A DAREN ranar Lahadi da ta gabata Allah ya ɗauki ran mahaifiyar darakta a Kannywood, Malam Salisu Mu’azu, Malama Khadija Hassan a Jos, Jihar Filato, sakamakon rashin lafiya.
Marigayiyar mai shekaru 81 ta rasu ta bar ‘ya’ya goma, daga cikin su akwai shi Salisu wanda ƙane ne ga fitaccen jarumi Sani Mu’azu.
Da fatan Allah ya jiƙan ta, ya kyautata makwancin ta, amin.