ALLAH ya yi wa Jami’in Yaɗa Labarai na ƙungiyar masu shirya finafinai ta KAFIGAN, Malam Adamu Ibrahim Kabala, rasuwa.
Ya rasu a yau Litinin a Kaduna bayan ya yi fama da rashin lafiya.
An yi jana’izar sa da safe a gidan sa da ke Bakori Road a unguwar Kabala Costain, Kaduna.
Ya rasu ya bar matar sa da ‘ya’ya da dama.
Rasuwar Adamu ta girgiza jama’a, musamman’yan fim na Jihar Kaduna, waɗanda da dama sun yi addu’ar Allah ya rahamshe shi.
Ƙungiyar KAFIGAN ta miƙa saƙon ta’aziyyar ta ga iyalan mamacin, ta kuma jajanta wa masoyan sa da abokan aikin sa.
A cikin takardar sanarwa wadda Daraktan Yaɗa Labarai na ƙungiyar, Malam Al-Amin Ciroma, ya rattaba wa hannu, KAFIGAN ta ce marigayin mutum ne mai sauƙin kai, mai son zaman lafiya, kuma mai sadaukarwa ga cigaban masana’antar Kannywood.
Ta ce a matsayin sa na tsohon Shugaban Ƙungiyar Marubutan Finafinai (Scriptwriters Guild) na Jihar Kaduna, ya nuna ƙwarewa matuƙa a aikin sa.
Bugu da ƙari, ya bada gagarumar gudunmawa wajen kafa KAFIGAN a jihar.
Takardar ta ruwaito cewa Shugaban Kwamitin Dattawa na KAFIGAN, Malam Isma’il Na’abba (Afakallah), da Darakta-Janar na ƙungiyar, Malam Adamu Bello (Ability), duk sun miƙa gaisuwar su.
Ita ma babbar furodusa kuma makusanciyar marigayin, Hajiya Fatima Ibrahim Lamaj, duk sun miƙa gaisuwar su tare da bayyana alhini kan wannan babban rashin.
KAFIGAN ta yi addu’ar Allah ya jiƙan Malam Adamu Kabala tare da fatan Allah ya yi masa sakayya da gidan Aljannar Firdausi.
![]()







