• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, October 12, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22

by ALI KANO
May 20, 2025
in Labarai
0
Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22

Malam Y.Z. Ya'u, Babban Daraktan CITAD

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

WATA ƙungiya mai zaman kan ta mai suna ‘Centre for Information Technology and Development’ (CITAD) ta bayyana “matuƙar damuwa” kan dakatar da finafinan Kannywood 22 da Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta yi a ranar Litinin.

Babban Daraktan CITAD, Malam Y.Z. Ya’u, ya faɗa a cikin wata sanarwa da ya rattaba wa hannu cewa, “A yayin da muke la’akari da muhimmancin haɓaka kyawawan al’adu da kare ɗabi’un al’umma, muna so mu ja kunne cewa kada ayyukan tacewa su riƙa take haƙƙin jama’a na yin amfani da intanet ko a riƙa daƙile fasahar su.

“A wannan zamani da intanet ta zama wani babban makamin ɗabbaka harkar ilimi, da nishaɗantarwa da ƙarfafa tattalin arziki, matasa suna ta ƙara rungumar kafofin intanet domin samun abubuwa daban-daban da za su yi amfani da su.

“Ƙoƙarin tace ababen ƙirƙira na intanet ba tare kyakkyawan nazari ba, ba kawai zai takura wa ‘yancin ƙirƙira ba ne, a’a zai ma iya ingiza masu ƙirƙira zuwa wasu wuraren da ba a so su je da wasu industirin fim waɗanda ba su da ƙa’idojin kare al’adun da gwamnatin jihar take so ta kare.

“Ba cinya ba ƙafar baya, irin waɗannan wuraren da za su iya zuwa wajen su, za su iya saka matasa cikin wasu abubuwan da aka ƙirƙira waɗanda suka yi hannun riga da kyawawan ɗabi’un da hukumar take so ta kare.

“Haka kuma muna damuwa da yadda musguna wa jama’a kan ‘yancin amfani da intanet yake ƙara ta’azzara a Jihar Kano. Misali, kama Buhari Abba na jaridar Kano Times da aka yi saboda abubuwan da ya wallafa a intanet ya haifar da babbar damuwa game da ‘yancin faɗar albarkacin baki.

“Irin waɗannan abubuwan da ke faruwa ba kawai suna haifar da rashin yarda tsakanin al’umma da gwamnati ba ne, har ma suna jawo barazana ga ‘yancin jama’a a ƙarƙashin Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya.”

CITAD ta ƙara da cewa: “Bugu da ƙari, ita fa intanet waje ne wanda ba ya da shinge, wanda ƙauyen duniya ne inda labarai da ababen ƙirƙira suke shawagi suna shiga inda suka ga dama ba tare da iyakoki ba. Ba zai yiwu wata jiha ta ware kan ta ba a wannan duniya da ta riga ta cakuɗe. Yunƙurin yin hakan ba zai haifar da ɗa mai ido ba, sai ma ya tunzura masu ƙirƙira da muke da su har su riƙa kewaye dokokin gwamnati, suna wallafa abubuwan su a inda hannun hukuma ba zai iya kaiwa ba.

“Saboda haka, cibiyar ‘Centre for Information Technology and Development’ (CITAD) tana kira kamar haka:

  • ”Gwamnatin jiha ta riƙa kare haƙƙin jama’a na ‘yancin faɗin albarkacin baki da na samun bayanai, kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya tanadar.
  • “Muna kira ga hukumomi a Jihar Kano da su kauce wa duk wani abu da zai iya take haƙƙin ɗan’adam na yin amfani da intanet, wanda ba kawai zai karya masana’antun ƙirƙira ba ne, har ma ya ɓata sunan jihar.
  • “Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta riƙa bin hanyoyin rungumar kowa da kowa wajen tafiya tare da dukkan masu ruwa da tsaki, waɗanda suka haɗa da ‘yan fim, da ‘yan gwagwarmayar kare haƙƙin amfani da intanet, da sauran su, domin fito da ƙa’idojin da suka dace, waɗanda za su kare kyawawan ɗabi’u a yayin da suke martaba ‘yancin jama’a na yin amfani da intanet.”

Loading

Tags: Abba El-MustaphaCentre for Information Technology and Development (CITAD)Hukumar Tace Finafinai Da Ɗab'i ta Jihar KanoYZ Ya'u
Previous Post

Gwamnatin Kano ta dakatar da haska finafinan Kannywood 22 a intanet da talbijin 

Next Post

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

Related Posts

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu

October 6, 2026
Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba
Labarai

Za a ƙaddamar da reshen Kaduna na KAFIGAN ranar Asabar

October 1, 2026
Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu
Siyasa

Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu

September 30, 2026
Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa
Siyasa

Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa

September 30, 2026
Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa
Siyasa

Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa

September 29, 2026
Next Post
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya - Idris

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!