SHUGABAN Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, ya bayyana cewa ɗaya daga cikin dalilan da suka sa hukumar ta gudanar da taron Mauludin Manzon Allah (SAW) karo na biyu shi ne domin a yauƙaƙa haɗin kai a tsakanin sha’irai.
An shirya taron ne tare da haɗin gwiwa da gamayyar ƙungiyoyin sha’iran Jihar Kano, kuma shi ne karo na biyu.
Taron, wanda aka gudanar da a jiya Alhamis a harabar gidan talbijin na ARTV da ke Titin Maiduguri a Kano, ya samu halartar wasu daga cikin manyan jami’an gwamnati da mawaƙan yabon Annabi (s.a.w.) masu yawan gaske.
A jawabin nasa, El-Mustapha ya ce: “An shirya Mauludin domin samar da hanyar kyautata alaƙa tsakanin mawaƙan yabon Annabi sallallahu alaihi wa sallama da kuma Hukumar Tace finafinai ta Jihar Kano, a sakamakon ruwa da tsaki da hukumar take da shi a game da ayyukan masu yabon.
“Don haka ne a shekarar da ta gabata muka samar da wani tsari na shirya Mauludin domin haɗa kan sha’irai da kuma kusanto da su ga hukumar, wanda hakan ne zai sa a samu sauƙin magance matsalolin da ake ganin sha’iran suna da su ta hanyar kula da ayyukan su da kuma yi musu gyara daga masana.”


Ya ƙara da cewa, “Babu shakka, jama’a shaida ne, zuwa yanzu an samu sauƙin ƙorafin da ake yi a kan su, saboda mun mayar da hankali wajen samar musu da kyakkyawar hanyar gudanar da ayyukan su ta hanyar jawo su a jiki da kuma shirya musu tarukan ƙara wa juna sani, inda muke gayyato malamai masana suna yi musu bita a kan kiyaye lafuzza wajen gudanar da ayyukan su na yabon Annabi sallallahu alaihi wa sallama.
“Don haka muna fatan wannan alaƙa za ta ci gaba domin samar da waƙoƙin yabon Annabi cikin ladabi da kuma natsuwa.”
Shi ma da yake nasa jawabin, Shugaban Gamayyar Ƙungiyoyin Sha’irai na Jihar Kano, Sidi Abba, ya bayyana godiyar sa ga El-Mustapha bisa kulawa da kuma jawo su a jiki da ya yi, wanda ba su taɓa samun haka ba sai a lokacin sa.


Sidi Abba ya ce: “Muna alfahari da kai Abba El-Mustapha da ka ba mu dama kuma ka jawo mu a jiki domin ganin an samar da kyakkyawan tsari da gudanar da ayyukan yabon Annabi sallallahu alaihi.
“Domin kai ne ka nuna mana ka damu da a tsaftace harkar yabon Annabi, don a kawo gyara a cikin ta. Kuma alhamdu lillah mun samu ci gaban da ya sa muke alfahari da kai a matsayin ka na masoyin mu kuma masoyin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama.
“Kuma za mu ci gaba da bayar da goyon bayan mu a gare ka, a dukkan ayyukan ka na kawo gyara a gare mu.”
Daga nan aka shiga waƙoƙin yabon Manzon Allah, inda aka rinƙa gayyato sha’irai suna gabatar da waƙoƙin su, inda aka shafe tsawon wuni guda ana gudanar da taron.
Sha’irai masu yawa ne sun halarci taron kuma suka gabatar da waƙoƙin su. Kaɗan daga cikin su akwai Malam Bashir Ɗandago, Malam Bashir Ɗanmusa, Sidi Abba, Abdullahi Baba mai waƙar ‘Zangon Kataf’, Maryam Fantimoti, Sayyada Fati Baffa Fagge, Fati Musa mai waƙar ‘Rayuwa’, da sauran su.
![]()







