HUKUMAR kula da Haɗurra ta Ƙasa (Federal Road Safety Commission, FRSC), reshen Kano, ta karrama jarumar Kannywood, Hajiya Mansurah Isah, saboda gudunmawar da take bayarwa wajen taimaka wa mabuƙata da masu ƙaramin ƙarfi ta hanyar samar da abinci da kula da lafiyar su.
An karramawa ta ne a lokacin wani taron wayar da kan al’umma da hukumar ta gudanar a ofishin ta da ke Lawan Dambazau Link, daura da Titin Zariya a Kano.
Taron, wanda ya samu halartar ƙungiyoyin jinƙai da taimakon jama’a da dama, an gabatar da shi ne domin samar da hanyoyin da hukumar za ta bi domin wayar da kan al’umma, musamman masu amfani da hanyoyi, wajen gudanar da ayyukan su ta hanyar sana’a ko wasu ayyuka na daban.
Wannan ya sa hukumar ta gudanar da taron da ƙungiyoyin domin kusancin su da jama’a ta yadda saƙon zai fi shiga cikin al’umma cikin sauƙi.
A taron dai an bayar da dama ga mahalarta su yi tambayoyi da kuma neman ƙarin bayani, haka nan an bada shawarwari kan yadda ayyukan za su kasance wajen wayar da kan al’umma ɗin.
Hukumar ta ce ƙofar ta a buɗe take domin karɓar shawara daga jama’a a duk lokacin da aka zo masu da ita.
A ƙarshen taron aka karrama Mansurah.D
a take jawabin godiya, Mansurah ta yaba wa hukumar bisa ayyukan da take gudanarwa na kula da mutane da dukiyoyin su a duk faɗin ƙasar nan.
Haka kuma ta yi godiya bisa zaɓo ta da aka yi a cikin miliyoyin jama’ar ƙasar nan aka karrama ta domin ganin ta da aka yi a matsayin mai bada gudunmawa ga al’umma.
Ta ce: “Wannan karramawa ta zama wani ƙarin ƙarfi a gare ni wajen gudanar da ayyukan da nake yi na hidimta wa jama’a, kuma za mu bayar da dukkan gudunmawar da ake buƙata da goyon bayan mu ga wannan hukumar ta FRSC wajen gudanar da ayyukan ta.”
![]()







