• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Dole mu tafi da zamani a harkar rubutun mu – Jamila Rijiyar Lemo

by MUKHTAR YAKUBU
October 17, 2025
in Marubuta
0
Dole mu tafi da zamani a harkar rubutun mu – Jamila Rijiyar Lemo

Hajiya Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HAJIIYA Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo tana ɗaya daga cikin manyan marubuta mata waɗanda suka daɗe suna bayar da gudunmawa a fagen rubutun littattafan Hausa. Ta rubuta littattafan hikaya, waƙoƙi da dirama da dama. Ta samu kyaututtukan karramawa a harkar rubutu a lokuta daban-daban, ciki har da gasar Hikayata ta BBC Hausa inda ta zo ta biyu a shekarar 2019.

A wannan tattaunawar da mujallar Fim ta yi da ita, haziƙa Jamila ta yi bayani kan yadda harkar rubutu take a baya da kuma yanzu da al’amarin ya koma soshiyal midiya.

FIM: Da farko za mu so ki gabatar da kan ki ga masu karatun mu.

JAMILA ABDULLAHI RIJIYAR LEMO: To da farko dai suna na Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo. Ni ‘yar garin Kano ce, a unguwar Rijiyar Lemo, kuma an haife ni a shekarar 1980. Na yi karatu tun daga firamare har zuwa jami’a a matsayin digiri. Ina da yara guda shida – uku maza, uku mata. A yanzu ni ma’aikaciyar gwamnati ce a Ma’aikatar Yaɗa Labarai, ina matsayin Jami’ar Yaɗa Labarai ta Ƙaramar Hukumar Bichi a Jihar Kano.

FIM: A yaushe kika fara harkar rubutun littattafan Hausa?

JAMILA: Na fara rubutu ne tun ina makarantar firamare, kuma daga lokacin da na fara rubutu zuwa yanzu na rubuta littattafai guda tara. Akwai na farkon su shi ne ‘Kanya Ta Nuna’, ‘Bakin Ganga’, ‘Tattabara’, ‘Shan Koko’, ‘Cizo Da Kamar Ceto’, ‘Zaƙi Da Maɗaci’, ‘Mamaya’, ‘Makomar Mu’, da kuma na A Daidaita Sahu. Sannan ina rubuta waƙoƙi haka da muƙalu.

FIM: Ko ya aka yi kika zama marubuciya?

JAMILA: To, farkon rubutu na dai akwai yaya na wanda yake koyar da mu darasi a duk ƙarshen mako. To, wata rana sai nake duba littattafan sa, sai na ga rubutaccen labarin wasan kwaikwayo, nake tambayar sa, “Yaya Nasir, kai ka rubuta wannan?” Sai na ji abin ya shige ni, na ji zan iya. Ina jin a lokacin ina aji uku ko huɗu ne. Don ya ƙarfafa mini gwiwa sai ya ba ni kuɗi na sayo littafi da biro. Daga nan na fara, na rubuta wani labari mai suna ‘Idan Ba Ka Ci Naman Kura Ba…’ Kuma tun daga nan na ci gaba da rubutun littattafan, amma dai ban kai ga buga littafin ba har sai da aka yi mini aure, bayan na fito daga gidan aure ne na buga littafi na na farko, wato ‘Kanya Ta Nuna’. To daga nan sai duniya ta fara sani na, domin kuwa ‘Kanya Ta Nuna’ ya samu karɓuwa a ƙasar nan har ma da ƙasashen waje.

Kuma ba zan manta ba, Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, ya bayar da gudunmawa sosai wajen tallata ni a duniya, don a lokacin idan Turawa sun zo hira da marubuta akan je har gida a same ni don a yi hira da ni a matsayin marubuciya.

Jamila da ɗaya daga cikin littattafan ta

FIM: Ko za ki iya tuna marubutan da suke tashe a lokacin da kika shigo harkar rubutu?

JAMILA: Zan iya tunawa. A lokacin manyan mu na harkar rubutu da na samu akwai Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, Balaraba Ramat, Ɗan’azumi Baba Ceɗiyar ‘Yangurasa, Aminu Abdu Na’inna, Bala Anas Babinlata, Bilkisu Funtuwa, Zuwaira Isa, da dai sauran su.

Sai kuma waɗanda muka shigo harkar kusan tare da su, irin su Bilkisu Yusuf Ali Rabi’a Talle Maifata, Umma Sulaiman ‘Yan’awaki, Hadiza Nuhu Gudaji, Maryam Kabir Mashi, Alawiyya Wada, Halima K/Mashi, da sauran su.

FIM: A yanzu zamani ya tafi da rubutun littattafan, ya koma soshiyal midiya. Ko ya ya kike kallon yadda rubutun ya sauya?

JAMILA: Gaskiya ne zamani ya tafi da rubutu, an daina buga littattafai, sai dai a ɗora a onlayin, amma dai duk da haka ina alfahari da rubutun da na yi na littattafai, don ya ɗaga daraja ta.

