A YAU aka gudanar da rana ta biyu ta Bikin Baje-kolin Finafinai na Harsunan Afrika na Kano, wato Kano Indigenous Languages Africa Film Market and Festival (KILAF).
Taron, wanda ake gudanar da shi a Ɗangote Business School da ke sabuwar Jami’ar Bayero da ke Kano, an fara shi da kallon finafinan da suka shiga gasar wanda a tsarin taron an shirya za a rinƙa kallon finafinai daga ƙarfe 10 na safe zuwa 5 na yamma.
An kalli fim na farko wanda aka shigar da shi cikin gasar daga ƙasar Afrika ta Kudu. Sai kuma na biyu daga Ruwanda.
Bayan an gama kallon su da misalin ƙarfe 12 na rana, sai aka tafi hutun cin abinci tare da sallar Juma’a.
Haka kuma an yi baje-kolin kayayyakin gargajiya da suka haɗa da riguna, kayan zane-zane da sauran abubuwan tarihi na Afrika
Akwai kuma ɓangaren abinci da abubuwan sha na gargajiya da aka ƙawata taron da su domin buƙatar mahalarta taron.

Haka nan an zagaya da baƙin da suka zo daga ƙasashen daban-daban domin nuna musu abubuwan tarihi da al’adu na Kano.
Bayan an dawo da misalin ƙarfe 3 aka haska fim ɗin ‘Kakanda’ na Ahmad Sarari wanda kuma shi ne fim ɗin Hausa na Kannywood kaɗai da aka shiga gasar da shi.


An kammala kallon fim ɗin da misalin ƙarfe 5 na yamma, yayin da mahalarta suka tafka muhawara mai zafi dangane da irin salon da fim ɗin ya zo da shi, wanda ya sha bamban da sauran finafinan Hausa da aka saba gani.
Malam Khalid Musa ne ya rufe taron da addu’a da misalin ƙarfe 6 na yamma.
A rana ta ƙarshe, wato gobe Asabar, za a ci gaba, kuma a ranar ne za a bayyana finafinan da suka yi nasara a gasar tare da ba su kyaututtukan da suka samu.
![]()







