya a gasar duniya ta Oscars.
A cewar sa, ya fuskanci tsana daga Kannywood da Nollywood ne saboda inda ya fito.
Da yake amsa tambayoyin mahalartan taron, daraktan wanda ya ci kyaututtukan karramawa da dama a wurare daban-daban, ya faɗi irin gwagwarmayar da ya sha, ya ce: “Na samu kai na a tsaka-mai-wuya saboda ni ɗan Arewa ne, amma kuma Kirista.
“Ita Kannywood, da yake yawancin ta industirin Musulmi ce, ba ta karɓe ni sosai ba. A ɗaya ɓangaren kuma, su ma Nollywood, wadda yawanci Kiristoci ne, ba su karɓe ni ba saboda ni ɗan Arewa ne. Sai na samu kai na ina lilo a tsakanin duniyoyi biyu.”

A cewar sa, ya samu sauyin rayuwa ne daga lokacin da aka zaɓi ‘Mai Martaba’ a matsayin fim ɗin da zai wakilci Nijeriya a gasar Oscars.
Ya ce: “Abubuwan sun canja ne daga lokacin.”
Bayan wannan ƙi da aka nuna masa, Prince Daniel Aboki ya kuma haɗu da wahalhalun rashin kuɗi. “Ba wanda yake so ya zuba jari domin dai ni ba sanannen darakta ba ne,” inji shi.
Wata matsalar kuma ita ce samun lokeshin inda babu tashin hankali saboda matsalar tsaro da ake fama da ita a Arewa.
Ya ce: “Saboda barazanar Boko Haram da sace mutane da ake fuskanta, sai da muka bi a hankali wajen zaɓen wurare masu kwanciyar hankali.
“A ƙarshe dai mun ɗauki fim ɗin a Daura, wato garin su tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.”
Babbar matsalar da su Prince Daniel Aboki suka fuskanta ita ce da suka yi asarar sama da rabin fim ɗin da suka ɗauka saboda shirmen da wani ya yi masu.
Ya ce: “Mun yi asarar kimanin kashi 46 cikin ɗari na dukkan aikin da muka yi.” Da faɗin haka, sai masu sauraren sa a taron suka ja numfashi saboda mamaki.
Ya ce maganin matsalar kaɗai shi ne tilas suka sake ɗaukar aikin.
A ƙoƙarin sa na ceto fim ɗin, Aboki ya nemi shawarar mai kular masa da editin fim ɗin don jin yadda za su yi. Ta ce: “Na kira shi na tambaye shi idan akwai abin da za a iya yi. Sai ya ba ni amsa da wata aya daga cikin Baibul da ta ce: ‘Za a tashi ƙasusuwan da suka bushe’.”
Ya ce: “Abin da kuke gani yanzu shi ne wani sabon ɗaukar fim ɗin. Ba ma alfahari da abin da ya faru, to amma gaskiyar lamarin kenan.”