Kuma a cikin labarin da na rubuta akwai wanda na shiga gasar rubutun Hikayata na BBC. Don haka duk da zamani ya tafi da mu, zan ita cewa alhamdu lillah, mun ci nasara, kuma cigaba da rubutun littattafai na onlayin wani cigaba ne; da ba a ci gaba da rubutun onlayin ba da zamani zai tafi ya bar mu ne. Don haka muna da damar da za mu isar da saƙon mu a duk yadda zamani ya juya.

Amma dai hakan ba zai sa mu daina rubutun littattafai muna bugawa ba. Don haka a baya-bayan nan na buga littafi na mai suna ‘Makomar Mu’, domin zamani ba zai sa mu bar mafari ba. Amma duk littattafai na ina son na fitar da su a onlayin don ya zama muna tafiya da zamani. Kuma in-sha Allahu duk littattafai na – da na baya da wanda zan yi nan gaba – za a rinƙa samun su a onlayin don tafiya da zamani.

Shida daga cikin littattafan Jamila Rijiyar Lemo

FIM: Kasancewar ki tsohuwar marubuciya, ko yaya alaƙar ki take da marubuta na yanzu, musamman masu rubutu a soshiyal midiya?

JAMILA: Duk da yake dai ban cika halartar abubuwa na marubuta ba sosai, amma dai ina da kyakkyawar alaƙa tsakani na da su; suna mutunta ni sosai, kuma wasu ma daga cikin su sukan nemi shawara a waje na, wasu na san su a fuska, wasu ban san su ba. Amma duk da ban san su ba idan suka ji suna na suna mutunta ni sosai. Kuma gaskiya mafi yawan marubutan na yanzu suna da mutunta na gaba da su, sannan suna da ƙoƙarin yin tambaya a kan abin da ya shige musu duhu a kan harkar rubutun su domin a yi musu gyara. Don haka kaso mafi yawa daga cikin su suna da mutunta mutane kuma suna son gyara, duk da dai akwai wasu marubutan onlayin da suke da kurakurai a cikin rubutun su, don ka ga ba a taru an zama ɗaya ba.

Don haka ina yaba wa masu son gyara a matsayin mu na manya a gare su, hakan yana burge ni, saboda su ne za su zamo magadan mu a nan gaba. Kuma za mu so a ce waɗanda suka gaje mu suna yin abin da za a yaba da shi, don ga yanzu girma ya fara kama mu, mun fara zama tsofaffin marubuta! Muna fatan Allah ya ƙara musu basira da ɗaukaka.

FIM: Waɗanne irin nasarori kika samu a harkar rubutu?

JAMILA: To, alhamdu lillahi, nasarori dai an same su. Babbar nasara ita ce mun rubuta saƙo ga al’umma kuma saƙo ya isa, duk ana kiran mu ana yi mana godiya da sambarka, saboda sun karanta littattafan da hakan ya zama wata hanyar warwarewar matsalolin su.

Wasu kuma za su kira mu su sanar da mu matsalolin su mu warware musu, muna sanar da su daidai yadda Allah ya sa muka fahimci matsalar da yadda za a warware ta, kuma suna gamsuwa, alhamdu lillahi. Idan ma abin ya fi ƙarfin sanin mu sai mu ce su jira mu don mu tambayi na sama da mu.

Jamila Rijiyar Lemo (ta farko daga dama) tare da abokan nasarar ta a bikin gasar Hikayata ta BBC Hausa ta 2019 lokacin da ta zo ta biyu

To ka ga wannan ma nasara ce ba ƙarama ba. Don mafi alherin mutane shi ne wanda ya amfanar da su. To gaskiya ni rubutu na, ina yin amfani da damar da nake da ita ne wajen faɗakar da mutane, kuma idan har an yi dace mutum ya samu kan sa a cikin masu amfanar da mutane, to ka ga kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Fatan mu shi ne mu yi rubutun da zai amfane mu duniya da lahira.

FIM: To, madalla mun gode.

JAMILA: Ni ma na gode sosai.

Loading

Tags: Gasar HikayataJamila Rijiyar Lemolittafimarubuciya
Previous Post

Abin da ya sa na fi shaƙuwa da marigayiya Hauwa Lawan Maiturare a duk aminai na – Bilkisu Yusuf Ali

Next Post

Ƙwararren marubucin fim, Adamu Ibrahim Kabala, ya kwanta dama

Related Posts

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro
Marubuta

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro

January 10, 2026
Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama
Marubuta

Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama

December 25, 2025
‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa
Marubuta

‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa

December 25, 2025
Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo
Marubuta

Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo

December 24, 2025
Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu
Marubuta

Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu

December 19, 2025
Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata
Marubuta

Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata

December 8, 2025
Next Post
Ƙwararren marubucin fim, Adamu Ibrahim Kabala, ya kwanta dama

Ƙwararren marubucin fim, Adamu Ibrahim Kabala, ya kwanta dama

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!